32

56 8 1
                                    

💥 *RUD'ANI...*🤦🏻‍♀️

     *FREE BOOK*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)

          *SLIMZY*
  Wattpad@slimzy33

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

*Mai bukatar a tallata masa hajarsa 07042277401*

Ga mai bukatar littafaina akwai complete documents

*Zainul Abideen 300*
*Izza Ta 300*
*Duhu sarkakiya 300*
*Ramin mugunta 300*
*Kukan zuci 300*
*K'ugiya 500*

*tuntubeni 07042277401*

                       *32*

Bugun zuciyar fatima ne ya tsananta cike take da tsananin rud'ani da tashin hankali kallonsu takeyi d'aya bayan daya hawaye ne ke Ambaliya a fuskar fatima waigowa Anwar yayi idonsa ya sauka akanta wadda ta jingina da bango idanuwanta rufe gammm hawayene kawai ke gudu kamar fanfo,

huci yayi ya furzar da iska mai zafin gaske cikin kidimewa ya karasa ya d'ora hannunsa akan kafad'ar fatima jiki a sanyaye tausayinta da kaunarta na ratsa sassan jikinta a sanyaye ya kira sunanta wanda taji kanar ya zuba mata rushin wuta,

"fatima.....sannu kinji akwai abinda yakeyi miki ciwo ne?ki fad'amun kinji?ki bude baki kimun magana inji dadi"bude idonta tayi ta jefesa da wani kallo mai cike da tuhuma da tsana ja da baya yayi gabansa na faduwa kallon da fatima tayi masa kallo ne na masu hankali ba hauka ba yadda ta kafesa da ido yaji ko motsi bazai itaba,

tsaki gimbiya rumaisa tayi "aikin banza aikin wofi iska na wahal da mai kayan kara wallahi dubi yadda ka susuce ka dimauce akan wanan d'ibar iskar",

zabura yayi zai kai mata mari sai kuma ya sauke hannunsa yana nunata da yatsa jikinsa na tsananin rawa yake magana "dik abinda zamuyi nidake muyi amma karki kuskura kice zako ketare kan iyaka domin fatima ba saarki bace fatima ta wuce gaban ko zageta ki kirata da d'ibar iska matukar ina numfashi bazan taba bari wani ya wulakantamun itaba matar da zan aura"....

"Hmmm ita kanta datasan waye kai da ko kallonka bazatayiba tsohon mazinaci?tsohon Mashayi?"

kara fatima ta kwalla tasa hannu ya toshe kunnuwanta tana kururuea rumaisa na gama magana tayi murmushi ta barsa nan tsaye kamar an dasa shi har ta kai kofa ta juyo "zab ajiye maka ita a inda zaka sa a dauketa dan wanan yarinyar tana barazana da mutuncinka da aurena ni kaina kayi gaggawar aikowa a sace maka yarka ka kaita inda inta girma zaka daukota kabawa wanan bugun iskarx"ta bace hannu yasa ya kaiwa bango naushi saida hannunsa ya fashe sanan ya juyaga fatima da take juyi a kasan carpet mai laushin gaske rike da kanta wanda ke sarawa kamar zai rabe gida biyu,

cikin sauri galadima ya iso tare da wata kuyanga wadda tayi kiransa ta sheda masa taji ihu da karar fatima,

"Subha meye yasamu zahrau?Anwar naga kana cikin d'akin"ya kalli hannun Anwar dake fitar da jini yace "subhanallahi meye yasameka haka?Aljanin ya kawo hari ko?"

girgiza kai Anwar yayi Yana kallon fatima jikinsa a sanyaye wani bangare na zucuyarsa cike yake da tsananin tsoro da furgici meyasa fatima ta yanka ihu?meyasa ta runtse idonta batason budewa tana hawaye?kardai fatima taji maganganun da suka tattauna da rumaisa......kuyanga hajara ce ta taimaka wajen d'ago fatima galadima ya Shiga kiran sunanta kasa bude idonta tayi zuciyarta na tafarfasa ko a mafarki bata taba tunanin Anwar ba mutumin kirki bane,Anwar mazinaci ne Anwar Mashayi ne kankat Anwar yayi zina da matar dan uwansa?rushewa tayi da kuka bakinta na rawa kamar ana watsa mata ruwan sanyi,

sallama akai muryar afrah ce ta shigo ta kalli fatima ta yatsina fuska sanan ta dubi Anwar da jini ke zuba a hannunsa ta dafe kirjinta cikin furgici tace "yaya meyasameka?meyasamu hannunka?"kwallar da yake boyewa ce ta zuraro a fuskarsa kafafuwansa sun kasa daukarsa dakyar ya kalli hannunsa ya kalli afrah data zuba masa ido cike da tausayawa "yaya momy da daddy suna jiranka kataho mutafi"ta yaya zai iya tafiya yabar fatima a nan?bayan yana zargin Fatima na cikin hankalinta idan ba haka ba menene yasa fatima fad'aea cikin wanan mummunan halin data Shiga? wayarsa ta shiga ruri ya duba daddy ne ya kalli afrah fakyar ya hadiyi wani miyau mai kauri da d'acin gaske yace "muje"tayi gaba ya juya takun sahun takalminsa fatima taji a hankali ta bude jajayen idanuwanta bakinta ya bushe karau tausayin faruk ne ya soma shigarta Allah sarki faruk mutumin kirki,

RUD'ANIWhere stories live. Discover now