10

196 16 0
                                    

💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻‍♀️

  *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)*

                   *SLIMZY*✍🏻
       _wattpadd@slimzy33_

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

                            *10*

Ajiyar zuciya Malam abbah ya sauke ya dubesu Duka ya maida dubansa Ga rabiah wadda gumi ya Gama jikata fuskarta tayi jajir saboda kuka....ya dubi ummah wadda Shi take kallo ko wanne a cikinsu gabansa faduwa yakeyi Banda abbah Wanda tuni zuciyarsa ta kekashe,

Gyaran murya Malam abbah yayi "tabbas Fatima na cikin hatsari ko Ince itada saurayinta faruk Dan suna tare"da sauri abbah ya dago Yana kallon Malam rabiah zatayi magana Malam abbah ya katse Mata hanzari "a halin yanzun babu abinda suke bukata sai addua domin suna cikin matsanancin yanayi saboda aljanin dake wahalar dasu bakin Arne ne Baya sallah kuma bashida Imani ko kadan.... Yana can tare dasu a wata duniya ta daban"

Cike da damuwa ummah tace "Malam yanzun babu wani Abu da zaa iyayi ya dawo dasu?"

"Idan ya dawo dasu to Fatima Zata dawo da matsanancin ciwo Dan yanzun haka ta makance kuma a binciken da ya Nuna mana ya sadu da ita ya watsa Mata muguwar cuta ta gabanta Wanda maganceta babban bala'i ne da tashin hankali samun maganinta na wajen wanan aljanin Daya sadu da ita dole shine zai warkar da ita"

Kuka ummah ta rushe dashi cike da tashin hankali dukkansu kuka sukeyi daga rabiah har ummah Banda abbah Wanda ya jajirce yayi namijin kokari Shi kansa cijewa kawai yakeyi babu abinda bakinsa ke ambata sai innahlillahi wa innahilaihi rajiun....dik wata kafa ta jikin abbah Wanda gashi ke tsurowa babu Inda Baya gumi.....

  "Malam....Ka taimakemu da rokon Allah ko Allah zaisa a dace"

Girgiza Kai Malam abbah yayi "tabbas babu abinda ya gagari Allah zamuyi rokon Allah idan munsamu nasara shikenan.....don abun da kamar wuya"

Ajiyar zuciya abbah ya sauke yasa hannu cikin aljihunsa ya Ciro kudi ya ajiye a gaban Malam abbah "Ga wanan sadaka Malam abbah nagode sosai Allah ya saka da alheri"

  "Ameeen "ya amsa Yana girgiza Kai...abban ya dubi ummah "Ku tashi mutafi ko"...be Jira mezatace ba yayi gaba haka nan suka Mike babu kwarin gwiwa sai tashin hankali dake fuskokinsu suka biyo bayan abbah.....

  A kofar gidan Malam rabiah kuka takeyi tana fadin "nashiga uku....Dan Allah kayi wani Abu abbah Akan wanan lamarin inason yaya Fatima kayi wani Abu aljanin nan ya dawo da ita"....wasu Yan Mata da sukai musu kuriiii da ido suna jinjina Kai suka kalli juna ko wacce Tasha ado kallo Daya zakayi musu kasan cewar Yan jamia ne...abba bece komiba yasa Kai ya Shiga napep dole Suma suka shigo sukabar kofar gidan,

*********
  Gimbiya rumaisa na zaune gefenta zagaye da bayi wasu na Mata gyaran farce wasu nayi Mata yankan kumba wata baiwa sanye da jajayen Kaya ta shigo ta zube a gaban rumaisa "ranki ya dade Fulani na son ganinki a sashenta"

Yatsina fuska rumaisa tayi ta dau mintuna kafin ta iya bata amsa cike da sarauta "je kice Mata gani nan zuwa"

Ta Mike ta fice cikin sauri,tsaki rumaisa taja "ni wanan matar Mai take nufi Dani ne?...mtswww ban fiyeson shisshigi a lamurana ba da ta barni na gudanar da aikina da kaina da yafi"ta dau lokaci kafin ta Mike ta gyara tsatuwarta bayi suka take Mata Baya zuwa sashen mama Fulani....kamar daga Sama ta ganshi a gabanta,kallo Daya tayi masa gabanta ya Fadi kwarjininsa da haibarsa yasa ta sunkuyar da Kai....Saddam yayi murmushin mugunta "har kin tashi a baccin Kenan?ko kinada bukatar a sake sakaki wani baccin ne?"ya d'aga Mata Gira cike da rashin fahimta take kallonsa ya gifta ta gefenta kamshin turarensa ya bugi hancinta take taji kanta ya Sara Mata ta dade tsaye tana binsa da kallo kirjinta na cigaba da harbawa....

RUD'ANIWhere stories live. Discover now