💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻♀️
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)**SLIMZY*✍🏻
_wattpadd@slimzy33_*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*12*
Dakyar abbahn Fatima yasamu motar ta tashi saidai Yana tukin ne motar gefe Daya tayi masa nauyi tamkar Wanda aka dorawa Kaya a gefe minti minti yakan share zufar dake keto masa ta ko ina gaban rigarsa ya jike sharkaffff yuhana nagefensa take ya rikid'a ya koma sadam dinsa da abban Fatima yasanshi dashi yana kallon abban Fatima Yana murmushi,abbah kuwa ta gefen idonsa yaga mutum zaune hakan yasa hannuwansa suka Fara rawa da karkarwa....cikin sanyin murya sadam yace "meyasa hannunka yake rawa da karkarwa?nazo muyi Karon namu dakai Dan na tabbatar kaike kokarin ginamun Katanga tsakanina da matata Fatima......"abbah bece komiba ya bude Baki da niyyar addua sadam ya hura masa iska take harshe ya cika bakinsa motarsa ta soma gargada a tsakiyar titi....juyowar da abbah zaiyi sadam ya gani zahiri Amma kwayar idonsa sun koma na jini tamkar gudan jini abba ya runtse idonsa cike da tsoro da furgici take ya saki Kan motar a guje motar ta rika Karo da motoci ta tunkari wata katuwar trailer.....
Jikin Fatima ya soma rawa kamar wacce Ake watsawa ruwan sanyi cike da tsananin faduwar gaba,faruk idonsa na kanta Yana mamakin yanayin nata a wanan lokacin ya d'aga ido yaga hasken Rana babu sanyi sai tsananin zafin Rana Amma take rawa d'ari....lokaci d'aya yaga hawaye na gangarowa a idonta,cikin sanyin jiki yace "bintu yadai?meke faruwa?bakida lafiya ne?ko kinajin yunwa?"lokaci Daya ya jero Mata wadanan tambayoyin hade da kafeta da idanuwa.....
Bata ganinsa Amma fa idonta farare Tass kamar madara wadanda suke fidda ruwa a wanan lokacin....dakyar ta saita kanta cikin rawar murya tace"faruk....inajin wani Abu a jikina inaso Inga abbah na in rokesa gafara rashin kunyar da nayi masa Akan auren faruk.....domin bansan da wani ido Zan kallesa ba idan har muka hadu a filin kiyama idan besameni da Rai ba...inaji a jikina tamkar Allah ya Raba ganawa tsakanina da mahaifina faruk....."ta rushe da kuka Kai ban tausayi,
Kallonta faruk yakeyi take kwalla ta cicciko a idonsa sosai ya Danne hakoransa Dan tabbas shima kukan yakeso yayi ko zaisamu sassaucin abinda yakeji a zuciyarsa a halin yanzun gaba Daya ya Gama rauni....kalaman Fatima sun ratsa masa zuciya sosai....cikin taushin murya da lallashi yakai hannunsa Yana share Mata hawaye "wanan kukan da kikeyi a yanzun haka ba karamin tadamun da hankali yayi ba Fatima....kisani rayuwa da mutuwa Duka na Allah ne don Allah Kada kiyi wani tunani inaji a jikina zamu fita a wajen nan da rayukanmu kuma zamu hadu da iyayenmu"
"Ba lallai ni in hadu da nawa iyayen ba faruk....wani Abu nakeji a jikina tamkar ina gab da Rasa Daya daga cikin jigogin rayuwata"...ruko hannunta yayi yadan matse hawaye nabin idonsa batare da yace komiba ya matsa gefenta ya Dora kanta a kafadarsa ya cigaba da hawaye,
"Faruk.....Dan Allah kayimun wani alkawari mana a rayuwata?"...jinjina Mata Kai yayi don bayaso yayi magana ta fahimci kuka yakeyi taji alamar Kada kansa hakan yasa ta cigaba da magana...."ko bazaka aureni ba faruk inaso Ka kasance tare Dani har karshen rayuwata......don nasan babu sauran d'igon soyayyata a zuciyarka face tausayina...kuma Kada kataba rabuwa Dani faruk koda kayi aure,...koda yake kanada aure yanzun haka"tace tana murmushi tana daga manyan idonta kamar tana ganinsa....hawaye ne ya Digo a hannunta masu zafi ta dago hannun tana fadin" farukkkk....faruk kuka kakeyi?Dan Allah Kada kace bazakayi mun wannan alkawarin ba"
Cikin wata irin murya yace "nayi miki"ya matse hannuwansa da nata waje Daya Yana sauke numfashi.....
*********
Mama Fulani na zaune ta jingina da kilisa bayan ta Gama breakfast anuwar ya shigo sashen nata,saidai kallo Daya tayi masa taga alamar tamkar Yana cikin wata damuwa,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...