💥 *RUD'ANI....*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers*)*SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33*SADAUKARWA:* *FATY DANMALIKI*
*24*
Tsaye yayi a bakin kofar Shiga fada gabansa na tsananin faduwa tare da fargabar abinda zai tarar addua yayi a cikin Ransa yasa Kai ya Shiga ciki da sallama dauke a bakinsa Yana karasawa ya durkusa a gaban mahaifinsa cike da fargaba dakewa yayi ya sunkuyar da Kai babu Wanda yayi magana tsawon mintuna kafin Mai martaba ya nisa yace"Umar Ka canja daga Umar faruk Dana danasani zuwa wani na daban a iya sanina faruk Dina Yana Jin magana shin meyake yawo akanka?idan da sharrin aljanine yanzun fa? galadima yayimun bayani game da Komi hakan yasa na sassauta daga fushin da nakeyi maka yanzun kuma naji wai GA Inda kake Ka komawa wanan yarinyar wadda taso tarwatsa maka rayuwa"
Tabbas faruk yaji mamakin Yadda Mai martaba keyi masa magana domin yayi tunanin zafin zaifi haka wani farin ciki ne ya lullubesa tabbas dole yayiwa galadima gagarumar kyauta..."wanan ba matarka bace?inace ciki ne a jikinta kuma naka ne?Ashe dalilin dayasa bakada lokacinta Kenan?to Ka Shiga hankalinka kasani idan zakayi aure ma BA yanzun Zan yarje maka ba"
"Allah ya taimakeka kayafemun nayi laifi Amma ina neman agajin sarki Mai adalci ya mahaifina Kai adaline ga iyalanka da alummarka Dan Allah kabarni in duba lamarin yarinyar nan koda bazan aureta ba"
Shiru Mai martaba yayi batare da yace Komi ba wani kishi ne ya turnuke rumaisa wato ma neman hanyar Kula waccen ragowar aljanin yakeyi Kenan?tayaya ma akayi Mai martaba ya sauko daga fushin da yakeyi dashi?.....mikewa tayi take cikin kissa ta dafe kanta tayi Kasa Zata Fadi da sauri mama Fulani ta tallabota tana fadin "ninasan zaaa Rina mace Mai ciki da laulayi irin haka a rinka zancen auro wata a gabanta AI dole ta Shiga wani Hali da sauri faruk ya kalleta ta watsa masa wani kallo Wanda a idon momynsa tayi masa kallon ita kanta Saida gabanta ya Fadi irin tsantsar tsanar data hango ta faruk a kwayar idon Fulani....bayi ta Kira guda biyu suka tayata ruko rumaisa ta kaita bangarenta suna Shiga rumaisa ta gyagije kawai ta saki kuka "nashiga uku mama Fulani faruk ya daidaita da Mai martaba da alamar badadewa zai yarje masa auro wata nikam ya zanyi"
Murmushin mugunta Fulani tayi "taya zaki Bari hakan ta kasance?kina bacci Koko kin mutu shin ke meye naki nadamuwa bayan Shi kansa faruk din kashesa zakiyi?"
Da sauri ta kalli Fulani,Fulani ta gyada Mata Kai alamar ehh mana "da zarar kikasamu dama aikasa lahira zamuyi so nakeyi cikin nan naki yayi kwari idan kuma bakiyimun haka ba to ki tabbatar asirinki ya Gama tonuwa na cewar ba cikin faruk bane a jikinki cikin Anuwar ne kanin faruk sanan inada video dinki lokacinda kuke holewa keda anuwar,Kar kuma kiyi tunanin har anuwar Zata shafa kece Zata shafa Dan Zan bayyabarda cewar kwaya kikasa masa yasha ya aikata alfasha dake"ta karasa maganar tana kallon rumaisa Ido cikin Ido,gumi ne ya jika rumaisa tabbas wanan matar tasamu babban makami akanta Amma bazata Nuna Mata nata makircin yafi nata ba sai nan gaba murmushi kawai Tayi ta nemi waje ya zauna.
Bata sake cewa Komi ba sai kishingida da tayi tana sauke numfashi cike da tsananin kishi ta Shiga saka abubuwa a cikin ranta tana warwarewa.....
Mama Fulani kuwa mamakin Yadda Mai martaba ya sauko takeyi tayaya zaiyi saurin sakewa faruk haka?bazai yuwuba Yadda bata haihu da Mai martaba ba dolene Dan Daya Haifa ta tarwatsa masa sukuni....
*******
Abinda ya faru daga farko har karshe tun barinta gida da sunan aure tabawa ummah da rabiah labari har izuwa dawowarsu da rayuwarta a gidansu anuwar dashi kansa anuwar din ta kwashe ta fadawa ummah,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...