Chapter 18

49 2 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

Salamu alaikum! Ya muke ya haquri da juna?
Lol!
Kwana 2 na zama busy ne sakamakon rashin lafiyar Mahaifiyar ta, wanda hakan yayi consuming tym dina har bana samun lokacin da zanyi typing.
Amma Alhamdulillah yanzu jikin nata da sauqi, Allah ya qara mata lafiya da sauran Al'umma baki daya.
Ina farin cikin sanar daku kuma next chapter din mu zamu ta6o Hafeez da Mila muji yanda suke, tunda wasu suna complain sun soma manta su😅.
Nagode muku, Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfane mu duniya da lahira.
Kar a manta 'yan Wattpad a dinga votes da comments, haka ma 'yan whatsapp a ringa comments please.

                                *18*

Kano city, 2012!

Gidan gaba daya ya kacame da hidima tamkar wanda zasuyi baqi daga bangon duniya.
Qamshin girki kala kala ke tashi cikin gidan da kuma qarar kwanuka a kitchen.

"Ni Aminatu! Wai yaran nan kuna da hankali kuwa? Duk wadannan abincin cikin wa zaku zuba shi?"
Ummi ta fada a lokacin da take shigowa kitchen ganin yanda dukkansu suka bazama da aiki.

Hadeeza dake aikin hada coleslaw kuma ta kasance mafi kusa da speaker da suka kunna kida ne ta rage volume sannan ta maida kallon ta ga ummin tace "kai ummi mutane dayawa mana, kinga fa banda mu da ma'aikatan gidannan ko iya 'ya'yan Abba mudan ai sun isa su gama da wannan abincin".

Dariya Maryam dake yiwa cake din da tafi kama da ta birthday kwalliya tayi tace "kinsan ko jiddah zata cinye rabin abincin nan kuwa"

"Wayyo Hannu na" Teema dake juya pepper chicken kan wuta ta fada a shagwabe tana duba hannun dake mata zafi sakamakon qonewar da tayi.

Dukkan su maida kallon su gareta sukayi inda ummi tayi saurin qarasawa inda take tana tayata duba hannun sannan tayi mata tofi a wajen tana mata sannu.

"Ni ban ma san dalilin da zai sa su baki aikin nan ba, ga irin ta nan ai yanzu kin qone, matsa ni in qarasa".
Lokaci daya maryam da Hadeeza suka kalli juna kafin su maida kallon su ga ummin da tayi magana.
Su kam har sun gaji da mamakin yanda ummi ke lalla6a teema wai a dole auta.
Sun sani ko kusa ummi bata da wasa akan yaranta musamman ta wajen aiki, shiyasa tunda akayiwa wata tsohuwar mai aikin su aure ma ummi ta hana a sake kawo wata, a cewar ta sunyi girman da zasu iya girki da gyaran dakunan su da wanke wanke.
Sharar cikin gidan da goge goge kuma akwai Habu mai yi safe da yamma yakan yi cikin gida, inda Abbati da dan gidan lawwali me gadi ke yin ta harabar gida da bawa shuke shuke ruwa.

Ummi tana da doka da tsari sosai, takan tsaya tsayin daka ta yi aikin ta na girki ko kuma ta raba musu suyi, hatta da mazan ma idan suna nan dole su ta6uka wasu abubuwan, ko wanke wanke ma raba musu take da zarar sun gama cin abinci da wanda zaiyi.
Amma sau dayawa Teema kan yi shagwa6ar ko taji ciwo ko wani abu kuma sai ummin tace a qyaleta wani yayi wai ai da sauran ta.

"Hajiya ummi ikon Allah! Yanzu da Nice ko Deedee da tuni kince dan wannan qunar mun fara ihu, amma dayake wannan yarinyar ce har kina fadan an sa ta aiki mai wahala"

"Bari 'yar uwa, dadin abun ma ita ta za6i aikin da kanta. Kwadayin naman ta yaja mata"
Hadeeza ta qarashewa Maryam suka tafa suna dariya.

"Ummi kinji su ko" Teema dake gefen ummi ta fada tana turo baki.

"Ya ishe ku, idan ma tayi kwadayin ai a gidan su tayi ba gidan wani taje tace a bata ba, Kun samu ma tana iya qoqarin ta ta taya ku aikin?"
Ummi ta fada tana maida kallon ta ga su Hadeezan.

"Hmm" Hadeeza da maryam suka fada a lokaci daya suna cigaba da aikin su.

"Yauwa yaya Maryam, a jikin cake dinnan haka zaki sa Happy birthday "Abban Teema" tunda dai ai nice auta."
Teema ta fada bayan wani lokaci da kowa yayi shiru yana aikin shi.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now