🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*19*
Sokoto 2020,
Duniya cike take da damuwa da qalubale kala kala, takan juya maka a lokacin da baka ta6a tsammani ba, ko dai ya kasance juyin na farin ciki ne ko kuma na baqin ciki.
Ire iren wadannan juyikan Jamila ke fuskanta a rayuwar ta a halin yanzu, har kuma ta rasa gane inda wannan juyin zai kaita.Da fari bayan gano sakamakon cutar dake damun ta, tayi baqin ciki na wani lokaci kafin ta kwantar da hankalin ta ta dauki hakan a matsayin hanyar samun Hafeez a rayuwar ta.
Tabbas Hafeez ya taimaka sosai wajen taya ta goge damuwar ciwon dake damun ta, wanda hakan ya cigaba da tsunduma ta cikin kogin qaunar shi ba dare ba rana.
Tana son shi da dukkan jikin ta da ruhin shi, musamman a iya zaman su na dan wannan lokacin bayan tafiyar Aysha.Duk da cewa daga baya Hajiyan Hafeez ta dawo gidan da zama, kamar yanda ita ma Jamilan taga dacewar hakan tunda babu wani babba a tsakanin su cikin gidan, saidai sam hakan bai hana Hafeez cigaba da damuwa da damuwar ta ba.
Sau dayawa ya kan kirata musamman da yaran shi suyi hira, ko kuma yace su tafi wajen wasan yara wanda a nan sukan yi hira da tun bata sakin jikin ta da shi har ta fara.
Ta kan bashi labarin makaranta ko kuma abinda ya faru a quruciyar ta da makamantan su, wani lokacin shima ya kan bata nashi idan na dariya ne suyi idan na baqin ciki ne su jimantawa juna.Abinda Hafeez bai sani ba shine da duk wani kusanci da suke qarawa, da yanda zuciyar Jamila ke qara fadawa tarkon son shi.
Saidai tana iya qoqarin ta taga a matsayin ta na 'ya mace batayi abinda zai sa kimar ta ko mutuncin ta su zube a idanuwan shi ba.
Hakanan kawai sau dayawa takan ji haushin shi na yanda ko sau daya bai ta6a furta mata kalmar so ba gashi har sun gama jarabawa zata koma gida.
A kullum tunanin ta bai wuce ace yanzu da zarar ta koma shikenan sun rabu da Hafeez da yaran ba sai kuma randa Allah ya hada su.
Hatta Hajiyan Hafeez ma a yanzu sunyi sabon da tabbas ko da Jamila bata son dan ta bata burin ta rabu da ita.Iya zaman ta da Hajiyar ta lura mace ce mai kima da kuma kau da kai akan abinda bai shafe ta ba. Ta lura Hajiyan tana da matuqar kirki da kyautatawa mutane musamman na qasa da ita.
Ta kan ja Jamilan a jiki tayi mata nasiha sosai kan riqo da qaddarar da Allah madaukaki ya dora mata.
Ta kan ce mata "kiyi farinciki 'ya ta, ubangiji ya za6e ki ya jarabce ki saboda irin son da yake miki."
Ire iren wadannan kalaman na Hajiyan sun taimakawa Jamila sosai wajen cire tarin damuwoyin ta da maida hankalin ta wajen karatun ta.
Dadin dadawa Hajiyar har magungunan da aka dora Jamila da Hafeez din akai, ta kan tabbatar da cewa sun sha su akan lokaci musamman ma ita Jamilan.
Ita kam sam bata ga aibun Hajiya ba kamar yanda Aysha tasha fada.
Ita kam ko kusa bata ga abin qi a tare da Hajiyan ba ko kuma abin gudu a tare da ita ba.
Ita kam tana ganin Hajiyar a matsayin uwar da kowanne d'a ko suruka zasuyi Alfahari da ita.
Shiyasa ma ko a yanzu da take hada kayanta na tafiya gida take jin haushin rabuwa da Hajiyan, d'an nata da kuma jikokin ta.Cuccusa kayan kawai take domin ita kadai tasan abinda take ji a ranta.
Da ciwo kaso abu ba tare da ya san kana son shi ba, da ciwo kuma kasaka ranka akan abu kuma ka tabbatar wa da kanka bazaka samu ba.
Shiyasa ko a yanzu ma zuciyar ta ke qunar da ta saukar mata da zubar hawayen ta.
Shikenan yanzu ta gama karatun ta ta kuma bar sokoto kenan sai dai ziyara? To ziyarar ma wajen wa zata zo tunda basu da wasu 'yan uwa? Ita kam idan har ba kar6ar sakamakon ta na makaranta ba bata jin akwai abinda zai sake dawo da ita garin.Qarar Abulkhairi da taji shi ya katse ta daga tunanin ta ta fita daga dakin da sauri don ganin abinda ke faruwa.
Abulkhairi ta gani wajen dining table flask din ruwan zafi ya fado mishi a qafa shine yake wannan ihun, gashi babu kowa a wajen.
Da gudu ta qarasa wajen tana dauke Abulkhairin, banda kuka babu abinda yake yi.
Duk sai ta rasa inda zata nufa ma da Abul din duk ta rikice gashi sai faman kuka yake tana lallashin shi don itama gab take da fara nata kukan.
![](https://img.wattpad.com/cover/146407140-288-k405691.jpg)
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
General FictionLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!