Chapter 24

43 1 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                                *24*

Sokoto 2020,

Tsaye yake jikin mota yana qara duba agogon hannun shi don ya san ko ba a fada ba dare yaja sosai.
Umar dake sanye da lab coat ne ya iso gareshi yana fadin "Au ashe ka fito ina ta duba ka a ciki".

"Na fi minti 5 da fitowa ai, ashe dare yaja haka?"
Hafeez yayi tambayar yana qara duba agogon hannun shi.

"Wallahi kuwa, nima fa sai yanzu na samu kaina. Allah dai ya basu lafiya".

"Amin dai, ni zan wuce umar duk yanda ake ciki ma yi waya. Nasan zuwa anjima ko gobe da safe 'yan uwan nata zasu qaraso".
Hafeez ya fada yana qoqarin duba makullin motar shi dake aljihun rigar shi.

"Toh shikenan babu damuwa. Allah dai ya saka maka abokina. Amma fa mutumina nima ka sani a case"
Umar ya fada a lokacin da suke qara musabahar hannu da Hafeez.

Dariya Hafeez yayi yace "Kaidai anyi matsoracin likita wallahi. Sai da safe dai. Nagode"
Da haka sukayi sallama Hafeez yaja motar shi yana fita daga asibitin.

Ko da ya isa gida yayi parking maimakon ya fito daga motar kawai sai ya kwantar da kujerar motar ya kwanta yana tunanin abubuwan da suka faru a ranar.
Zai iya cewa dai gaba daya shi kam ranar nan tazo mishi a baibai.
Da fari yana zaune gida ciki kadaici da tunani kala kala kafin zuwan Ibrahim da har ya dan ji dama dama.
Basu wani dade sosai ba tare kuma Aysha ta bayyana da ta ta dramar har tana roqon ya mai da ta wanda daga bisani ma suka koma ciki suka bar ta a nan da maigadi wanda yasata dole ta fita.

Bazai iya cewa minti nawa ko hour nawa aka dauka bayan faruwar hakan ba kawai yaji kiran Mahaifin Jamila wanda yayi mishi Albishir da cewar ya turo manyan shi maganar auren su da Jamilar.
Yayi farin ciki bazai 6oye ba ba dan komai ba sai dan ko babu komai yasan cewa auren Jamilar zai rage wani kaso daga cikin matsalar shi.
Shi kam yasan bazai ce kai tsaye yana son Jamila ba saidai yana da yaqinin zaman su tare zai kawo Alkhairai da yawa fiye da duk wani sharri.
Yana da yaqinin Jamila zata kula da shi da yaranshi da ma Mahaifiyar shi kamar yanda a baya yake zaton Hadeeza zata mishi.
Yana kuma da yaqinin shima zai kula da ita da dukkan buqatun ta kamar yanda a baya ya kula da Aysha da babu abinda ta saka mishi dashi ma sai sharri.

Qarar wayar shi a wannan lokacin ita ta katse shi daga tunanin da yake inda ya duba yaga kiran umar ne.
Yayi mamakin yanda maganar da umar ya fara mishi bayan amsa wayar shine "Hafeez kana ina?"
Bai tsaya bashi amsa ba ya mayar mishi da tambayar "Lafiya dai ko?" Domin ko ba a fada mishi ba zuciyar shi da yanda umar ke tambayar ya tabbatar mishi da ba lafiya ba.
Nan take Umar ya sanar mishi cewa an kawo Aysha asibitin su cikin yanayi mai muni wanda shima daqyar ya iya gane ta wai wani mai mota ya kade ta ya gudu a yanayin da ake ciki ma ana ta ya tata6ur za da wadanda suka kawo ta cewa baza a kar6e ta ba sai da 'yan sanda da kuma kudin asibiti tunda private ne ba na gwamnati ba.

"To ni kuma umar meye nawa? Ku kira 'yan uwanta mana"
Hafeez ya fada kai tsaye bayan dukkan bayanan da umar yai mishi.

"Haba Hafeez, ya ina gaya maka rayuwar uwar yaranka na gab da salwanta amma kana nuna halin ko in kula. Nasanka Hafeez, idan har Aysha ta mutu a wannan yanayin ba tare da ka taimaka mata ba bazaka ta6a yafewa kanka ba. Don Allah kazo ko ba dan ita ba don girman Allah da kuma darajar yaranku".

Shiru Hafeez yayi bai amsawa Umar ba sai ma katse wayar da yayi don kuwa shi bai ma san me zai ce ba.
Yasan abinda Umar ya fada gaskiya ne idan Aysha ta mutu a wannan halin ba tare da ya gwada taimaka mata ba tabbas bazai iya kallon fuskar yaranshi ba.
Saidai kuma ko kadan baya son abinda zai qara hada shi da Aysha bare ma yaga fuskar ta.
Bai san me ya tuna ba kuma kawai yaji ya miqe yana daukar mukullin motar shi inda kai tsaye ya nufi asibitin su Umar din da ba wani nisa ne dashi da gidan shi ba sosai.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now