Chapter 2

119 7 0
                                        

*QADDARAR MU CE*

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                     *2*

Ko da Hafeez (Abu Mahmoud) yayi parking a harabar asibitin bai fito daga motar ba sai da ya kira Hadeeza ta fada mishi ward din da kuma Number dakin da suke, da Hanzari ya nufi cikin asibitin yana dube dube har ya isa inda Hadeezan ta fada mishi..

Zaune kuwa ya sameta ta kifa kanta a kujerar dake kusa da gadon tana aikin rera kuka, ga Mahmoud kuma dake ke kwance akan gado kamar matacce, Hakan ba karamin razana Hafeez yayi ba don haka ya qarasa har inda suke a hanzarce domin Har ga Allah zuciyar shi ta raya mishi Yaron ya mutu ne.
Sai da yazo dab da gadon mara lafiyan ya qare mishi kallo sannan ya lura da alamar Rai a tare da yaron, Wata ajiyar zuciya ya sauke yana furta "Alhamdulillah" can kasan makoshin shi.
duk da cewa ya lura da yaron na jin jiki amma hakan yafi ace mutuwar ce.
Samun guri yayi a gefen gadon ya zauna yana sauraron kukan da Hadeeza take ta faman rerawa, abinda ya bashi mamaki har yanzu kanta a kife yake alamar cewa bata ji qarar bude kofar shi da takunshi ba ma bare zaman da yayi a gefen gadon dake dab da kujerar ta. Ba karamin tausayi ta bashi ba domin yana da masaniyar yanda take matukar kaunar dan nata, yana kuma da masaniyar irin halin da take shiga a duk sanda yaron bashi da lafiya. Amma a iya sanin shi Hadeeza mutum ce mai jarumta da kokarin boye halin da take ciki saidai a yau ya lura tana kukan duk wani ciwo da ta danne ne, tana kuka ne daga ruhinta, zuciyar ta da kuma idanunta.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Hafeez ya furta yana sauke wani numfashi.

Girgiza kujerar da Hadeeza take kai yayi yace "Babe, ki tashi gani nazo."
Da sauri ta dago kanta idanun nan sun hade da farar fatar fuskar ta sunyi jajur, ga wata majina da ke kokarin sauko mata daga hanci.
"Yaushe kazo? Sannu da zuwa" ta fada cikin dasasshshiyar muryar ta da ta tabbatar mishi da ta dade tana aikin kukan.
Handkerchief ya zaro daga Aljihun shi ya miqa mata "Goge fuskar ki tukunna, Your face looks like a red tomato 🍅 (Fuskar ki tayi ja kamar tumatur)" ya fada yana dan murmushi.
karba tayi tana harararshi inda shima yayi wani gejeren murmushi kafin yace "Tun yaushe?"
Ta gane tambayar tashi yana nufin tun yaushe suke asibitin ne don haka tace "kwana 3 kenan"
"What? Kina nufin yau kwanan ku 3 amma sai yau nake Sani Hadeeza?"
Hafeez yayi tambayar muryar shi cike da mamaki.
Ita kam Hadeeza shiru tayi mishi, to me ma zata ce mishi? Yaushe ma take da nutsuwar da zata kirashi tace mishi Mahmoud yafara jijjiga a lokacin da suke Home work dashi a gida kuma har yau bai farfado ba?. Jin tayi shiru ne ya sashi cewa
"3 freaking days Hadeeza, sai yau nake sani? Me kika dauke ni ne?"

"Ya salam" ta fada a zuciyar ta amma a zahiri sai tace "Kayi Hakuri, bani da wannan nutsuwar ne, wayar ma sai yau da safe da naje gida na dauko"
Sai a lokacin ya ji ya dan gamsu domin shi kanshi yasan ya kirata yafi sau 20 bata dauka ba, sanin da yayi sun dan samu matsala ne a haduwar su ta karshe ana gobe faruwar rashin lafiyar Mahmoud din yasashi tunanin ko fushi take dashi, hakan ne ma yasa shi niyyar biyawa gidan idan ya tashi daga aiki sai kuma ga kiranta wanda yasa shi zuwa asibitin a yanzu.
"Shikenan ya wuce, yanzu ya jikin nashi? Me aka ce yana damun shi kuma this tym?"
Gyara mayafin abayar ta tayi dake kokarin saukowa kasa kafin tace "to gashinan dai, tun ranar a haka yake, Dr ma'aruf yace dole sai anyi mishi transplant (dashen koda) this tym"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'u" Hafeez ya fada yana dafe kanshi.
"Anyi duk gwaje gwajen da ya dace dan a sa mishi nawa, amma yace bazaiyuwu ba saboda medical condition dina saidai a nemi wani shine ma dalilin da yasa na kira ka." Hadeezan ta fada ba tare da ta sanar dashi gaskiyar sabuwar cutar da a yanzu take da ita ba. A ganin ta wannan ba lokacin da ya dace bane.
"Yanzu an samu wanin ne?" Hafeez yayi tambayar yana duban Hadeeza.
Kallon da yaga ta mishi ne yasa shi gyara zancen shi da cewa "Ina nufin akwai wanda aka samu ko da na siyarwa ne?"
Girgiza mishi kai kawai tayi sannan tace "yace ba kasaifai ake samu ba, shiyasa ma yace kawai idan akwai wani nashi da zai bayar sai a nema, sannan yace bamu da lokaci mai tsayi na jira"

Tirqashi! Tashin hankali da ba a sa mishi rana.
Tabbas Hafeez ba qaramin kaduwa yayi ba domin idan ya fahimci zancen Hadeeza tunda ita ba za a iya daukan nata ba ya zama kenan shine 2nd option? yasani ya dauki Alkawarin rike Mahmoud tamkar dan da ya haifa, ya kuma sani yana son Hadeeza da tilon dan nata matuka domin Mahmoud yaro ne mai shiga rai, Hasalima Mahmoud shine silar haduwar shi da Hadeeza.. To amma duk da haka koda fa (Kidney) ba kmr jini bace da zai kwanta a cire salin alin.
"Kayi shiru baka ce komai ba" muryar hadeeza da ya ji ne yayi saurin dawowa daga tunanin shi. murmushin qarfin hali yayi mata yace "Ba komai zan samu shi Doctor din muyi magana za a yi abinda ya dace, shikenan ko?"
"Eh! Allah ya bada lada" Hadeezan ta amsa tana mai jin dadi a ran ta.
"Babu damuwa,ni bari naje zan dawo zuwa anjima inshaa Allah" ya fada yana miqewa sannan ya zira hannun shi a aljihu ya zaro kudin da a qalla zasu kai dubu 20 ya mika mata.
"ga wannan ko za a buqaci wani abu, ban tsaya siyan komai ba saboda duk kin daga min hankali" ya fada yana mika mata kudin.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now