🌸QADDARAR MU CE🌸
🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)
*29*
Kano city, 2012.
Sallama da fatan Alheri zuwa ga kyakykyawar yarinya, son kowa qin wanda ya rasa, Dije na, Dijen Deeni.
Nasan zaki yi mamakin dalilin da yasa na za6i aiko miki wannan takardar a madadin kira ko text da na saba yi miki.
Saidai rubutuna a nan shi zai tabbatar miki da muhimmancin saqon, da kuma muhimmancin ki a gare ni.Me yiwuwa a yanzu kina cikin doki da farin cikin kasancewar wannan ranar, ranar da kike burin mallaka ta a matsayin mijin ki. Saidai kuma ina mai baqin cikin sanar dake cewa hakan ba mai yiwuwa bane, aure na dake ba abu ne wanda zai faru a yau ba ko kuma a nan gaba ma.
Banzo garin kano da niyyar haduwa da mace don na aure ta ba, haka kuma ban fara kula ki don na aure ki ba ko dan ina son ki, nazo ne kawai don gudanar da harqalla ta, harqallar da ko kusa bata da alaqa da wadda kike tunanin ina yi.
Nasan zaki ji zafi idan na sanar dake cewa dukkan abinda ya faru tsakani na dake nayi shi ne don kudi, ko kuma wani son zuciya ta, ba wai don soyayyar da kike tunanin ina miki ba, amma tabbas wannan shine gaskiyar magana.
Daga ranar da na gan ki naga kin min a matsayin budurwar da zan share lokacina da ita tsawon zamana a kano, kyawun ki, surar ki, da kuma jan ajin ki babu shakka sun jawo ni gare ki.
Saidai bayan na samu labarin gidan ku, da kuma kasancewar mahaifin ki tsohon dan siyasa, hakan ya bani damar kusanta kai na dake don samun abinda nake nema.Mata da yawa a garuruwa daban daban su suke kawo kan su gare ni har ma na samu damar da zan damfari iyayen su, amma na lura ke din ta musamman ce.
Kin so ki wahalar dani, kin so ki sa na canja sheka, saidai kuma Allah yayi ina da rabon ci a jikin ku, Allah yayi zan ci dukiyar da na tabbatar da ta al'umma ce tunda kudin siyasa ne, shiyasa Allah ya ara min dama har ta kai ga na samu abinda nake so.
Saidai ki sani nima ina da tawa hujjar na za6arwa kaina wannan rayuwar, sannan ki sani bana tsallake 'yan siyasa da 'yan kasuwa masu son zuciya wajen nawa kasuwancin.
Mai yiwuwa a yanzu bazaki gane ba, mai yiwuwa a qiyama idan da dama na fada miki dalili na na yin hakan, a duniya dai kam ina da yaqinin tsakanin mu ya zo qarshe.
Miliyan dari ne target dina akan ku, amma duba da irin gwagwarmayar da kika sha kafin a amince dani a gidan ku yasa na tausaya zuwa miliyan hamsin.
Saidai yayan ki yana da wayo, ko kuma mai yiwuwa Allah ne ya cece ku na tsaya a miliyan talatin.Ban san meyasa naji ina son sanar dake duka wannan ba kafin na barki, saidai nasan cewa ko a cikin 'yan mata na ina ji dake.
Ina kuma jin dadin kasancewa dake a ko da yaushe.
Saidai ban san dalilin hakan ba.Me yiwuwa abinda nake ji a kan ki so ne, me yiwuwa kuma sha'awa ce kawai, saidai ko ma menene ki sani ina son kudi fiye da komai na rayuwa ta, sannan zan iya yin duk wata dabara don na same su cikin duniyar nan, ko da kuwa hakan zai tarwatsa zuciyoyi da dama.
Ina so ki sani zan za6i kudi fiye da ke da ma kowanne mutum a rayuwa ta, zan kuma zaga duniya in neme su ta hanyar da zan iya don samun farin ciki na, tunda ni bani da wanda zai nema min.
Ni kadai na taso, ni kadai nake dawainiya da kaina, saboda haka zan nemi kudi ni kadai na bawa kaina jin dadin da na kasa samu a baya.
Don haka ina miki fatan Alheri a rayuwar ki ta gaba, ina kuma fatan wasiqar nan tazo miki kafin lokaci ya qure miki don ki koma ga masoyin ki na gaskiya.
Masoyin ki dake son ki ba don kudi ko don kyawun surar ki ba.
YOU ARE READING
QADDARAR MU CE
FantasyLabarin "QADDARAR MU CE" labari ne da ya shafi soyayya ta jini da qaunar juna, labari ne da ya shafi tausayi da jin qai, sannan labari ne da ya shafi kuskure da nadama. Ku biyo ni kuji yanda labarin zai kasance. #Masu ce!