💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻♀️
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)**SLIMZY*✍🏻
_wattpadd@slimzy33_*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*8*
Saddam yayi girgiza take ya Kara girma ya Zama katuwar halitta a tsaye....daga kafarsa yayi ya ajiye dik Inda ya taka sai Kasa ta lotsa saboda girmansa....wuta ke fita a bakinsa haka ya tunkaro faruk cikin wani irin Amon sauti yake fadin "saina kashe Ka....kasheka zanyi Dan bazaka taba ceton Fatima a hannuna ba"ya d'aga Kai Sama yayi ihu dajin ya amsa kuwwar sautin Saddam,
Jikin faruk babu Inda Baya rawa Yana ja da Baya gumi ya Gama jikasa ta ko INA Yadda kirjinsa ke farrr farrr kana iya hangowa Saddam na zuwa gab da faruk yayi kururuwa ta Kada kansa ya dubesa hancinsa na fidda ruwan jini da idanuwansa.....bakin faruk na karkarwa cikin dakewa yace "Kada Ka matso kusa Dani Ka cutar Dani domin bazaka iyaba,dik a Inda kaga Ka iya to tabbas Allah ne ya Baka iko...."
Fatima daga Inda take yashe tayi zaman Yan bori take jiyo maganar faruk da Alama Saddam kashe faruk zaiyi wani taimako Zata iya masa?shin a duniya suke ko a lahira oho?gashi bata gani sammm ta makance....."wayyooo Allah Ka kawo mana dauki....farukkkkkkk Kada ya kasheka Ka kyalesa kayi tafiyarka Ka barmu a wanan dajin nidashi domin nice na janyowa kaina.... wayyyoooo Allah idona aaaaaa"ta kwalla gigitacciyar Kara...faruk ya juya ya kalli Yadda take zaune tana rizgar kuka tausayinta ya kamasa gashi bata gani ya dubi kafafuwanta har jinin dake zuba ya bushe,
"Kalleta dakyau kayi Mata kallon karshe domin kasheka zanyi....na makantar da ita makanta ta harabada....saina rabata da dik wasu sassa masu amfani a jikinta"....
Ya d'aga kafa zai tako yasa hannunsa ya watsa Sama ya tada iska ta Shiga Kada ko INA a wajen wata irin guguwa ce ta taso Mai ban tsoro bishiyoyin wajen suka Shiga faduwa karaaaa ta ko inaa juyawa dajin keyi ya d'aga Kai ya kalli Saddam dake gabansa Yana masa dariyar keta....ido ya rufe ya Shiga ambaton Allah cikin saa ya d'aga muryarsa iya karfinsa ya soma karanto ayatulkursiyyu.....a daburce yake sakin wanan ya kamo wanan...
Wuta ce ta tashi a jikin Saddam yayi kururuwar wahala yasa karfinsa ya d'aga farukkk Sama Yana kokarin sakosa Kasa faruk ya karanto a'uzubikalimatillahi tamma wamin kulli shaidanin hamma wamin kulli ainin Lamma....aiko wata iska tayi Sama dasu tare ihu Saddam yayi Yana kokarin Kai ma faruk Shaka...
Fatima datai zaman Yan bori tana waige waige bata iya ganin Komi cikin rudu da fargaba take fadin "Dan Allah Kada Ka kasheshi Ka sake Shi ya tafi gida....ni Ka kasheni nice na jawowa kaina.....wayyoo faruk ina sonka......"tace cikin kururuwar kuka....
A galabaice Saddam ya Fadi Kasa ji kake timmmmmmmmm....Saida dukkansu suka toshe kunnuwansu faruk ya dubesa cike da tsoro hayaki yaga ya tashi cikin kiftawar ido ya bace battrrr,
Waige waige faruk keyi Kada yazo yayi masa illa....saidai Amon muryarsa da sukaji Yana magana a galabaice...."faruk Ka tsokalowa kanku masifa....ni zaka Sawa wuta?saina aiko muku da masifa Kala Kala....ni YUHANA.....'yace cikin daga murya,
A sanyaye faruk ya sauke ajiyar zuciya...cikin Ransa yace akwai nasara a fili kuma ya furta "ta Allah ba taka ba....."...hayaki bakin Kirin ya hanga yayi cannnn Sama "natafi masarautarku saina tarwatsa ahalinku"
Jikin faruk yayi sanyi ya taka a hankali ya karasa gaban Fatima wadda take zaune ta mimmike kafa hawaye wani nabin wani fuskarta ta bushe da hawaye lebenta sunyi jajir fuskarta ta fada,
Kamshin turarensa ya bugi hancinta ta Shiga lalube da hannunta tanaso taji Inda yake....kamar Wanda take gani ya girgiza Mata Kai kibar" kawo hannu gareni keba muharramata bace Fatima"....hawaye nabin fuskarta idanuwanta farare tassss kamar tana gani,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...