Chapter 22

56 3 0
                                        

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                                *22*

Kano city, 2012.

Kwanci tashi yau kwanaki bakwai kenan da rasuwar Alhaji Mustapha yareema.
Mutuwar da ta girgiza dubban al'umma bare kuma ahalin gidan shi mafiya kusanci dashi.

"Ki daure kici abincin nan uwata, ke kadai suke jira"
Abun mamaki wai gwaggo Mero ke lalla6a Hadeeza kan taci abinci.
Ita kam yanda gwaggon ta ta da Maman Taha da take ganin sun tsaneta suke nuna damuwar su akan ta kwanakin nan har abun yana bata mamaki.
Duk da cewa kuwa ba wani abun mamaki bane duba da yanda mutuwar ta dake su musamman ma Hadeeza da ta kwana 3 a asibiti tun da ta samu labarin mutuwar.

Bazata iya fadar yanda akayi har ta ganta a asibiti ba bayan ta samu labarin mutuwar Abban nata.
Saidai abu daya ta sani shine bata san ma sanda akayi jana'izar shi har aka kai shi ba don bata farfado ba.
Ko da ta farka aka tabbatar mata da hakan tayi kuka tayi baqin ciki, saidai ta yarda Abban yana gidan shi na gaskiya wanda ko ba dade ko ba jima ita ma zata je.

Ta lura tunda aka sallamo ta daga asibiti kowa ke haba haba da ita, duk da dai ta lura hatta sauran 'yan uwan ta ma ana kulawa dasu tunda su ma duk mutuwar ta dake su.
Ummi kuwa wani abun Al'ajabi da ya same ta shine yanda ko kusa bata iya wata magana da ya wuce amsa gaisuwar mutane da kalaman da basu wuce daya zuwa biyu ba.
Mutuwar mijin nata tazo mata a lokacin da bata ta6a tsammani ba dole bakin ta ya rufe ta shiga damuwa.

Idan akwai abinda ke 6ata ran Hadeeza a zaman makokin nan bai wuce yanda mutane ke wadaqa da abinci da lemuka ba tamkar wani gidan biki.
Dadin dadawa kuma ga 'yan siyasa dake ta faman safa da marwa a gidan wadanda suka kasance 'yan jam'iyyar Abban nasu da ma 'yan Jam'iyyar adawa.
Duk da suna kawo musu kudade ne da ma kayan abinci, amma sai take ganin kamar sun maida zaman makokin wani taro ne na siyasa ko kuma campaign din wani daga cikin 'yan siyasar tunda talakawa basu fasa hayaniya ba idan sun gan su.
Baqin cikin ta ma bai wuce zuwan shugaban qasa da wasu gwamnoni ba da har ya tara jama'ar da basu ta6a tsammani ba cikin unguwar ma ko tace kanon baki daya.
Abin takaicin ma wai har da 'yan jarida da gidan talabijin masu daukar abubuwan dake faruwa kamar wani biki.

Hakanan take jin cewa duk baaqin da suke zuwa dinnan ba wai don Allah suke zuwa ba. Daga dai talakawa da zasu zo don samun abincin da zasu ci su tafi dashi, sai kuma Attajirai da 'yan siyasar da zasu zo don biyan buqatar su da kuma nuna matsayin su cikin Al'umma.
Ko a yanzun ma da take zaune ta tusa abinci a gaba takaicin ta bai wuce da aka zo aka ce Ministern lafiya yazo ba wai suje su gaisa.

Yanzu da duk Abban nata yana da irin wadannan mutanen dayawa daga cikin su basu zo sun duba shi ba sai yanzu?
Ta sani lafiya ta Allah ce amma sai take jin kamar ministern lafiya yana da yanda zaiyi a bullowa lamarin Abban nata da ace yazo ko sau daya ne ai zai tursasa Abban ayi abinda ya dace amma bai ta6a ko zuwa ya duba shi ba.

"Deedee, yaya Haidar yace kiyi sauri ke ake jira".
Hadeeza taji dasashshiyar muryar Teema da tasha kuka ta fada.

Ita kam ta gaji da wannan kiran, babu dama su zauna zaman awa guda ba a ce wani babban baqon yazo ba da zasu je su gaisa.
Tabbas da ace tana da inda zata gudu da tuni ta dade da guduwa ko zata samu salama.
Miqewa tayi tana gyara Hijabin dake jikinta ta ta riqe hannun Teema suka wuce.

Kamar dai yanda aka saba shi din ma gaisuwa ce da wani tarihin yanda suka yi zaman mutunci da Abban, sannan ya dauko maqudan kudi ya basu bayan Alqawarin cewa idan suna da matsala kowanne lokaci su tuntube shi kansu tsaye zai biya musu ita.
Sun riga sun saba da jin irin wadannan alqawuran nasu na 'yan siyasa, sannan kuma Abban su yasha fada musu ko bayan ranshi kada su sa ran cewa wani abokin shi zai taimaka musu domin basu da tabbas, su kama 'yan uwan shi dakyau sune yasan duk lalacewa bazasu bari yaranshi su tagayyara ba.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now