🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen. Mersoo)
*27*
Kano city, 2012.
Ya sha jin wasu mutanen na cewa idan suna cikin wani tashin hankali ko damuwa suna ganin dishi dishi a idanun su, ko ma su ce ba sa gani baki daya.
Saidai shi ko kusa hakan bai ta6a faruwa dashi ba, bai ma tabbatar hakan na faruwa da gaske ba sai yanzu da ya fito daga 6angaren Daddy yaji yana hada hanya sakamakon dishi dishin da yake gani.Duk da dai cewa yana da yaqinin shi ba iya ganin nashi ne ya dauke ba, tunanin shi ma gabaki daya ne ya dauke don haka yake addu'ar Allah ya mai da shi BQ lafiya yaji shi a dakin shi ko zai samu damar zama ya nutsu ya sake fahimtar abinda Daddy yazo mishi dashi.
"Yayan su".
Yaji an kira shi.Yasan mutum daya ce take kiran shi da wannan sunan cikin gidan, ya san ba kowa bace sai Anty samira Matar Daddy ta uku don haka ya tsaya tare da juyawa saitin da yaji muryar ta ta.
Tsaye ya gan su jikin mota ita da yaran ta 'yan biyun gidan "Nasim da Na'im" 'yan autan Daddy kamar yanda ake musu kirari.
Ko da bai tambaya ba yasan unguwa zasu je yanda yaga dukkan su cikin shiri a bakin mota.
"Nace da Allah ko zaka zo ka dan miqa mu gidan Maman Hayatu?.
Wai yau ake birthday din Hayatu shine zan kai su Nasim, gashi kasan mota ta tana wajen gyara har yanzu. Shi kuma Bala driver daga cewa bari ya shiga ya kai wa Maman Baffa saqo ya fito mu tafi har yanzu yaqi dawowa.
Me yiwuwa ko wani aikin yake mata kuma".Girgiza kai kawai Tahan yayi tare da yin wani gejeren Murmushi.
Wato da gaske ne da ake cewa abubuwa da yawa basa canjawa, ya yarda cikin abubuwan nan har da matsalolin gidan su.Ya tabbatar Mama ce zata cewa Bala direban ya zauna ko kuma tasa shi wani aikin don kawai ta nunawa Anty samiran cewa bata isa ba, ko kuma don ta quntata mata ma kar ta fitan.
Ya riga ya gama fahimtar matsalar gidan su. Ya kuma gama gane Babbar mai matsala cikin Matan Daddy Mahaifiyar shi ce.
Duk sanda zakaji wata matsala to zakaji ance "Maman Baffa" .
Ita dai har kullum ya rasa dalilin da yasa ta kasa daina kishi da sauran matan Daddyn.Ya lura yanzu ta dan dagawa Maman jiddah qafa kishin nata ya koma kan Anty samira.
Saidai ya san hakan yana da nasaba da rashin zaman Maman Jiddah a gida sosai tunda tana zuwa aikin ta a matsayin ta na ma'aikaciyar lafiya kuma Nurse mai Babban matsayi a yanzu.Baya ga haka ma har chemist ne da ita wanda duk da ba ita take zama ba takan je lokaci zuwa lokaci.
Hakan yasa Mama mai da idon ta kan Anty samira, musamman da take ganin kamar Daddy yana fifita ta don yaga ta fi su quruciya.
Saidai kuma shi Taha ya karanci kowa a cikin su. Ya kuma yarda Daddy ba wai yafi son Anty samira bane kawai saboda quruciyar ta ko dan kasancewar ta kyakykyawa dangin shuwa arab.
Tasu ce dai tazo daya tunda ita ta iya lalla6a shi ta kwantar mishi da hankali, sannan kuma bata da yawan qorafi da mita kamar Maman.Ita kuwa Maman Jiddah ma aikin ta ta sa a gaba, hidimar ta da business din ta a yanzu su suka fi damun ta don haka ma ya zama bata da wani lokacin Daddyn sosai da har za a yi kishin da ita ma yanzu.
Saidai duk da haka, hakan bai hana Mama Rabi kishi da ita ba. A ganin ta duk wata qafafar ta da qaryar bokon ta dai da kudin Daddyn take yi tunda a gidan shi ta fara karatun har kuma ta gama ta kai matsayin da take yanzu."Amma idan kana wani abu ba damuwa. Sai muje mu tari napep. Dama saboda kayan nan ne musamman cake din bana so ta samu matsala".
Muryan Anty samiran ta katse Taha daga tunanin da yake.
![](https://img.wattpad.com/cover/146407140-288-k405691.jpg)
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
General FictionLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!