26

157 23 4
                                    

💥 *RUD'ANI....*🤦🏻‍♀️

        *FREE BOOK*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers*)

                  *SLIMZY*✍🏻
          Wattpad@slimzy33

*SADAUKARWA:* *FATY DANMALIKI*

*KAMAR YADDA NAYI ALKAWARI ZAN CIGABA DA POSTING 3RD DECEMBER INSHA ALLAH GASHI NAFARA BAYAN DAUKEWAR HANYAR SADARWA DA MUKAYI NA WASU WATANNI YANZUN ZAMU D'ORA*

                      *26*

Cikin sauri rabiah da ummah suka nufi dakin Dan ganin meye ke faruwa GA mamakinsu Fatima suka gani kwance babu alamar numfashi ihu rabiah tasaka ta dago Fatima tana Kiran sunanta "yaya faty yaya kitashi Dan Allah meke damunki"tasaki kuka tana kallon ummah wadda itama a razane take tana kallon yar Tata saidai ta danne zuciyarta gudun Kada rabiah ta fahimci itama a tsoracen take dakin takebi da kallo bataga alamar wani Abu Wanda ya razana Fatima ba ta Kara duban Fatima ta tallabota ta Shiga tofa Mata ayatul kursiyyu da amanar rasulu ganin ummah na tofa addua itama rabiah ta Shiga tofa Mata cikin mintuna da Basu wuce goma ba Fatima ta sauke ajiyar zuciya ta zabura ta zauna tana waige waige tana kallon ummah juyawa tayi ta kalli madubun dakin data kalla bataga komiba cikin tsoro ta ruko ummah tana kalle kalla "ke Fatima ki natsu menene ya razanaki haka kika Fadi a sume me kika gani fadamun"

Har yanxun a tsorace take ta Kara juyawa sanan ta dubi ummah ta fashe da kuka "ummah Saddam nagani cikin kamannin anuwar na tabbatar ba anuwar bane domin anuwar Bai shigo gidan nan ba cikin bakaken Kaya da mummunar kama na gansa"tace cike da furgici "nashiga uku ummah ya dawo gareni nasan bazai kyaleniba Saiya kassara rayuwata kamar Yadda ya kudura"

Ummah ta nisa cike da damuwa tace "Allah bazai bashi saa ba domin zamu Mike da addua kuma dole zamuje wajen Mai magani yanxun ki tashi kiyi alwala kiyi sallah idan kin idar zamu tafi wajen Malam abbah Inda mahaifinki yaje kafin ya mutu"

   "Toh ummah"a sanyaye ta Mike tana waige waige ta shige toilet cikin sauri sauri Tayo alwala ta fito saboda a tsorace take.....

Kamar Yadda ummah ta fada haka suka dunguma suka nufi gidan Malam abbah Wanda yayi adduoi sosai kafin daga bisani yasaka wani hayaki ya nemi yuhana Wanda wanan zuwan a mummunar kama yazo masa kamanninsa sun tabbatar masa da fansa yazo dauka.....ya dade Yana magana dashi kafin ya fito Inda su ummah ke zaune dukkansu ko wanne kirjinsa na dukan uku uku,

Gyaran murya yayi sanan ya soma magana "tabbas shine yazo a kamannin saurayinki Wanda shine yayi silar warkewarki daga cutar Daya saka Miki,wanan Karon da daukar fansa yazo saidai fa kuyi hakuri aikin yafi karfina indai anaso aci karfinsa ta Inda aka hau ta nan zaa sauka"

Daga ummah har su Fatima ko wanne ya shiga RUD'ANI ummah ce tayi ta Maza tace"Malam kayi mana bayanin ta Inda aka hau ta nan Ake sauka"

"Ehh toh....kauyen da sukaje tasamu waraka nan zasu koma domin Shi kadai ne zaiyi maganinsa Wanda ya kaita Shi zai Kara kaita a cigaba da magani domin alamu sun Nuna dauketa yakeso yayi Wanda inhar yayi nasara to tabbas Saiya rabata da ranta"

"Innahlillahi wa innahilaihi rajiun...."Shi kawai ummah ke ambata yayinda Fatima ta fashe da kuka suka rungume juna itada kanwarta suna kuka maiban tausayi,

"Sanan Abu nagaba shine ayi gaggawar yiwa Fatima aure Dan idan ya karayin nasarar aurenta a Karo na biyu ya dauketa to ya tafi da ita Kenan harabada idan ya Barta da ranta Kenan"

  "Yanzun menene abunyi Malam"ummah tace cike da damuwa "ehh mafita ce nafada muku bakuyi latti ba akwai sauran lokaci inaso suyi gaggawan zuwa ga Wanda yayi Mata magani"

RUD'ANIWhere stories live. Discover now