Chapter 14

73 2 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

Ramadan kareem to all "Qaddarar mu ce" fans... Allah ya 'yanta mu cikin bayin da zai 'yanta a wannan wata mai Albarka. Allah ya datar damu yasa mu gama azumin nan cikin sa'a. Amin.
                           
                              *14*

Tafiya take tamkar tsohuwar mahaukaciyar da ta shekara goma tana hauka ko kuma ince tsohuwar mara lafiyar da ta dade tana jinya.
Ko kadan bata hayyacin ta, bata kuma cikin nutsuwar ta.
Duniyar ta mata zafi fiye da tunanin mai tunani. Mamaki ma take ta yanda duniyar da ta aura zata juya mata baya lokaci guda.
Duka duka ba'a kai biyu da faruwar komai ba amma komai nata ya lalace, wannan kadai ya isa ta gane cewa duniyar budurwar wawa ce.

Wata bishiya mai dayke da inuwa saboda tsananin cikar ganyayen ta ta samu ta zauna a qarqashin ta bayan ta siya ruwa mai sanyi a wani shago lokacin da take tafiyar.
Ji tayi wasu Zafafan hawaye na ziyartar kuncin ta a lokacin da take shan ruwan.
Ita kam ta dade tana jin ana cewa abinda ka shuka shi kake girba amma ko kadan bata san cewa girbar abun baya daukar lokaci ba kamar yanda nata yayi.

Har yanzu ta kasa goge hoton Al'ameen da Mimi qawar ta abokiyar shawarar ta kwance a gado daya suna lalata.
Ko kusa ko a mafarkin ta bata ta6a kawo cewa Mimin zata ci amanar ta ba duk da kuwa tasha jin labarin Al'ameen din yana kula wasu matan Amma sam ita bata kawo a jerin yan matan da take ganin ma kamar sharri ake mishi zai kula mimi da tun farkon Alaqar su yasan qawar Ayshan ce kuma aminiyar ta.
Amma sai gashi ranar da ta nufi gidan shi bayan tabbatar da sakamakon gwajin ta da Hafeez a asibiti, sai ta tarar da abinda yafi sakamakon gwajin nata tashin hankali.

Ta yaya zata manta cikin yanayin da ta riske su? Ta yaya zata manta yanda sukayi tsilli tsilli da ido a lokacin da ta riske su?
Ta yaya zata manta yanda Al'ameen da Mimin suka nuna halin ko in kula lokacin da take sanar dasu cewa suna dauke da cuta mai karya garkuwar jikin?

"To ke sai yau kika sani?
Well, welcome to the club. Sai ki fara shan magani kafin lokaci ya qure miki."
Amsar da Al'ameen ya bata kenan lokacin da ya ke qoqarin zira jallabiyar shi.
Mimin kuwa da gaba daya zuwan Ayshan yasa ta takurewa gefen gado tuni Aysha ta nufe ta tana qoqarin shaqa ta tana huci tamkar wata zakanya.

"Kema kin sani mimi? Kin sani kika 6oye min? Tun yaushe? Tun yaushe kike tare da Al'ameen? Tun yaushe kike cin amana ta mimi?"
Ayshan tayi tambayoyin lokacin da take cakumar wuyan mimin.
"Ke ke da Allah sake ta, sake ta nace"
Al'ameen ya fada a tsawace lokacin da yake raba Ayshan da jikin mimin.

Ganin hakan ne ya bawa mimi qwarin gwiwar maidawa Ayshan martani, sanin cewa babu abinda ta isa tayi mata tunda Al'ameen din yana tare da ita.
"Tun lokacin da kika gama kwadaita min dadin samun Al'ameen a matsayin saurayin ki, tun lokacin da kike 6oye mishi sirrin aurenki ni kuma nayi amfani da damar wajen tona sirrin ki da kusanta kaina dashi.
Maganar HIV kuma wannan ba sabon zance bane, tuni ni da Al'ameen mun dade da sanin wannan tun kafin mu fara tarayya kuma muna magani yanda ya kamata. Kuma da kike maganar cin amana, ai ni ta qawance naci, ke kuma da kika ci amanar auren ki me za a kira ki dashi?".

Aysha da tuni taji kanta yana wani mugun sarawa bangon dake mafi kusa da ita ta dafa.
Gaba daya ta rasa gane dalilin da yasa ranar tazo mata da abubuwa masu muni da bata ta6a tsammani ba.
Da fari samun labarin cutar ta da yanda Hafeez ya nuna fushin da tsawon shekarun su bata ta6a gani ba, daga baya kuma wanda ta gina zuciyar ta da soyayyar shi ta fifita shi fiye da mijin ta na sunna shi ta kama kwance da aminiyar ta abokiyar shawarar ta da ta dau yardar ta da amanar ta ta bata, yanzu kuma ga ta a gaban ta tana mai da mata martani har ma da samun labarin lokacin da suka dauka tare da yanda suka munafince ta suke nemawa kansu sauqi daga cutar da sai a ranar ta samu labarin ta.
Dadin dadawa ma abinda ya dada bata mamaki yanda mimin take mata magana babu tsoro ko ladabi.
Duk da cewa qawar ta ce kuma aminiyar ta amma tsawon lokacin da suka dauka tare mimin a qasan ta take, umarnin ta take bi, tsoron 6acin ran ta ma take yi, amma sai gashi tana kallon qwayar idanunta ba tare da kunyar ma laifin da ta kamata tana aikatawa ba wai tana maida mata martani.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now