🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*26*
Kano city, 2012.
"Ummi........"
"Bana son jin komai, ki fita kawai, fita don Allah".
Ummin tayi saurin katse Hadeezan tare da nuna mata qofa da yatsun ta.Miqewar tayi daga gefen gadon da take zaune, saidai kuma ta qi fitar kamar yanda Ummin ta umarce ta.
"Ki yi haquri, don Allah ki yafe min. Ki daina fushi dani".
Hadeezan ta furta a gajiye, da dukkan magiya cikin muryar ta.Ta gaji da matsalolin, ta gaji da fushin kowa, ta gaji da wannan tension din na cikin gidan su da dangin su.
Ta rasa me yasa son wani zai zama wani babban zunubi da ta aikata wanda kowa zai dinga fushi da ita.
Babbar damuwar ta ma wanda yafi kowa daukar abun da zafi itace Ummi.
Ummin ta fa wadda ta ke ji cikin ranta fiye da kowa da komai.A baya daa za a tambayi Hadeeza wanda tafi so fiye da komai Abban ta ne, kuma har yanzu ma har kwanan gobe shine take so fiye da kowa.
Saidai mutuwar Abban ta ya qara musu shaquwa matuqa tsakanin ta da Ummin su, shaquwar da a baya basu samu ba.
Shaquwar da tausayin junan su ya zama silar qullata, shaquwar da a yanzu Hadeeza take nema a tare da Ummin da yanzu take gudun ta, ko kuwa tace ma bata son ganin ta."Bana son ganin ki, ki fita don Allah"
Ummin ta maimaita, tare da tabbatar wa Hadeeza cewar ta rasa wannan shaquwar tasu, ta kuma qara tabbatar wa a idon Ummin da kamar tana qyamar kallon ta.Fitar tayi da sauri tare da rufowa Ummin qofa, sakamakon wasu hawaye da taji suna qoqarin ziyartar fuskar ta.
A bakin qofar sukaci karo da Maryam da ke qoqarin shiga dakin ummin wadda da Alama daga makaranta ta dawo.
Ta lura da irin kallon banzan da Maryam ke mata, saidai yanzu ba Maryam ce damuwar ta ba don haka ta wuce abinta ba tare da ta tanka mata ba.Ko da Maryam ta shiga a zaune taga Ummi jingine da gado ta daga kanta sama , da ta qarasa kuwa gab da Ummin Hawaye ta gani na zuba a idanuwanta, wanda hakan yasa Maryam yadda jakar da ta dawo daga makaranta a gefe tare da zama gab da Ummin.
"Ummi....
Don Allah indai akan Deedee ne kike wannan kukan ki daina. Ki rabu da ita tunda ta dage kiyi mata fatan Alheri ki zuba mata ido. Idan Qaddarar ta ta rubuta mata auren wannan mutumin mu bamu isa mu hana ba.
Nasan da ciwo akan abubuwan da tayi, nasan kina jin ciwon yanda ta za6i wani fiye da mu. Nasan dole zakiji babu dadi, amma don Allah kiyi haquri. Ki daina damun kanki kar hakan ya jawo hawan jinin ki ya tashi".
Maryam ta furta cikin nutsuwa ba tare da sanin cewa ita kanta tana da wannan nutsuwar ba.Ta riga ta gama duk nazarin da zata yi taga hanyar da suka dauka bazatayi maganin Hadeezan ba ko kuma tasa ta canja.
Taurin kai a jinin Hadeeza yake, son kanta ma a jinin ta yake shiyasa bata damu da kowa ba sai kanta.
Shiyasa ma ta rabu da Taha ta qeqashe idon ta ba tare da ta damu da nasiha da lalla6in da suka mata ba akan ta rabu da wancan kodadden Mujaheed din.
Shiyasa da Ummi ta rantse cewar bazata auri wani ba sai Taha har ta kai qara wajen Uncle bature wanda dole sai da yazo kano akan maganar.Ko da Uncle bature yazo a gaban shi da Daddy da Ummi da shi kanshi Tahan ta qara maimaita bata son shi, kuma ita tana da wanda take so take kuma burin aura.
Sosai hakan ya daurewa kowa kai musamman ma Ummi da take ganin Hadeeza ta za6i fushin ta shiyasa taqi barin maganar kamar yanda ta umarce ta."Dukkannin ku 'ya'ya ne, bazan so abinda zai cutar daku ba. Kuma dukkannin ku ina da ikon za6a muku abinda naga zai dace daku amma bazan muku dole ba.
Idan kinga cewar wancan din shine abinda kike so kuma kin tabbatar da hakan, to ki fada mishi ya turo magabatan shi don a san abinda za a yi.
Ranar aure dai bazata canja ba, komai zai kasance yanda aka tsara shi."
![](https://img.wattpad.com/cover/146407140-288-k405691.jpg)
KAMU SEDANG MEMBACA
QADDARAR MU CE
Fiksi UmumLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!