39

62 7 1
                                    

💥 *RUD'ANI...*🤦🏻‍♀️

     *FREE BOOK*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)

          *SLIMZY*
  Wattpad@slimzy33

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

*Mai bukatar a tallata masa hajarsa 07042277401*

                       *39*

dak'yar rumaisa ta hadiyi wani miyau mai kauri idanuwanta jajir take bin fatima dashi fatima kuwa kallonta takeyi tana shu'umin murmushi,

"lokaci ne yayi da na juyo gareku lokaci yayi da ni zanyi sanadiyyar barinki gidan nan idan ke baki sanadin bari na ba dan Haka kafin safiya ki mika kanki da kanki kafin ki wulak'anta cikin dubban jamaa sanan kindaisan sarki zaisa a jefeki sakamakon zina da kikai da Aurenki"
  faruk ne ya shigo sashen sanye da kayan bacci rike da takarda a hannunsa idanuwansa jajir bayan ya duba takardar yaga abinda ke ciki bashi likita ya fad'a masa ba,saidai mamaki ne ya kashesa ganin fatima tare da rumaisa,

murmushi fatima tayi hade da sunkuyar da kanta k'asa "kayi hakuri ka fito baka sameniba ko?na jiyo kukan mai sunan momy shine nazo naga ko lafiya ashe mamanta ce ta shiga wanka kuma na tsaya nayi mata godiya akan karamcin da sukayimun d'azu"ta karasa maganar kanta a kasa tana kokarin tura takardar jijkin wandon baccinta cikin saa kuwa faruk bai ganiba,
wani kallo yake jifan rumaisa dashi wanda hantar cikinta tuni ta kad'a tabi fatima da kallo yadda take tafiya tana d'ingisa kafa cikin ransa yace "Allah sarki da kinsan tuggun da wanan ke had'a miki ko kallonta da shegiyar yarta bazakiyi ba fatima mai kyakkyawar zuciya,yayi murmushin gefen fuska,

nuna rumaisa yakeyi da yatsansa manuni jikinsa har rawa yakeyi yana nuna mata takardar hannunsa "nasan ko menene wanan kece kika shiryasa na tabbatar ba wanan takardar likita ya kawo ba ina takardar da aka kawomin kika canja?"cikin tsawa yake maganar,

gaba daya rumaisa ta fita hayyacinta ya daka mata tsawa "nace ina takardar?"jikinta ya soma rawa gaba daya a rude take tabbas faruk besan takardar gwajin jinin nan tana tare da fatima ba dan haka dik yadda zatayi ta kubuta zatayi"

turo baki tayi cike da rashin kunya ta galla masa harara "kai kasan inda takardar take dan haka ni bansaniba dik abinda kake shiryawa kaga na wulakanta sai Allah ya so"ya wanka mata mari ya cafko gashin kanta ta saki yar kara,
yasa hannu ya toshe mata baki "zaki fadamun gaskiya ko yaya?"cikin azaba tace "wash sakarmun kaina"ganin yadda takeyi yasa ya hankadata ko ganin gabansa bayayi yace "nabaki daga nam zuwa safiya ki fito da takardar nan idan ba haka ba"ya wuce hanyar fita tace"idan ba haka ba sai me?"wani kallo ya mata ya fice,

ta durkushe a kasa ta fashe da kuka ta kalli agogo dare yayi sanan tasan mama fulani itace da mai martaba dik runtsi tasan tana sashensa ta yunkura ta mike kamar mahaukaciya ta shiga safa da marwa cikin dakin tana kaiwa tana komowa mafita kawai take nema ji takeyi tamkar kada gari ya waye....

*******
daga kai fatima tayk daga kwanciyar da tayi wanda idonta biyu taga faruk zaune ya rafka tagumi hawaye nabin fuskarsa tausayinsa ne ya kamata wata zuciyar na cewa ta mika masa takardar wata na hanata tasani tabbas tabashi takardar nan zai tuhumeta akan sanin abubuwa game dashi ba yanzun takeso yasan tana masa yak'i ba tabbas zata gama da rumaisa sanan ta koma ga babbar giwar wanda tasan kayar da ita ba abu bane Mai sauki,

likita ne ya kira faruk yayi saurin dauka "likita yanzun ya zaayi ya zaayi ja fitar dani a wanan tsaka mai wuyar ina cikin matsala"daga kwancen sa fatima take cikim zucuyarta tace baka cikin matsala kanadani ina gab da rabaka da wanan karfen kafar,

daga cikin wayar likita yace "solution daya ne yarima shine karka bawa sarki wanan takardar da aka canja ka nemi takardar da bata komi bace ka bada yadda ko nazo da niyyar karantawa zaace baa ganta ba sai an sake zaa bijiro da cewar saceta akai amma inhar kabashi wanan to kashinka fa ya bushe"

RUD'ANIWhere stories live. Discover now