1

983 49 4
                                    

💥 *RUD'ANI...🤦🏻‍♀️*

  *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*(Home of expert and perfect writers)*

          *SLIMZY✍🏻*
   _Wattpad@slimzy33_

*SADAUKARWA:* *FATY DAN MALIKI*

                *1*
Kyakkyawar yarinya ce fara tass yar siririya tana tafe rungume da takardunta ta fito babbar jamiar dake cikin garin kaduna wato kaduna state university wadda akewa lakabi da gidan biki,
  Tsaye take gefen titi lokacin da wani tsoho mai bara ya taho ta gabanta ya tsaya,samm bataga tahowarsa ba ganinsa tayi kawai a gabanta tsaye da robar bararsa kalar shud'i manyan idanuwanta ta dago farare tasss ta dorasu akansa jikinsa dukun dukun kallon tun daga sama tayi masa har kasa yana sanye da bakin takalmin roba mai rufi tayi tsuki tayi gaba tana watsa masa wani kallo mai cike da kyama...

Takowa yayi gabanta yace "dan allah yarinya ki taimakemi kibani sadaka fisabilillahi....tun rana nake bara bansamu abinda zanciba"

Cike da masifa ta tasowa tsohon"shin kaganni da abinci koko tukunya kaga na sauke?malam ina tsaye a can ka tsaya nazonan ka biyoni me kakeso inyi maka"

Wasu samari ne suka faka motarsu gabanta "teemah dollar"suka fada a tare,tayi farrr da ido "shigo ciki mu rage muki hanya musaukeki mana"

Babu musu tasa hannu zata bude murfin motar tsohon ya ruko hannun rigarta "ki taimakeni to ki tsallakar dani titi"....juyowan da zatayi tayi masa wata hankada ya fadi tana nunasa da yatsa cike da masifa "wani irin abune malam zaka ruko hannun rigata dubeka da jikinka sai zarnin futsari kakeyi"tayi tsaki ta fada motar ta rufe sukaja a guje tsohon dake yashe a kasa yabi motar nan da kallo....idonsa hawaye ke bi wani nabin wani....take hawayen nan suka rikide zuwa jini.... daga idanuwansa yayi hasken wuta ya bayyana ya dukar da kansa ya bace....

  "Keko teemah meyasa kikaiwa wanan tsohon wulakanci haka banji dadi ba koda yake hakan bakomi bane a wajenki"

Dayan dake zaune gaban motar ya karbe "kaiko bakaga yadda ya wani ruko rigarta ba da jikinsa kamar an tsamosa daga kwata sai wari yake tunda mukai parking motarmu ta cika da d'oyi wallahi....koda yake tsoho ma teemah yasan irin kyaunki inaga mu yara?"ya juya ya kashe mata ido,ta tabe baki "can masa...yauwa....ga street din mu nan wanan"ta nuna da yatsa sukai kwana,

Tunda ta hangosa ranta yayi mugun baci take ta tsaidasu dan bataso ma suga wancen gajan a kofar gidansu cewar yana jiranta...fita tayi tai musu godiya suka ja motarsu tana takunta mai daukar hankali mai kama da hawainiya ya dira a gabanta bata gansa ba shiko ita yake kallo har yanzun tsohon nan hawayen jini ne a idonsa fuskarsa ta sauya kala bakinkirin kamar bayan tukunya haka yake bin bayanta bata ganinsa harta iso ya tsaya daga nesa yana kad'a kai,

Yellow din shadda ce jikin saurayin da slipas a kafarsa tayi butu butu saidai kyakkyawa ne ajin farko saidai kallo kayan jikinsa zai nusar maka da cewar ba ko sisi a aljinunsa shan gabanta yayi da murmushinsa mai kayatarwa "kin dawo fatima sannu da dawowa....tun dazun Nazo rabiatu tacemun kinje makaranta na tsaya jiranki"
Tsaki taja "shin wai har yaushe zakasan cewar niba kalarka bace dubeka dan Allah talakan kayau mai nasama yaci bare ya bawa na kasa?shin wai ko kunyar zuwa wajena bakayi?"

Ransa ya baci idonsa sukai jajir ya daure ya cije lebe "fatima ina sonki kiyi hakuri kinji idan ina takuraki soyayyarki ce take yawo a jinin jikina da bargona bazan iya sukuni ba face ina tare dake burina ki bani dama da soyayyarki in shayar dake madarar kauna"

Tunda ya soma magana take kallonsa,dubeshi wani haushi ya tokare mata makogwaro kalli fatar jikinsa kalar hutu tamkar mai kwana cikin AC ya tashi a AC amma bashida ko naira sai haduwar da fata irinta masu hannu da shuni,
"Kadaina mafarkin samun soyayyata niba kalarka bace wallahi ka kiyayeni nafada maka kadaina zuwa wajena wai bakaji sunana teemah dollar ba?nadace dakai faruk?..."tayi tsaki tayi gaba abinta idonsa suka cicciko da kwalla ya girgiza kai,

Yakai minti sha biyar ko zata fito ya kara tozali da ita ko zai iya barci amma sammm babu alamarta hakan yasa ya kwashi yan matan kafafuwahsa yayi gaba yana tafe kalamanta nayi masa kuna a zuciya....

Tsohon nan kuwa yana tsaye jini nabin idonsa yayi girgiza take ya sauya kamanni zuwa wani kyakkyawan saurayi hadadde...ya mika hannunsa gabansa ya ware ya tsugunna ya bugi kasa saiga dankareriyar jeep baka sai walkiya takeyi hannunsa rike da makullin mota yana kadawa wani kamshin turare mai azabar dadi ke tashi a jikinsa,

Yaro ya kira ya aikasa cikin gidan"shiga gidan nan kace ana kiran fatima"cikin wata murya mai shegen dadi yayi maganar har saida yaron ya juyo ya kallesa,sanan ya shiga gidan...

"Teemah tun dazun nake fama dake kije kiyi alawala kince ko laasar bakiyiba ga magriba amma kinki tashi ko?"

  "Ummah yanzun zanyi inadan hutawa ne nagaji sosai..."

"Assalamu alaikum wai fatima tazo inji wani mai mota...kyakkyawa a waje"cewar yaron....wani zabura teemah tayi "mai kace?"yaron ya kara maimaitawa batare da ta tambayi waye ba tace "jeka ganinan zuwa kace masa"yaron ya juya,

Mantawa tayi da wata gajiya ta mike jiki na rawa ta bude jakarta ta ciro hoda....rabiah kanwarta ta fito fuskarta jike da ruwa alamar alwala tayi "yaya faty...kinko ga yaya faruk?"
Yatsina fuska tayi "nagansa talakan banza"ta cigaba da goge gogen fuska...."haba yaya faty yaya faruk yana sonki sosai"

"Ni bana sonsa sai me?ke banson iyayi da kicifi bacemun daga gani"...ummah kuwa sakin baki tayi tana kallo kafin tace "Allah ya shirya.. amma kiyi maza kada kidade har abbanku ya dawo"
Kobin ta kan ummah batayi ba tayi waje tana taku tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki....

Tana fitowa daga gate din gidansu tayi tozali dashi jingine da jikin mota kamshin turarensa ya bugi hancinta kallo daya tayi masa gabanta ya yanke ya fadi saboda bata taba ganin kyakkyawar halitta irin wanan guy dinba....shima wani kallo yayi Mata na seconds sanan ya wayance ya sakar mata murmushi mai dauke da maanoni kala kala...sandarewa tsaye tayi tana tasbihi a ranta zuciyarta cike da farin ciki gara da Allah yasa bezo ya ganta da wancen fakirin ba....kallonsa take ko kiftawa batayi ya bude baki cikin wata irin murya yace "karaso mana dollar...."harda wani jaaaa yayi da ya kira sunan... tayi farrr lallai guy din yasanta ta taho da takunta har gabansa.....

*******
Hawaye ne ya wanke fuskarsa yana kishingide da farar jallabiya tun dawowarsa daga massallaci....ko rufe ido yayi fatima yake gani shin wace irin rayuwa ce yan matan yanzun suka daukarwa kansu mai cike da RUD'ANI da abubuwan alajabi?.....shin meyasa mata suka dau son duniya sukasawa zuciyarsu?tabbas yanason fatima kuma bazai taba fito mata a shi din waye ba zai cigaba da bin ta yagani?....shin zataso shi daga baya a yadda yake koko zata cigaba da wulakantasa?sautin muryarta ke amsa kuwwa a kunnensa..."mai nasama yaci bare ya bawa na kasa kana fakirinka?"..ya lumshe idonsa tamkar mai bacci sanyin AC ya kauraye dakin....anya zai iya bacci kuwa batare da ya koma wajenta ya ganta ba?

"Ya faruk momy tace ka fito kaci abinci"gyada mata kai kawai yayi ko amsa ya kasa bata saboda tunanin dake cunkushe a zuciyarsa......


*SLIMZY* ✍🏻

RUD'ANIWhere stories live. Discover now