Chapter 5

66 8 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                         *5*

A hankali ta soma bude idonta har ta kai ga bude shi gaba daya. Ganin ta tayi kwance a kan gado daure da drip a hannun ta. qoqarin fincike drip din take taji muryar Hafeez.
"Be careful Hadeeza, kar ki cire drip dinnan"
Juya idanunta tayi saitin da yake zaune a wani empty gado dake kusa da nata.
"Me nake yi a nan?, ina Mahmoud yake? Da gaske yaro na ya mutu?."
Ta yi tambayoyin tana kokarin miqewa zaune.
Tasowa yayi daga inda yake zaune ya dawo gefen gadon da take kai ya zauna.
"Ki kwantar da hankalin ki, Mahmoud bai mutu ba"Hafeez ya fada cikin nutsuwa.
Bata san sanda ta sauke wata ajiyar zuciya ba tace "Yana ina? Inaso na ganshi indai da gaske kake."
"Zaki gan shi mana amma sai wannan drip din ya qare Hadeeza."
Hafeez ya fada yana nuna drip din da yatsan shi.

Gani tayi ma kamar Hafeez din ya raina mata hankali don haka kafin yayi aune ta tsige har butterfly needle din dake Hannun ta.
Da sauri Hafeez ya matsa gareta, wata auduga dake locker gefen gadon ya dauka ya sa mata a hannunta ganin yanda jini ke fitowa.
"Haba Hadeeza, baki da hankali ne? yanzu kuma idan kikayi wa kanki rauni fa?"
Hafeez yai tambayar ranshi a 6ace.
Bata ko amsa shi ba ta fizge Hannunta da ya riqe ta sauko daga kan gadon ta nufi hanyar waje ko takalmi babu bare kuma wani mayafi.
Bin ta yake yana qwala mata kira riqe da takalman ta da mayafin ta amma tayi mishi banza tacigaba da tafiyar ta ko damuwa da tsirarin mutanen da suke kallon su bata yi ba.
Ganin Hadeeza bata da niyyar tsayawa yasa ya damqo hannun ta.
Bata fizge ba ba kuma ta juya ta kalleshi ba tace "Ka sake ni, ina so in tabbatar da gaskiya da kaina tunda kai bazaka fada min ba"
"Bazan sake ki ba, har sai kin sanya takalmin ki da mayafin ki don bazan iya jure kallon da mutane suke miki kamar wata ta6a66iya ba"
Hafeez ya fada bayan ya karkato da Hadeezan tana fuskantar shi.

Bata ce mishi komai ba ta fizgi takalmanta da mayafin ta. Zira takalman tayi a qafarta, mayafin kuwa kawai kara shi tayi a kafadar ta. Dadin abun ma doguwar rigar atamfa ce a jikin ta kuma ba wai ta wani kama ta bane.

Tafiya suke yi kowa da abinda yake saqawa har suka isa bakin qofar dakin da Mahmoud ke kwance.
Hannunta ta dora akan handle din amma tsoro da fargabar ganin gawar Mahmoud din ya hanata budewa. Ganin hakan ne yasa Hafeez ya matsa gaba ya dora hannunshi akan nata ya murda handle din.
Rufe idanuwanta tayi gam ta ja ta tsaya a bakin qofar ba tare da tayi yunqurin shiga ba.

"Wuce mana" Hafeez ya fada yana kallon Hadeeza da idonta ke rufe.
"Bazan iya ba Hafeez, bazan iya kallon gawar Mahmoud ba"
Ta fada cikin wata murya mai ban tausayi.
Bai ce mata komai ba ya kama Hannun ta ya ja ta har zuwa gadon da Mahmoud ke kwance.
Har a lokacin Hadeeza bata bude idonta ba saida Hafeez ya qara magana.
"Ki bude idonki Hadeeza, trust me, Mahmoud yana nan da ranshi"
Wasu jerin addu'o'i ta fara karantowa a zuciyar ta kafin daga bisani ta bude idonta.

Kwance yake a kan gadon maqale da oxygen da robar abinci a Hancin shi. idanunshi a rufe wanda ya bayyana zara zaran lashes din idonshi. Duk da cewa fuskar shi da ilahirin jikin shi sun kumbura kadan amma hakan bai 6oye kyawun halittar Mahmoud ba. Babu tantama Mahmoud kyakykyawa ne ajin farko da kallo daya zaka mishi ka tabbatar da duk inda iyayen shi suka fito tabbas sun hada jini da dangin Shuwa Arab, fulanin Asali ko  kuma larabawa.
A hankali Hadeeza ta qarasa dab dashi ta kamo Hannunshi tana zub da qwalla.

Ko da ace ba dan da ta haifa da cikin ta bane dole tasan zata zubar mishi da qwalla, bare Mahmoud da tunda ya taso tsawon Rayuwa bai shaqu da kowa kamar ita ba. Ji take yi ina ma a bata za6in rayuwar ta ko lafiyar Mahmoud din, tabbas da ko tantama bazatayi ba zata bada rayuwar ta fansa ga tashi lafiyar.
Wani irin kuka ne ya ku6ce mata mai cin rai da ta tuna cewa bata da wani taimako da zata iya yiwa dan nata a yanzu.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now