🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*28*
Kano city, 2012.
Godiya ga Allah madaukakin sarki da ya halicce ta, ya raya ta, ya sanya ni'imomi cikin rayuwar ta, ya hada ta da Mujaheed don ya zama wani jigo na farin cikin ta, ya amince mata samun Mujaheed din a matsayin masoyi, sannan yanzu ya nuna mata wannan ranar da za'a daura mata aure dashi, auren da take fatan mutuwa ce kawai zata raba.
Godiya ga Daddy, ummi, da sauran ahalin ta da suka amince mata, suka kuma yarje mata har ta kai ga ganin wannan ranar.
Godiya kuma ga zainab aminiyar ta wadda ta baza basirar ta wajen yi mata kwalliyar da zatace tsawon rayuwar ta bata ta6a ganin kyawun ta kamar na yau din ba.Ita kam komai na kwalliyar ya birge ta, gashi dai ba a ca6a komai an cika ba amma kuma tayi kyau matuqa. Zata iya cewa ma ko kwalliyar jiya ta Sisters eve da aka kashe maqudan kudi bata kai ta yau da zainab din tayi mata ba.
Babu abinda zata ce ga Allah da kuma kowa sai hamdala, komai na ta yana tafiya yanda take so, burikan ta duka a yanzu suna gab da cika. Awanni kawai ya rage mata ta amsa sunan Matar Habibin ta, farin cikin ta kuma rayuwar ta.
Sake kallon kanta tayi a madubin dake gabanta tare da sakin wani murmushi wanda yayi matuqar qara mata kyau.
"Maasha Allah! Daga ni din ne ko daga hannun ki zee?".
Zainab dake tsaye riqe da dankwalin farin leshin da zata daurawa Hadeezan, Murmushi tayi tare da girgiza kanta tace "Kema kin san amsar ai, ni tsaya in daura miki dankwalin nan kinsan dai yau ba ke kadai bace amaryar".
"Ya ilahi! Yanzu Maryam tunda na fita har na dawo bakiyi wankan ba ba kuma ki sha maganin ba?"
Muryar Anty Hafsa dake shigowa dakin ta sa su maida idanun su kanta.Sanye take da wata Royal blue din shadda wadda taji aiki mai ratsin jaa a jiki da yayi matuqar kar6ar kalar fatar ta.
Duk da dai Anty Hafsan ba fara bace kamar su Hadeeza, saidai ba zaka kira ta da baqa ba, musamman da ya kasance zaman london da kuma wadata yasa kalar fatar ta qara haske sosai, shiyasa kaloli kamar Jaa da Royal blue din suka haskaka ta sosai kuma suka qara mata kyau."Ni fa Anty Hafsa na gaji da shan wadannan abubuwan, duk concoction yayiwa mutum yawa a ciki".
Maryam dake zaune kan gado sanye da kayan bacci ta furta tare da kumburo baki.Ita sam bata ga dalilin wannan matsin ba, sun takura mata, ko kuma tace Anty Hafsa ta takura mata matuqa.
Tun daga ranar da Taha yaje ya same ta har ya mata fada kan rufe daki shikenan Anty Hafsa ta samu dama.
Ba don san ran ta ba dole ta haqura Anty Hafsan tasa ake mata gyaran jiki tsawon kwanaki 6 tunda ba a fara mata da wuri ba.
Baya ga haka ga wasu turarukan wanka na dole da ake sa ta tasaka a ruwan wankan ta.Ba wai fa ba sa mata qamshi ba ko kuma bata jin dadin su, ita dai kawai haushin ta shine suna mata wannan abubuwan ne saboda zasu aurar da ita ga wanda take ganin babu fa'idar suyi mata wannan gyaran saboda shi, tunda dai auren nan ba na soyayya bane, aure ne kawai na zumunci da kuma biyayya.
Ta ji dadi ma da yanda tun ranar basu qara haduwa ba, bai qara zuwa ba bai kuma ko kira ta ba, saidai taji suna waya da Teema yana tambayar ina take.
"Wallahi Maryam idan kika bari nazo kanki sai kin raina kanki. Duka zan miki kamar ba gobe wallahi".
Furucin Anty Hafsan da ya bawa Hadeeza da zainab dariya.
Zainab tace "Haba Anty Hafsa. Amarya ce fa. Ki rufa mana asiri dai"."To ai ita kanta bata san ita amaryar bace, da bata dinga wannan shashancin ba. Ace mutum ya zama mahaukaci? Biki dai ko ba naki ake yi ba tunda da 'yan uwanki ai kya tashi kiyi wanka ki shirya. Amma kina zaune a haka har anyiwa Jiddah da Teema kwalliya, yanzu gashi har an gamawa Yayar ku kina zaune babu abinda kikayi".
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
FantasyLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!