Chapter 13

51 5 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE 🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                            *13*

Rayuwa cike take da qalubale kala kala, shiyasa wasu sukan kira ta da jarabawa.
Yanda take juyawa mutum lokaci guda tazo mishi da abinda bai ta6a tsammani ba kadai ta isa ta qarawa mai hankali imani da tsoron Allah.
A Shekarun da basu kai goma ba da suka wuce idan aka cewa Hadeeza zata shiga halin da take ciki a yanzu tabbas zata qaryata, zata kuma tabbatar wa wanda ya fada din cewa hakan ba mai yiwuwa bane.
Sai gashi a yanzu itace zaune cikin harabar asibitin da a yanzu ta zame mata tamkar gida tana kukan da bata san yaushe ne qarshen shi ba.
Kamar yanda bazata iya tuna sanda ta fara shi ba haka bazata ce ga sanda zata daina ba.
Kuka ne irin wanda kowacce uwa zata yi idan ta tsinci danta a irin halin da Mahmoud ke ciki a yanzu, kuka ne na sanin bata da hanyar da zata bi ta magance matsalar da take ciki, kuka ne na fargaba, fargabar abinda tasan bazata iya hana shi faruwa ba, fargabar rasa Mahmoud dinta na har Abada kamar yanda Dr. Ma'aruf ya tabbatar mata.

Kasancewar tsanantar da jikin Mahmoud yayi yasa aka maida shi ICU wanda hakan ba qaramin daga hankalin Hadeeza yayi ba.
Ta lura a kullum ciwon Mahmoud din tsananta yake qara yi sannan a kullum matsalolin ta qaruwa suke yi.
Dukkan abinda take ganin ta mallaka tana qoqarin rasa shi a ciwon Mahmoud din, ciki kuwa har da Hafeez.
Duk da cewa bata samu amsar tambayar ta wajen Ma'aruf na haqiqanin abinda ke damun Hafeez din ba, saidai ta riga tasan ba wai matsala ce kawai ta rashin dacewar da akayi wajen gwajin ba.
Ta sani akwai wani abu da suke boye mata, saidai bata san dalilin Hafeez na rashin dawowa asibitin ba kimanin kwanaki 3 kenan haka kuma bata san dalilin shi na qin kiran ta ba, ba kuma ta san dalilin shi na rashin daukar kiran ta ba wanda hakan ya dada jefa ta cikin damuwa.
Ba wai damuwar dake damun ta ce kadai damuwar ta ba, damuwar dake damun Hafeez din a yanzu itama ta shiga jerin matsalolin ta. Ta kasa manta ganin ta dashi na qarshe a office din Dr ma'aruf, ta kasa manta yanda hawaye ke zuba daga idanuwan shi. Ta kasa cire damuwar Hafeez din cikin ta ta damuwar.
Qarin matsalar ta kuma kiran da Dr ma'aruf yayi mata da rana akan cewa ta same shi a wani restaurant dake tsallaken asibitin.

Bata wani 6ata lokaci ba taje ta same shi a cikin wajen zaune riqe da gwangwanin maltina da kuma abinci a gaban shi.
Daya daga cikin kujerun dake jikin teburin da yake zaune ta ja ta zauna bayan ta mishi sallama.
Sai da suka gaisa cikin mutunci da girmamawa sannan ya tambaye ta ko akwai abinda take son ci ko sha.
Saidai duk da tace a qoshe take Ma'aruf din sam yaqi barinta haka sai da yasa aka kawo mata ruwa da kuma lemo mai sanyi.

Sun dau tsawon wani lokaci kafin Ma'aruf din ya soma yi mata bayanin dalilin kiran nata.
"Hadeeza, nasan abinda zan gaya miki tamkar ya sa6a qa'idar aiki na ne kuma bai cancanci a matsayi na na likita in kasance wanda zai bada gudummawa wajen daga miki hankali ba."
Dr.Ma'aruf din ya fada a lokacin da yake dire maltinar dake hannunshi kan tebur sannan ya numfasa ya cigaba.
"Maganar gaskiya Hadeeza jikin Mahmoud yayi tsananin da a kowanne lokaci zamu iya rasa shi muddin ba a samu anyi dashen nan ba. Ki sani a yanzu halin da yake ciki fa duk abinda zamu mishi a asibiti tamkar a banza yake, duk wani hope da zamu baki na qarya ne muddin ba a yi transplant din nan ba, gashi kuma a kowacce rana rashin nasara ake samu na samun lafiyar ta shi."
Hadeeza dake fuskantar Ma'aruf tuni idanunta suka soma cika da qwalla duk da cewa abinda ma'aruf din yake fada abubuwa ne da ita kanta ta sansu, ba ta ma san dalilin dayasa zai kirata don tuna mata abinda ta riga ta sani ba.

Tamkar Ma'aruf din ya karanci zuciyar ta, sai ya cigaba da cewa "Ban kira ki nan dan na daga miki hankali ko na tuna miki ciwon da Mahmoud ke ciki ba, na kira ki ne na baki shawara a matsayi na na aboki kuma kamar Uba ga Mahmoud."
Sai da ya ja wani dogon numfashi sannan ya cigaba da cewa "nasani bani da hurumin da zan tambaye ki kan wani abu da ya shafi personal life dinki, amma a matsayi na na abokin ki ba likitan ki ba ina mai baki shawara da ki taimaki rayuwar Mahmoud idan har kinsan akwai wani dan uwanki ko dangin ki da zasu iya taimakawa a taimaka a samarwa yaron nan abinda zai zama waraka a gareshi tun kafin lokaci ya qure."

QADDARAR MU CETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang