🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*17*
Waiwaye!
Kano city, 2012......
"And they live happily ever after" Ta fada fuskar ta cike da nishadi a lokacin da take qoqarin rufe littafin.
"Sadaqallahul azim" Tahan ya fada yana gyara zamanshi yana kuma maida kallon shi ga Hadeezan da tunda takai aya fuskar ta ke dauke da murmushi.
"Kasan da farko naso ace james ta aura, amma daga baya naji dadi da ta auri jacks. Yafi iya soyayya, shi james was too bossy, arrogant, and arrrghh kawai bai min ba"
Yanda ta qarashe maganar tana yamutsa fuska har da dafe hannun ta a ka tamkar tana maganar wasu mutanen gaske ne ba na littafi ba.Taha da tunda ta fara maganar yake kallon ta murmushi kawai yake a ranshi yana qara mamakin yanda Dee din tashi ke daukar mutanen novel da gaske.
Da fari yana daukar abun nata yarinta, amma gashi dai har ta kammala degreen ta na farko babu abinda ya canja daga gareta ta wannan fannin.A wancan satin da tana karanta mishi wani labarin da ko kusa ba fahimtar shi yake ba, kawai tsintar shashsheqar kukan nata yayi, da ya tambaye ta ma sai tace wai anyi breaking heart din wadda tafi so a littafin ne.
Ya kasa gane mutum irin Hadeeza, ta kan yi wa labaran da da kanta take rubuta su kuka, bare kuma wadanda wasu ne suka rubuta."Tee mana! Kai baka yi commenting ba. Na karanta maka labari babu ko sisin ka amma kayi shiru ka tsare ni da ido".
Hadeezan ta fada a shagwabe tana tura baki, wanda hakan ya dawo da Tahan daga tunanin da ya tafi.Sake sauke wani numfashi yayi sannan yace "Shukran ya Habibty, labarin yayi dadi. Saidai bamu tsinci komai da zai amfani rayuwar mu ba a nan gaba daga ciki. Kinga munyi asarar kusan hour 2 da wani abu kenan a banza."
Hararar shi tayi tana qara ta6e fuska tace "zaka fara ko? Kuma da kake cewa bamu tsinci komai ba, ai kuwa akwai lessons sosai a cikin rayuwar Jacks da sarah, irin sacrifice din da suke wa junan su, da yanda suke gudanar da soyayyar su ai duk ilimi ne. Muma mun qaru ai".
Juya manyan idanun shi yayi wanda hakan ya zama dabi'ar shi a duk lokacin da bai gamsu da zancen mutum ba sannan yace "Dee, duk wani ilimi na soyayya an riga an koyar damu a Alqur'ani da Hadisai tun da dadewa. Babu wani qato da zai qara wani abu wanda Annabi bai koyar ba.
Idan har zamu 6ata lokacin mu wajen karanta abinda wani bayahude ya rubuta yake son koyar damu, meyasa bazamuyi hakan kan Alqur'ani da sauran littattafan addini ba?. Yanzu ki duba ki gani fa tunda mukayi la'asar muke zaune a nan gashi har an kusa maghrib".Kallon shi take da irin yanayin da ta saba kallonshi a duk lokacin da yake mata irin wannan lecture, ita kam ta gaza gane matsalar Tahan.
Ta yarda tana son shi, ta kuma yarda tana mishi son da bazata iya canja shi da wani ba. Saidai ta kasa gane dalilin da yasa ra'ayin su ya kasa zuwa daya ta wannan bangaren.
Ita kam tana da burin kasancewa da wanda zai so ta yaso abinda take so, wanda zasu kwana ko su wuni suna kallo ko karanta littafi suna muhawara akan labarin.
Wanda zasu yi kuka suyi dariya a duk lokacin da suke kallo ko karatun.
Wanda zai yi koyi da soyayyar turawan da take ganin sun zarce kowa a wannan duniyar.
Wanda zai taimaka mata wajen isar da nata saqon ta hanyar rubutun da take yi.Amma saidai duk qoqarin ta na ganin ta canja Tahan, kullum qoqarinshi akan ya canja nata ra'ayin yake.
Tun kafin ya dawo daga sudan dinnan ya kan mata irin wadannan lecture idan suna waya tace mishi karatu ko kallo take, to amma ba koda yaushe ba sau dayawa saidai yace mata ta dinga ragewa, amma ita tunda ya dawo dinnan yake takure ta.
Har wani cewa yake shi bai so ta karanci fannin English din nan ba wai shi ya dada lalata ta.
![](https://img.wattpad.com/cover/146407140-288-k405691.jpg)
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
General FictionLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!