20

179 21 2
                                    

💥 *RUD'ANI...*🤦🏻‍♀️

*FREE BOOK*

  *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)*

                   *SLIMZY*✍🏻
       _wattpadd@slimzy33_

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

*Wanan shafin naki ne* *MRS JEBEE  from SLIMZY GROUP NOVEL*..... *Kuyi hakuri da rashin update Akan Kari Insha Allah zanyi kokari in rinkayi dik bayan kwana biyu*🥰❤️

                            *20*

yanda Fatima taga Rana haka taga dare koda safiya tayi zazzabi Mai zafi ya rufeta GA wani ruwa dayake bulbulowa ta gabanta tun ranan da afee ta bata wani ruwa Mai wani irin test Wanda ita kanta bata Yadda da wanan ruwan ba to wani irin ruwa ne haka yake fita a gabanta....rawar sanyi sosai Fatima keyi dik jikinta yayi zafi numfashi take saukewa Sama Sama....har ya wuce ta gefen window dinta yajiyo sautin numfashinta na sauka Sama Sama.....da sauri ya dawo babu ko sallama ya fada dakin Yadda yaga tana rawar sanyi ya tabbatar da ba lafiya ta tashi ba gashi hawaye ya bushe a fuskarta alamar taci kuka....

"Fatima.....meyake damunki?meke faruwa haka bakida lafiya ne?"ya tambayeta cikin tsananin rudewa,

Dakyar maganarta ke fitowa tace "zazza....bi kedamuna sosai inaso Inga ummah na dikda banida idon ganinta ko zaka taimakamun?"tace cikin tsananin ciwo,tausayinta ya kamashi haka ya Mike ya fice da sauri ta kofar kitchen ya Shiga ya hadu da afnan da meeniosky da afrah suna hada breakfast.

"Wani shin ina makauniyar gidan nan take ta fito tayi aikinta mana ko batasan safiya tayi ba?ke afrah jeki Kira waccen bakardagar"momy tace tana karasa shigowa kitchen,

Anuwar dake tsaye ya shigo babu wani tunani yace"afee jeki shirya kije wajen Fatima ki shirya ta tagyara jikinta mu Shiga garin Kaduna taga likita batada lafiya"

Da sauri meeniosky ta kallesa dukkansu ido suka zuba masa Banda momy wadda ta zabga salati tana tafa hannuwa "yanzun anuwar kafi karfin kazo Ka gaisheni sai Ka Fara zuwa wajen waccen makauniyar tukunna sanan zakazo wajena?wai tukunna ma kodai yarinyar nan aljanah ce ko matsafiya ce data tsaface kurwarka?"

Bakin ciki ne ya tokare ma meeniosky makoshi wadda ta Kasa jure tsananin kishi da tsanar Fatima wato anuwar ya tashi Yana wajen Fatima wayasani ma ko wajenta ya kwana?ya kamata ta datse igiyar alakar data kullu tsakaninsu kafin Fatima tayi Mata Karan tsaye a lamarin aurensu,cike da kwarin gwiwa meeniosky tace "momy AI ba aljanah bace ba kuma matsafiya bace saidai matar aljani ce"

Dukkansu suka juyo da dubansu GA meeniosky wadda ke jingine a jikin bangon kitchen din cike da kissa hawaye ya gangaro a idonta "momy Zamana bazai yuwu a gidan nan ba tun jiya Dana ganta nasan cewa inhar tana gidan nan yaya anuwar bazai Soni ba sanan Fatima ba makauniyar asali bace tasamu makanta ne sanadiyyar kwadayi don haka yanzun zanbar gidan nan koni ko ita kuma rayuwarku tana cikin hadari"ta fashe da kuka ta fice daga cikin kitchen din tana kuka afrah da sauri tayi jifa da matsami tabi bayanta momy cikin kidimewa ta kalli anuwar sanan ta take musu Baya.

Dafe Kai Anuwar yayi cikin tashin hankali,nan da nan idanuwansa sukai jajir jijiyoyin jikinsa duk suka tashi wata irin zufa ce ta mamayesa innahlillahi wa innahilaihi rajiun kawai yake ambatawa tabbas wanan yarinyar ta Rusa masa shiri tunda tayi furucun nan Akan Fatima yasan ta jefashi cikin masifa Amma Zata d'and'ana kud'arta a wajensa.

Juyawa yayi Bai Shiga cikin gidan ba kawai ya nufi sashen Fatima Bai tsaya jiran afee ba da kansa ya kimkimeta yasata a kafadarsa ya fice da ita...

Momy kuwa har tanayin tuntube wajen fitowa harabar gidan Yana kokarin bude mota ta daka masa tsawar da Saida ya razana "dakata Anuwar Ina zakaje da ita?"

RUD'ANIWhere stories live. Discover now