💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻♀️
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)**SLIMZY*✍🏻
_wattpadd@slimzy33_*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*16*
Kallon kallo faruk keyi shida amininsa cike da fargaba da tashin hankali faruk jikinsa na rawa yake Nuna masa "kaga abinda nake gani?kodai Baka gani ba?"
"Nagani faruk Ka kwantar da hankalinka Kada kaji tsoro dik sihiri ne da siddabaru irin na mugayen aljanu babu abinda zai faru kazo mu Shiga kawai"
Girgiza Kai faruk yayi "banajin zamu iya samun nasara a wanan lokacin domin babu abinda zai haifar sai RUD'ANI GA mutanen gidan mu kuma karahenta bazamuyi nasara ba"....ruko hannun faruk yayi cike da kwarin gwiwa yace "idan har muka ki Shiga yanzun to tabbas haka zamu dawwama cikin wanan yanayin kuma an rinka Shiga RUD'ANI Kenan gara kazo muje kayi addua Ka tofa a hannunka zanyi mu shafe jikinmu mu tunkari gidan"
Cikin rashin kuzari faruk ya amsa nan suka shafe minti goma suna adduoi hade da azhkar dik abinda yazo bakin faruk Shi kawai yake karantowa...haka suka tunkari kofar gidan cike da kwarin gwiwa
A harabar gidan dogarawa ne cike kasantuwar yau jumaa kowa Yana zuwa gaisuwar sarki...faruk ya sako kafarsa cike da faduwar gaba....gaba Daya hadimai da sarkin fada suka zube....wani nishadi ne ya tsunci kansa ciki murmushin nan nasa da yake Kara masa kyau da kwarjini na sarauta ya sakar musu...hade da Mika musu hannu su gaisa kowa yayi shock domin sun kwana biyu basuga haka daga yareemah ba tun bayan da yayi aure ya sauya yayinda wasu suka fada waswasi yanzun ya shige cikin gida fuskarsa babu annuri babu rahma baiko kallesu ba suna gaishesa Amma ya dawo ta kofar gida Yana faraa....koda yake kofofine kusan biyar a cikin gidan....ganin yadda sukayi faruk yasha jinin jikinsa Amma ya dake,
Sa kai sukayi cikin gidan direct hanyar fada sukabi....rumaisa ce yaci Karo da ita sanye da alkyabba Mai ruwan Zuma bisa Alama gaisuwar jumaa zatajewa sarki wani kallo yayi Mata Wanda baisan yayi Mata Shi ba,take yaji tsanarta da kyamarta sun dasu a cikin zuciyarsa....ya kauda kansa,
Ita kuwa cike take da mamakin ganinsa a nan bayan ta Barosa a sashenta ya Gama tattaba Mata jiki Yana sunsunarta to kodai ya fasa wankan ne ya bullo ya wata kofar gashi sunyi kicibis....tana tsaye tana tunani suka wuce koda ta juya sunyi gaba...hadimanta suna tsaye a bayanta suna jiran ta tafi su take Mata Baya......
Momyn faruk ce zaune a gefen dama jingine da kilisa yayinda mama Fulani dake gefen hagu Tasha ado sai walkiya takeyi ko wacce a cikinsu Tasha alkyabba gefenta masu hidimarta ne...kamshi ne ke tashi a cikin fadar Wanda dama kullum fada cikin kamshi take na turaruka Kala Kala....gaban faruk na tsananin faduwa hannunsa na rike da na amininsa suka Shiga fadar wacce Yana Shiga Maroka da masu busar algaita suka soma yiwa faruk kirari.....
Tsaye yayi cakkk a tsakiyar fada yayinda amininsa ya gurfana Akan gwiwoyinsa hawayene suka wanke fuskar faruk lokacin da yake kallon mahaifiyarsa ta rame sosai saidai tayi haske fuskarta babu walwala ko kallonsa batayi ba....takawa yayi ya karasa gabanta ya durkusa cikin shadshekar kuka Wanda yasa fada tayi tsit yace "ki kalleni ya mahaifiyata....faruk dinki ne na ainihi a gabanki ba aljani ba...wancen faruk din Daya muzantaki ya wulakantaki ba faruk dinki bane face shedanin aljani"Yana kokarin ruko hannunsa ta ture hannunsa ya Mike ya karasa ya Fadi gaban mahaifinsa ya ruko kafarsa "abbah nine faruk danka nadawo gareka magajinka danka Daya tilo Umar faruk wancen faruk din da yayi rayuwa daku Bani bane aljanine"
Kallon kallo aka shigayi cikin fada wani kallo Mai martaba ya watsawa faruk kafin yayi gyaran murya yace"Kai faruk karka shigo mun fada da wasan kwaikwayo mana?ko Ka Fara shaye shaye ne?kace bakai bane faruk din da muke rayuwa dashi to waye?Ka Gama iskancin da cika da batsewa saboda an aura maka rumaisa yanzun shine kazo da sabon rainin hankali?dama jiranka nakeyi kadawo hayyacinka"
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...