🌸QADDARAR MU CE🌸
By Merow Masu (Sen.Mersoo)
Salam, kamar yanda na fada a waccan Chapter ta baya, na dan zama busy ne kwana biyu da bazan iya samun damar yin updates a kai akai ba. Kuma har yanzun ma ba wai na zama free bane. A qara haquri har zuwa nan da sati 2 kafin ku qara ji na.
Amma Kafin nan ku shaqata da wannan!*10*
Wani lokaci mukan yi tunanin idan wani ya bar rayuwar mu kamar muma tamu rayuwar zata qare, amma abinda yake tabbatacce shine ba zata qare ba har sai Allah ya rubuta faruwar hakan.
Zaka ji da ma baka zo duniya ba, zaka ji dama baka hadu da wanen ba, zaka ji kamar ka kurma ihu duniya tasan halin da kake ciki, zaka ji bazaka iya jurewa ba, zaka yi kuka, zaka yi ciwo amma duniya bazata tsaya ba, numfashin ka ma bazai daina fita ba, haka kuma rayuwa bazata daina gudana ba.Irin wannan Hali Hafeez ya tsinci kanshi tun ranar da ya samu labarin auren sadiya, yayi kuka har bazaice ga adadin hawayen da ya zubar ba.
Bai ma san cewa kukan da yayi a zaria ba wani kuka bane sai da ya je garin sokoto, ya tabbatar wa kanshi ya rasa sadiyan shi har abada.
Zai iya cewa tun saukar shi abu daya kowa yake mishi Albishir dashi shine sadiyan tayi aure, ta kuma auri mai kudi babban Dan siyasa.Abinda ya dada qara quna zuciyar Hafeez shine har ya bar sokoto ya sake komawa zaria ya gaza samun amsar tambayoyin shi.
A tunanin shi kamar yanda yake gani a film ko ya karanta a littafi idan ya je sokoton zai ci karo da wata 'yar letter da sadiyan zata fada mishi dalilin ta na cin amanar shi.
Amma abun takaici babu abinda ya tarar sai surutu na mutane da kuma tunanin ta da garin ya dada haddasa mishi.
Gani yayi ko wanne titi, kowanne lungu, kai hatta motar shi da dakin shi sadiyan suke tuna mishi a garin, hakan yasa ko cikakken satin da ya daukarwa kanshi zaiyi bai iya qarasawa ba ya hada kayan shi ya koma zaria.Bayan komawar Hafeez da kwana 2 ya yanke shawarar zuwa makaranta tunda ya lura zaman nashi a daki ma shi kadai banda damuwa da tunani babu abinda yake qara mishi.
Shiryawa yayi tsaf cikin wata shadda dakakkiya ruwan toka ya sanya baqar hula da baqin takalmi ya dauki jakar shi ya fice, bai ma yi tunanin zuwa sashen iyalan kawun nashi ba don tunda suka samu labarin abinda ya faru dashi daga mahaifiyar shi suke ta wani lalla6a shi kamar wani yaro, shi kuma hakan ba qaramin dada karyar mishi da zuciya yake ba.
Wannan dalilin yasa yanzu baya son zuwa cikin gidan, yawanci ma abinci saidai a aiko mishi har daki.Tun daga nesa ya hango ta zaune kan kujerar tallar ta sanye da wani maroon din hijabi dogo ta duqar da kanta cikin cinyoyin ta.
Shi kam shaf ya ma manta da rayuwar ta banda lokacin da ya hange tan, ya ma manta shaf da yanda suka rabu bare kuma halin da ya barta da wannan azzalumin saurayin nata tsawon kwanakin nan.A hankali yake tafiya har ya qarasa inda take.
Zuciyar shi ce ta raya mishi ko bacci take ko kuma wani tunani mai zurfi a lokacin da ya tsaya a kanta yana lura da yanayin ta. wata sanda ya dauka a kusa da ita ya dan ta6a ta da ita, ya kuwa yi sa'a ta dago kanta da sauri tana goge idanunta.
Abun mamaki hawaye ya gani a idanunta, ga kuma yanda fuskar ta ta kumbura da wasu ciwuka hatta da le6en ta ya kumbura.
Take yaji tunanin shi ya bashi ko dai matsiyacin mustyn can ne ya daketa, amma gudun zargi yasa shi tambayar ta."Subhanallahi! Indo me ya same ki? Me ya samu fuskar ki haka? Wa ya ji miki ciwo?"
Hafeez din yayi tambayoyin yana qara duba fuskar tata.
Wani haushin Hafeez din ta qara jin ya cika mata zuciya ma, a ranta tace wannan dan rainin hankalin yana nufin bai san me ya haddasa ba.
Amma a zahiri shiru tayi don ita a ganin ta ma baya buqatar amsar ta."Tambayar ki nake bakya ji na ne?" Hafeez ya fada yana tsugunnawa a gaban ta yana qara fuskantar ta.
Ji tayi ya mata kwarjini yanda ya tsare ta da ido duk da cewa kuwa idanunta suna qasa ne, ba wai don taso ba tace
"Duk abinda ya faru ai kai ka jawo min, kuma wallahi bazan ta6a yafewa ba."
Shi kam bin ta yayi ma da kallon mamaki, so yake ya tuna laifin da ya aikata mata ma amma ya kasa.
A iya tunanin shi ma ita da saurayin ta ne suka bata mishi rai ranar da ya mai da ta gida.
Hakan ne ya sa shi qara mata wata tambayar yace "Ni kuma?, ta yaya akai kuma ya zama laifi na?."
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
FantasyLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!