14

173 13 1
                                    

💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻‍♀️

  *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)*

                   *SLIMZY*✍🏻
       _wattpadd@slimzy33_

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

You will always have a special place in my heart miemiey @ *Aisha* *Mahmud* *NEESHARH* ❤️💋

                            *14*

Kiran mamah Fulani ne ya shigo wayarsa cikin sauri ya dago wayar dake ajiye a gefensa,ganin itace yasa yayi tsaki ya wurgar da wayar gefe....ya maida kansa ya jingina gaba Daya bashida natsuwa waishin wanan yarinyar aljanah ce ko mutum tayaya daga ganin hotonta ya Rasa natsuwarsa duk Matan dake garin nan da suke rububinsa kowacce burinta tayi soyayya da Mr rich....tsaki yaja Jin wani Kiran ya Kara shigowa wanan Karon dagawa yayi har zai kashe sai kawai ya Danna recieeve ya kara a kunnensa hade da yin shiru....

"Haba yaron mamah ya inata Kiran wayarka Baka dauka?kana ina?kazo sashena GA breakfast Dinka a nan kayi"

  "Owk"kawai yace hade da datse wayar,jefar da wayar yayi gefe ya runtse idonsa kyakkyawar fuskarta yake gani tana canja masa launi daga Yadda take a hoto zuwa wani irin yanayi Mai ban tausayi....tamkar Mai bacci haka yayi furgigit ya tashi....janyo hoton yayi ya kafesa da ido,kafin ya Mike cikin sauri ya nufi sashen mama Fulani tare da kudurin tafiya gida Komi runtsi.....

Tana zaune a jikin window ta jingina tana sauke numfashi minti minti takan yi murmushi cike da nishadi....tabbas anuwar gwarzon namiji ne babu abinda take tunawa sai Yadda yake sarrafata a Daren jiya hakika jiya tana cikin tarihin rayuwarta....kamar ance ta waiga taga girlmawarsa cikin sauri ta Mike tsaye tana bin bayansa da kallo....Daya daga cikin kuyangin dake  durkushe a gabanta idonta na kanta ta taba ta gefenta tana Nuna Mata gimbiya rumaisa cike da tsaigumi suke jinjina Kai....

Saida ya bace ta saki sassanyar ajiyar zuciya,sai a wanan lokacin ta tunada yareemanta faruk Wanda yau Kwata Kwata bataga koda girlmawarsa ba....Tabe Baki tayi ta gyara zamanta tana kokarin saita natsuwarta......

********
  A sashen mamah Fulani anuwar ya Gama breakfast Sama Sama yaci abincin...."son"mama Fulani takira sunansa cike da kissa da mugunta,

"Bakazo Ka Bani labarin yadda ta kasance tsakaninka da mutuniyar ba"tace tana kallonsa,

Sai lokacin yayi gyaran murya ya tuna da abinda ya faru tsakaninsa da gimbiya matar yareemah....Tass ya labarta Mata a karshe yace "mama Amma gaskiya bazamu Dade muna wanan harkar ba saboda gaba Daya yanzun hankalina na Kan wanan yarinyar danaci Karo da hotonta,inaso yau insamu dad Dina ko yar gidan uban waye a nemamun aurenta"

"Meyasa zakatafi yau anuwar?kabari mana zuwa sati Mai zuwa anuwar"tace cike da kosawa burinta anuwar yayiwa gimbiya ciki....

  "No way mamah daga nan gida nayi Kila indawo yau Kila ba indawo ba sai wani lokaci"Yana fadin haka ya Mike ya fice tabisa da kallo ba haka taso ba,

*******
  Mai gadi kuwa shagala yayi da kallon faruk Yana tunanin a ina yasan Mai irin wanan fuskar tabbas wanan fuskar sananniya ce Amma a INA?zuciyarsa ta basa amsa da yareemah Umar faruk....saidai wanan bashi bane ko shekarajjiya yaji su hajiya na labarin yadda faruk Maison jamaa ya koma ya sauyagaba Daya,

Faruk kuwa cikin faduwar gaba ya karya harshensa ya sauya murya ba yanzun yakeso su Ganesa ba Dan idn suka Ganesa yanzun tabbas akwai matsala hakan yasa ya koma bafullatani zuryan,

"Ina so Inga Mai gidan nan ne....nida kanwata ne muke neman taimako mudin Yan gudun hijira ne"....jinjina Kai maigadi yayi Yana kokarin magana daddy ya fito sanye da jallabiya Mai ruwan Kasa dattijo da farin glass a idonsa....faruk ya d'aga kyawawan idanuwansa Yana kallonsa take yaji wani nishadi cikin zuciyarsa,

RUD'ANIWhere stories live. Discover now