Chapter 38

65 4 1
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                             *38*

Kano city, 2022.

Tunda ta tashi daga wayewar gari zuwa yammar nan take jin rashin dadin jikin ta.
Ji take yi tamkar an mata dukan tsiya, baki daya ga66an jikinta ciwo suke.
Sauqin ta ma daya da ya kasance weekend ne, Mahmoud da little suna gidan Daddy.

Wanka tayi ta shirya cikin wata doguwar rigar ta, bata jin sha'awar komai don haka ruwan lipton kawai ta sake hadawa tana sha.

Al'amarin farko da ta fara cin karo dashi a yanar gizo bayan bude wayar ta na mutuwar yarinyar da bata ji ba bata gani bane.
Yarinyar da bata gama sanin kanta ba bare ta san me duniya take ciki.
Yarinyar da bata dauki hakkin kowa ba, bata cutar da kowa ba amma aka salwantar da rayuwar ta.

Kuka sosai take yi ganin yanda aka daddatsa yarinya qarama kamar wannan aka saka a buhu.
Kuka sosai take yi ganin yanda iyayen Yarinyar ke bayani cike da radadi a zukatan su.

Ta rasa me mutane suke nema a rayuwar su, ta rasa wacce iriyar masifa da jarabar neman duniya ce zata sa dan Adam ya aikata irin wannan aikin.
Gashi dai bata san yarinyar ba, basu hada jini ba amma zuciyar ta sosai take mata ciwo da mutuwar yarinyar.
Tunanin ta bai wuce irin halin da iyayen yarinyar suke ciki ba, halin da zasu cigaba da kasancewa a duk sanda suka tuna rabuwar su ta qarshe da yarinyar ta su.

Duk yanda taso ta hasaso zuciyar ta ace hakan ga Mahmoud ko little ya faru sai tunanin ta ya sauya, to ina kuma ga iyayen yarinyar?
Ai ko babu hisabi, ko babu ranar tashin qiyama Allah bazai bar duk wanda zai iya aikata wannan danyen aikin ga dan Adam ba.

"Allah ya jiqan ki Haneefa, Allah ya bawa iyayen ki haqurin rashin ki".

Ta fada tare da goge hawayen dake zuba a idanun ta.

"Amin ya Rabbi. Allah ubangiji ya cigaba da tona asirin azzalumai, Allah ya dada tsare mu da sharrin masu sharri".

Sam bata ji shigowar shi dakin ba, bata ji zaman shi a gefen gadon ba ma.
Muryar shi kawai taji ta daki kunnuwan ta.

"Sarkin kuka".

Ya fada tare da gyara zaman shi.

Hararar shi tayi, hakan yasa shi murmushin dake matuqar qara mishi kyau a idanun ta.

"Nazo miki da albishir, amma tunda harara ta kike bari na koma da kayana"

Ya fada yana miqewa.

Jawo hannun shi tayi, tare da marairaice fuska.

"Allah sai ka fada min".

Kallon ta yayi yaga har lokacin bata daina hawayen nata ba, don haka ya koma ya zauna.

"Zan fada miki amma sai kin daina wannan kukan.
Nasani, ganin wannan tashin hankalin dole zai sa mutum mai imani a wani hali, amma dai kinsan condition dinki. Addu'a ya kamata kawai muyiwa yarinyar. Allah ya jiqanta da al'ummar musulmi gaba daya".

Share hawayen nata tayi, sannan ta qara fuskantar shi.

"To fada min, wanne albishir ne?"

"Sai kinyi murmushi tukunna".

Ya fada yana jawo ta jikin shi.

Murmushin tayi, shima ya mayar mata tare da shafa kanta.

"Guda biyu ne albishir din.
Na farko dai Teema ta sauka, su little an samu qanwa"

Zame jikin ta tayi daga nashi, cikin murna tace "Dan Allah da gaske?, yaushe? Shine basu kira ni ba?"

"Yanzu ba dadewa, nima ina hanyar dawowa suka kira ni. Sai gobe zasu Taho kano ma".

QADDARAR MU CEWo Geschichten leben. Entdecke jetzt