Chapter 36

69 7 0
                                    

🌸QADDARAR MU CE🌸

🌹By Merow Masu (Sen.Mersoo)

                            *36*

Kano city, 2020.

Kowacce rana akan rasa rai, wasu sakamakon jinya, wasu ciwon wuni daya, wasu hatsari ne, wasu ma babu ko daya kawai qarar kwanan ne.
Mu kan yi jimami, muyi wa mamatan addu'a, wasu ma muyi kuka tamkar bazamu daina ba.
Saidai kuma cikin hikimar ubangiji bayan kwana uku zuwa bakwai sai kowa ya watse, komai ya cigaba da tafiya kamar ko yaushe.
Masu aiki su koma bakin aikin su, masu sana'a ma haka da masu zuwa makaranta.

Saidai a 6angaren Hadeeza sam abun ba haka yake ba, yanda duk suka ta so ta shafe ko ta manta cikin sati ukun nan abun ya gagara.

Tayi kuka, kukan da bata jin ya rage ko qwayar zarran abinda take ji a zuciyar ta, haka kuma rashin ragewar bai hana ta daina yin kukan ba.

Yanda duk wani zai so lallashin ta, ya fada mata cewar wannan mutuwar ma kamar kowacce ce ta kasa yarda.
Me yiwuwa saboda ta kwashe shekaru rabon ta da dandanar zafin mutuwa ne, me yiwuwa kuma saboda wannan din tazo mata a lokacin da bata ta6a tsammani ba, ko kuma tace lokacin da ta fi buqatar zaman ran.

Mutuwar Abba ta sa ta a yanayin da bazata iya furta shi ba, mutuwar Mahmoud ta bar mata wani tabo da bata jin akwai ranar gogewar shi cikin zuciyar ta, amma mutuwar Maryam?
Bata san yanda zata soma siffanta halin da take ciki ba.

Bata san meyasa Maryam ta tafi a lokacin da suka samu shaquwar da take ganin tafi ta shekarun da suka shafe a baya ba, ko kuma dai yawan shekarun da suka wuce ne yasa take ganin hakan.
Sam ita kam bata sani ba.

Kwanaki uku kacal sukayi a asibitin kafin rasuwar ta, kwanaki ukun da zata qare rayuwar ta wajen tuna kowacce daqiqa, kowanne murmushi, kowanne sauti na kuka, dariya da kuma muryar Maryam.

Ko sau daya bata ta6a kawo cewa surutan da Maryam take mata zasu kasance gaskiya ba, bata ta6a tunanin cewar dukkan wasiyyar da Maryam ke bar mata da gaske take ba, bata ta6a zaton cewar da gaske Maryam zata tafi ta barsu ta kuma bar jaririyar da ta haifa ba.

"Ni Amina! Yanzu tun dazu baki ci abincin nan ba gashi har ya sandare?"

Muryar Ummi taji a kanta wanda hakan yasa hankalin ta komawa kan Ummin da sam bata ji isowar ta parlourn ba.

Dogon numfashi Ummi taja, tare da samun guri a gefen kujerar da Hadeeza ke zaune ta zauna tare da fuskantar ta.

"Khadija, shekarun baya da Alhaji ya tafi, munyi kuka mara adadi har munyi jinya ma, amma kuma mun haqura mun cigaba da rayuwar mu.
Mahmoud ma haka, ya tafi ya barmu a lokacin da bamu ta6a tsammani ba kuma shima mun haqura mun jure.
Shin sai yaushe ne zaki daina kukan rasuwar Maryam ne? Sai yaushe zaki gane cewar Maryam tafi buqatar addu'ar ki fiye da komai a yanzu?"

Ummin tayi tambayar tare da dafa kafadar Hadeezan.

"Me yiwuwa Allah yana so ya jarraba imanin mu ne, me yiwuwa ya bar mu a raye ne don mu yiwa su Maryam addu'a zuwa lokacin da muma za'a wayi gari babu mu.
Me yiwuwa Allah ya dubi zuciya ta ne, shi yasa ya dawo dake daidai lokacin da nake buqatar ki don ki maye min gurbin maryam,don ki share min hawayena, don ki fada min cewa komai zaiyi daidai, cewa Maryam tana inda kowannen mu sai yaje".

Shiru Ummin tayi, tare da sauke wata ajiyar zuciya, hadi da sauke hannayen ta daga jikin Hadeezan.

"Saidai kuma gashi ni nake lallashin ki, nice nake qoqarin danne baqin cikin rasa 'ya'ya na biyu da mijina don na kwantar miki da hankali, amma duk da qoqarin nawa abun yaci tura, na rasa wanne irin lallashi kike so nayi miki da zai sa ki daina yawan kukan nan, ki kuma daina hora kanki da yunwa da tunani".

QADDARAR MU CEWhere stories live. Discover now