Chapter 11

59 4 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

Salam, ina mai baku haquri sakamakon dogon hutu da na dauka na kwanaki, saidai ina mai tabbatar muku da duk abinda zai sa na yi kwanaki ba tare da posting "qaddarar mu ce" ba to babban uzuri ne, kuma ina fatan zaku kar6e shi.

Ina fatan a duk lokacin da kukaji ni shiru ba tare da nayi posting ba zaku yi min fatan Alkhairi da Addu'a ku kuma yarda da cewa duk sanda na samu damar yin hakan zanyi.
Wannan shine kadai hanyar da zaku biya ni ko da kuwa bangani ba ban kuma ji ba. Nagode da duk qaunar da kuke nunawa labarin.😊🥰
🙏🏻Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfane mu baki daya..

                               *11*

Wata ajiyar zuciya ya sauke mai ringimemen nauyi ya sauke lokacin da yaji cewa "An daura auren Hafeez Huzaifa Danladi da Aishatu Abdulhameed yaro akan sadaki naira dubu 20 lakadan ba ajalan ba".
Ya kasa gane me yake ji, ya kuma kasa fahimtar gaske ne ko mafarki ma. Ji yake kamar ba shi ba, duk da cewa gashi zaune cikin masallacin kuma cikin babbar riga, amma ya kasa yadda wai shi Hafeez ne aka daurawa aure.
Ya sani shi ya nema, ya kuma sani da amincewar shi akayi komai, amma sam bai ta6a tunanin zaiyi aure a shekarun shi na 25 ba, bai ta6a tunanin zaiyi auren da ba na soyayya ba, bai ta6a tunanin zai yi aure don tausayi ba, bare kuma yayi tunanin zaiyi auren je ka ka gani.
Eh! jeka ka gani mana tunda mahaifiyar shi bata amince da auren ba.
Tayi mishi gargadi mai tarin yawa lokacin da ya zo mata da buqatar shi, ta fada mishi cewa ba kowanne lokaci ne tausayi ke haifar da abinda ake so ba, ba wai bata son Ayshan bane, ba wai kuma bata son ta hada jini dasu bane tunda bata ma san su ba sai daga abinda Hafeez din ya fada mata.
Fargabar ta kawai rashin sanin abinda gaggawar zata haifar, rashin sanin ainahin cikakkiyar tarbiyyar Ayshan, duk da kuwa Hafeez din ma bai sanar da ita komai akan Baban Ayshan ba.
Ya dai fada mata kawai baban ta yana shirin aurar da ita ga wanda bata so saboda mijin da zai aureta ya fasa sakamakon ganin ta da Hafeez da yayi yana qoqarin rage mata hanya.

Saidai sam Mahaifiyar Hafeez ta gaza gamsuwa da wannan maganar ta Hafeez, taji kamar akwai lauje cikin nadi, taji kamar dan nata zai kinkimo abinda bai isa ya dauke shi ba.
Tana da burin yayi aure, tana kuma da burin ya hayayyafa, amma ita burin ta ya gina kanshi tukunna. Ya gama service ya dora da masters ya samu aiki ya bawa kanshi rayuwar da shi da iyalin shi bazasu wahala ba, domin kuwa tun akan sadiyan shi tayi alwashin samarwa dan nata rayuwa mai kyau ta yanda ba zai sake rasa wani abu don bai kai ya same shi ba.
Shiyasa ta kasa gane rashin fa'idar auren, shiyasa ta kasa amincewa, shiyasa ta gargade shi, ta hane shi, ta kuma fada mishi yana buqatar lokaci amma yaqi ji.
A ganin ta Hafeez kawai yana son yayi auren huce takaici ne tunda ya rasa sadiya, a ganinta Wauta ce tasa yake shirin auro wata yarinya da shi kanshi ba son ta yake ba. Hakan ne ma yasa tace bata lamince ba da taga ya matsa, ta kuma ce ko yayi ya sani ba da amincewar ta ba.

Kasancewar Hafeez mai naci a duk abinda ya sa gaba, hakan yasa shi ya dinga bin duk wanda yasan ya isa ya fadawa Hajiyan tashi taji. Tun daga kan babban yayanta, har zuwa yan uwan mahaifinshi da su suke ganin hakan ma kamar wani Alheri ne tunda zai yi aure, auren ma kuma na 'yar Garin zazzau din da ya kasance asalin Hafeez.
Ba wai don ta so ba, ba kuma don maganganun su da hujjojin su sun shige ta ba tace yaje yayi. Ta kuma kira shi ta sanar dashi ba wai tana qin yarinyar bane, tana qin abinda zai biyo baya ne na gaggawar da ake yi, don haka yaje yayi, amma kada ya zarge ta da duk wani matsala da aka samu.
Hakan ne ya bawa Hafeez damar tura yan uwan mahaifin shi nema mishi auren Aysha.
Duk da cewa su kansu kawun Hafeez da mijin gwaggon shi da wani qanin kakan Hafeez din sunyi mamakin yanda sam Malam audu mahaifin Ayshan bai yi wani tsatstsauran bincike akan su ba kuma yace ya basu, amma sai suka alaqanta hakan da kasancewar su fitattun mutane a zarian da kusan kowa ya sansu a fannin daukaka da kasuwanci.

QADDARAR MU CEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora