Chapter 12

52 3 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

       
                                 *12*

Bayan shekara 2!
Hafeez ne zaune a gajiye kan kujera yana qoqarin cire takalmin shi da ya kasance sau ciki.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya tabbatar dukkan takalman biyu sun bar qafar shi sannan ya jingina da kujera yana hammar da tayi daidai da shigowar Hajiyan shi parlourn dauke da tray mai drinks da kuma wasu snacks.
"To kar dai ka hadiye mu, na kusa gama abincin saura qiris. Ka tashi ka dan toshe gurbin yunwar da wannan"
Hajiyan ta fada lokacin da take qoqarin zuba mishi lemo bayan ta ajiye tray din kan center table.
Dagowa yayi a kasalance yana gyara zama yace "Wallahi Hajiya rabona da abinci tun jiya sai drinks kawai, kinsan ni abincin jirgin nan ba wani iya cin shi nake ba."
Miqa mishi cup din lemon tayi ta samu kujerar dake gefen Hafeez din ta zauna sannan tace "To laifin waye? Ace mutum zai dawo gidan su bazai iya kira ya fada cewa zai taho ba? Kawai saidai muga abu kamar dirar mikiya?"
Dariya ta bawa Hafeez din inda itama dariyar tashi ta sa ta dariya.

"Kai Hajiya, Nifa surprise naso nayi muku amma tunda nazo sai mita kikeyi, ko dai akwai wani abu da kuke ci idan bana nan ne?" Hafeez ya qarashe maganar da tambaya mai sigar zolaya.
"Abubuwa kai, Ai gashi kam kaga surprise don abinci sai nan da awa 5 zai sauka"
Hajiyan ta amsa itama cikin wasa da zolaya.
Hafeez da tuni ya ware idon shi yace "Ah zama bai kama ni ba, bari in tashi in bazama neman Abinci, dama Abokina sulaiman yana ta min mitar anyi bikin shi bana nan kinga sai naje na kwashi girkin amarya."
"To sarkin kwadayi, ka iya tafiya cin girkin amaryar wasu kai baka tsaya kaga taka amaryar ba ma bare kaci nata."
Hajiya ta fada tana hararar shi.
Sai da ya dan nutsu na wasu sakanni sannan ya gane inda zancen Hajiyan ya dosa, ashe fa Aysha tana makaranta.
Aysha!
Tsawon shekaru biyun nan da yayi a UK zai iya cewa babu ranar da zata zo ta wuce basuyi magana ba a waya, tun yana kiran Hajiya yace a bata har Hajiya ta gaji tace zata sai mata waya duk da kuwa da farko Hafeez din bai so ba a cewar shi kar wayar ta hana ta karatu.
Amma daga baya da Hajiyan tayi mishi bayanin cewa zata dinga kar6ar wayar duk sanda tasan Ayshan na da wani karatu ko zata je makaranta, sannan kuma ta bashi hujjar cewa yana da kyau Ayshan ta riqe waya ko babu komai saboda yan uwanta da suke nesa da ita sai yaji ya gamsu, ya kuma yadda Hajiyan bazata bari a samu matsala ba.

Cikin shekaru biyun nan babu laifi shaquwa mai qarfi ta shiga tsakanin su, ta kan sanar dashi dukkan abubuwan da ya faru a makaranta.
Ya lura da ta saba da makarantar, ta kuma yi sababbin qawaye da wasu abokan ma kamar yanda ta fada mishi. Sam hakan bai taba damun shi ba, a ganin shi yarinya 'yar secondary kuma JSS2 ma bazaka hana ta kula mazan ajin su ba saidai ya kan mata nasiha akan ta kiyaye.
Babban abinda yafi damun shi shine yanda ya lura da kamar Ayshan tana son rayuwar da tafi qarfinta, a duk sanda zata ga wani abu sabo a wajen wata qawar ta ko wani dan Ajin su sai ta fada mishi cewa tana son irin shi idan sukayi waya, tun yana ganin hakan yarinta ne har ya fara gane halin ta ne amma hakan baya hanashi tura kudi account din Hajiya ko na abokin shi Ibrahim yace A siya mata don gudun rigimar ta duk da kuwa Hajiyan shi tasha kwabar shi kan cewa kada ya saba mata da komai take so ace sai ta mallake shi.
Schoool bags kadai Aysha tana da kusan guda 8, banda takalma kusan qafa 10 da uniform sama da kala 7 da sauran abubuwa.
Abinda Hafeez ya dada karanta game da Ayshan shine tana da kishi na hada kanta da Hajiyar shi tun a yan shekarun ta da a yanzu take 16-17. A duk lokacin da zata ji yana waya da Hajiyar in har ya kira ta sai ta yi kicin kicin ta nuna yafi damuwa da Hajiyan akan ta. Shi din ma wauta da hauka yake daukar Al'amarin nata don haka sai ya bata haquri yace za a kiyaye.

Akwai ranar da Ayshan tana zaune da Hajiyan a parlour taji suna waya da Hafeez har Hajiyan tana mishi fada akan don me zai turawa Ibrahim kudi a siyawa Aysha MP3 bayan kuma yasan karatu takeyi, meyasa zai biye mata komai takeso ace sai anyi mata?.
Hakan ba qaramin fusata Aysha yayi ba har ta tashi ta wuce daki, duk da Hajiyan ta lura da hakan sai ta basar.
Ranar har maghrib bata fito daga daki ba har Hajiyan ta shiga tayi mata magana akan ko abincin rana bata ci ba amma sai tace ta qoshi.
Da kanta Hajiyan da taga har anyi isha ta zuba abincin ta kai wa Ayshan ta kuma bata haquri akan ba wai bata so a siya mata MP3 bane, a'a ta ga dai ba kida ya kamace ta ba karatu ne, amma tunda haka ne zata sa a kawo mata washe gari.
Sai a wannan lokacin Aysha ta sake har ma ta samu taci abincin sosai tunda dama yunwa take ji.
Ko da Hajiya ta koma daki mamaki take yi a ranta tana tausayawa Hafeez idan aka cigaba da tafiya a haka, gani takeyi nan gaba ba qaramar matsala za a samu ba.
Hakan ne kuma yasa da suka qara waya da Hafeez cikin dabara ta manya ta yi mishi fada akan ya dinga tanqwara Ayshan tun da sauran quruciyar ta, ya kuma saba mata da nuna mata ba kullum ake son abu ake samu ba don tana hango matsala a gaba idan akaci gaba a haka.
Duk da bata gaya mishi haqiqanin abinda ya faru ba amma shi kanshi yaji a jikinshi cewa akwai matsalar.
Ya kuma tabbatar da hakan ne wani zuwa hutu da yayi sau daya kafin wannan dawowar tashi, duk da yayi farin ciki da sauyin da aka samu na wayewar Ayshan, saidai a daya bangaren wasu halayyar nata yaji yana so ya canja mata.
Ya fahimci tana matuqar son 'yan uwanta wanda hakan ba laifi bane amma yanda take nuna kamar duk abinda Hafeez yayiwa mahaifiyar shi sai yayiwa innar ta abun na matuqar bashi mamaki.
A iya yan kwanakin da ya ta6a haduwa da innar ta da kuma yayar ta sai yake ganin kamar bazasu zuga ta ba, idan ma da ace baban ta ne take yiwa wannan campaign din sai yace shi yake zuga ta, to saidai ita sam Baban ta ma bai dame ta ba, bai kuma ga laifin ta ba tunda halin shi ya jawo mishi duk da kuwa ya kan mata fada kan duk lalacewar shi dai baban ta ne.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now