Chapter 15

79 2 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

Jumaat mubarak & Ramadan kareem to u all.
Allah ya kar6i ibadun mu ya bamu dacewa cikin wannan watan mai Albarka.

                              *15*

Hafeez ne kishingide a kan kujerar parlour yana bin ta da kallon duk wani motsi da take.
Abubuwa da dama a tattare da ita suna bashi mamaki fiye da tunanin mai karatu.
Sam ya kasa daina mamakin yanda qaddara mai girma irin wannan zata samu mutumin da baiji ba bai gani ba kuma har ya samu qwarin gwiwar cigaba da gudanar da Al'amuran shi tamkar komai bai faru ba.

Ko kadan labarin cutar da jamilan ta samu bai hana ta cigaba da karatun ta ko kuma kula da yaran Hafeez din ba kamar yanda take a baya bare kuma yanzu da ta tabbatar babu Aysha.
Ko kadan fasa auren ta da akayi sakamakon lalurar ta ta bai sa ta karaya ba ko kuma ta daina gudanar da Al'amuran ta. Idan ma akwai abinda Hafeez ya lura dashi shine yanda hakan ya qara mata kusanci da ubangijin ta, da kuma yanda ta ke qara tausayin yaran nashi da kula dasu.

A yanzun ma kallon ta yake yanda take ta dawainiya da su Abul tun dawowar su daga makaranta.
Kasancewar ranar juma'a ce yasa babu islamiyya shi kuma Hafeez yana saukowa daga masallaci ya dawo gida.
Kamar ko da yaushe kuwa ya tarar ita da Raliya sun gama shirya komai na abinci an ajiye a dining table saidai ko kusa baya jin yunwar dan haka ya nemi kujera ya zauna.
Kishingidar shi ke da wuya yaga jamilan ta fito daga dakin su Abul riqe da Hannayen su sun nufi dining ta zuba musu abinci, amma ganin Baban nasu yasa su shagwabar su a parlour zasu ci don dole ba don jamilan tana son zama inda Hafeez din yake ba ta biyo su, don ko babu komai Hanan dole sai an bata a baki indai ana so taci dayawa.

Ita kam har yanzu ya kasa daina mata kwarjini, qimar shi kuwa ko kadan ta kasa raguwa a idanun ta.
Kai idan ma akwai abinda wannan qaddarar ta su ta haifar mata bai wuce qara son shi da tausayin shi da take a cikin ran ta ba.
Ita ma da kanta lokacin da iyayen ta suka zo da maganar lallai ta bar gidan Hafeez din ta koma cikin makaranta da zama tunda babu matar gidan taso hakan, ba dan komai ba sai dan ta nesanta kanta dashi da kuma abinda take ji a tattare dashi.
Saidai yanda Hafeez ya dage akan suyi haquri su bar ta zaiyi iya qoqarin shi wajen kare mutuncin ta, kuma tunda ba ita kadai bace babu abinda zai faru yasa dole suka haqura akan ta zauna din.
Hakan yasa Jamilan da kanta ba don wani ya sa ta ta yanke shawarar dawo da kayan ta qasa dakin su Abulkhairin tunda dama can ita da Ayshan da Hafeez ne a sama.
Sosai hakan ya qara mata kima da daraja a idon Hafeez din don duk da yana da yaqinin bazai ta6a aikata wani mummunan abu da ita ba amma yasan hakan shine abinda ya dace.

Ya lura tana iya qoqarin ta wajen suturta kanta a cikin gidan idan har Hafeez din yana nan.
Ta kan mishi dukkan ayyukan da yake buqata amma ko kusa bata shagala wajen manta cewar shi ba muharramin ta bane.
Kasancewar ta ma'abociyar saka doguwar riga, wanda da yawa ta wannan 6angaren take yiwa Hafeez din yanayi da Hadeeza yasa ko da yaushe kanta rufe yake da mayafin dogayen rigunan ta.
Ta kan kuma saka Hijabi a duk lokacin da take sanye da wasu kayan ko kuma idan zata fita.

A yanzun ma kallon ta Hafeez yake yanda take ta fama da Hanan da duk spoon daya sai ta zuba surutu take sake kar6ar abincin.
Kallo ne na abubuwa da dama yake mata bayan wannan.

Tunawa yake da irin kalaman da Ibrahim ya fada mishi ranar da yaje mishi da labarin an fasa auren Jamilan kuma hakan yana bashi tausayi.
"To ka aure ta mana, tunda ai yanzu babu wani Hijabi a tsakanin ku. Kuma ko a da din ma babu tunda ai ba uwar su daya uban su daya da Ayshan ba".
Ibrahim din ya fadawa Hafeez a waccan ranar da yaje mishi da maganar.

Saidai duk inda Hafeez ya so ya kushe abun ko ya nuna mishi rashin yiwuwar hakan Ibrahim sai yazo da wata hujjar.
Shi kam ya sani yanda Jamilan ta rasa nata saurayin shima ya rasa Hadeeza kenan, domin ko da Hadeeza zata nemi suyi auren a hakan ma bazai ta6a yarda ba don bazai iya cutar da ita ba.
Dadin dadawa ma ko da ya samu dama yaje asibitin da su Hadeeza suke ya samu labari daga wajen Dr.Ma'aruf cewa Hadeezan sun koma kano da Baban Mahmoud din wanda hakan ba qaramin tsoma Hafeez a tunani yayi ba.

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now