7

225 21 1
                                    

💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻‍♀️

  *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)*

                   *SLIMZY*✍🏻
       _wattpadd@slimzy33_

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

                        *7*

Idonsa yakai fuskar Fatima da ta sharbe da hawaye wadda ta sankare dik jikinta ya saki alamun ta Suma....kallonta yayi jini nabin idanuwansa yasa bakinsa ya hura Mata iska take ta bude ido AI idonta na haduwa da nasa ta saki wata razananniyar Kara hade da fitsari... karar da Fatima tayi ne ya fargar da faruk ya zabura ya Mike idonsa ya sauka Akan tsohon aljani cikin muguwar kama....'innahlillahi wa innahilaihi rajiun"ya furta ya kalli kansa babu motar da suke tafiya ciki wani Daji me Mai dogayen bishiyoyi.....wasu suntsaye ne manya manya suka tunkarosu suna shawagi a Sama....Saddam ya d'aga hannunsa yayi kuwwa take yayi girgiza ya Zama katuwar halitta a gabansu....ja da Baya faruk ya somayi cikin rashin saa yaci tuntube ya Fadi kansa ya bugu da jikin dutse yayi yar Kara,

Teemah kuwa jinkinta ke tsananin rawa da bakinta kmr ana zuba Mata ruwan kankara harshenta yayi Mata nauyi dakyar ta bude Baki tace"Sadda...mmmmm Dan Allah kayi hakuri Kada Ka cutar Dani"

Yar dariya yayi da Saida dajin ya amsa "ke kika cutar Dani?....bil'adama bakusan darajar mutane ba kowa banza kuka daukeshi,ko kuna tunanin cewa Ku kadai kuke rayuwa a cikin duniyarku?bakusan cewa muma muna rayuwa tare daku ba....."yayi kuwwa ya dubi faruk "taurin kanka ya kawoka nan"

Faruk ya fashe da kuka tunawa da yayi yau din nan Ake daura masa aure ko wace wainar Ake soyawa a masarautarsu oho?Bai Gama tunani ba yaga haske ya bayyana a gabansa Yana daga ido ya kalla parlorn mahaifinsa ya gani gefe momynsa nata faman kuka Mai martaba Ransa a bace daga ganin Alama fada akeyi....faruk ya durkushe a wajen ya d'aga hannu Sama zaiyi addua Saddam yasa hannunsa Mai tsayi ya rike hannunsa yayi wata hajijiya ya jefasa cannnn Sama,

Teemah ya fuzgo hannunta tahonan gareni matata....yace Yana murmushi da hawayen jini ya hura iskar bakinsa yayi girgiza ya dawo kyakkyawan saurayi Saddam dinsa sakkkk....yayi Mata murmushin keta kallonsa takeyi ko kiftawa batayi hawaye na wanke Mata fuska tayi saurin daga Kai ta hango faruk can Sama Shi be fado ba Shi beyi Sama ba ta saki kuka,

Fuzgota yayi ta fada jikinsa yakai fuskarsa fuskarta ya fito da harshensa take harshensa ya rabe biyu kmr Na maciji tace "wayyooo Allah abbah.....wayyooo rabiah"ta kwalla kara

********
  Tana sanye da lafaya mara nauyi ta fito parlorn Mai martaba ko ganin gabanta batayi kamar daga Sama taga faruk a gabanta....cikin sauri taja da Baya ta murtsuka idonta ta zaro ido kallonta yakeyi Yana Dan murmushi,

"Momy"ya Kira sunanta cikin wata irin siga wadda Saida gabanta ya Fadi....tayi saurin kallonsa tabbas faruk dinta ne saidai to meyasa ya dawo a cikin Daren nan?

Fashewa tayi da kuka "faruk Dama kana nan kasakamu a cikin tashin hankali dagani har Mai martaba?faruk maiyasa katafi wajen wanan yarinyar wadda kaida kanka Ka Bani labarin rayuwarta na cikin hatsarin mugun aljani?"

Saddam yadan cije bakinsa cike da takaici wato shine mugun aljani?a zahiri gyada Kai yayi"nidai momy banason auren da zakuyimun shiyasa na tafi"....

Wata daga cikin bayin gidan da bata rigada ta kwanta ba ta leko ganin faruk da momy yasa ta jinjina Kai cike da gulmacikin sauri tayi sashen mama Fulani....

Bin bayan momy yayi har parlornta ya tsaya tsaye Yana kallonta tana kallonsa mamakin faruk yaki karewa a idanuwanta dubi Yadda ya canja ya Kara kyau saidai faruk ya Zama mara kunya tunda yake kallon cikin idonta.... takaici ne ya lullubeta ta dubesa "ficemun daga daki nafada maka tunda bakinka bazai iya budewa ya Bani hakuri ba Ka tsaya akaina kana kallon kwayar idona faruk abinda da bakayi"sai kawai yayi Mata dariya ya fice...

Yana fitowa ya bace ta leko cikin sauri tana Kiran sunansa "faruk......"bataga ko keyarsa ba ta koma ciki ta rufo kofa ta jingina da kofar ta fashe da kuka....cike da takaici wani irin masifa ke tunkarota?Mai faruk yakeso ya Zama?shin so yakeyi mahaifinsa ya tsanesa?...hawaye suka gangarowa momy ta runtse idanuwanta....

*******
Washe gari da safe,

Mai martaba Yana parlor mama Fulani Tasha lafaya golden Mai shegen tsada momy tayi sallama kamshin turarenta ya gauraye dakin gaba Daya,

Durkusawa gaban sarki tayi "ranka ya dade Allah ya taimakeka barka da safiya"

  Juyar da Kai Mai martaba yayi har yanzun yanajin kunar abinda faruk yayi masa gashi jiya an sanar masa da ganin faruk din a cikin masarauta "lafiya"yace ya kauda Kai,

Ta nisa "Ina neman agajin sarki"...daga Mata hannu yayi "dakata....karki kawomin wani kissa da raini bayan dik abinda danki yayi kece sila kuma kina sane?"tayi saurin dago Kai zatayi magana "idan kikayi magana sai nayi mummunan bata miki Rai Dan haka kisani labari ya isomin cewar faruk ya shigo masarauta jiya bayan kinbar nan yaje wajenki har dakinki ya Shiga haka ne?"

Ta jinjina Kai cike da damuwa momy dakyar ta hadiye wani miyau Mai daci tace"Afuwan ranka ya dade haka ne tabbas....Amma banida masaniya Akan danka magaji faruk baizo gareka ba"

  "Faruk bazai taba gadon sarauta ba,Dan haka na cire faruk daga sahun yarana"....hawaye ya gangaro a idon momy bakin ciki ya tokare Mata wuya take taji haushin faruk da kiyayyar Fatima ta darsu cikin zuciyarta babu Wanda ya janyo wanan gagarumar matsalar sai Fatima budurwarsa Wanda adalilim son da yake Mata gashi ya sabawa iyayensa,

Yunkurawa tayi takaici ya hanata cewa Komi....hat takai kofa sarki ya dakatar da ita "kimun Kiran rumaisa ki duba kiga Yadda yar mutane ta kwana sanan kice INA nemanta a nan"

Tadan rusunar dakai ta fice...ko ganin gabanta batayi...

******
Mikewa teemah tayi a galabaice tun Daren jiya Saddam ya zuba musu wani Abu Wanda motsin kirki basuyi daga ita har faruk koda ta Mike jini ne ya balle Mata ta kalli kafarta Yadda jini ke gudu ta zare ido....Kenan aljani ya kwanta da ita da wanan halitar tasa?....tunda ya bayyana Mata a tsirara taga halittarsa ta Suma bata sake sanin Inda kanta yakeba Ashe kwanciya yayi da ita...ta rufe ido wasu hawaye masu zafi na danasani suke bin fuskarta,
Ta dubi faruk ta karasa tana Shirin tabada Saddam dake bayanta bata saniba yayi kururuwarda taja da Baya cikin sauri a razane gabanta na faduwa....hangosa tayi nesa Yana takowa Amma bata ganin kafarsa Akan iska yake takowa,

Faruk ya yunkura Yana bin Fatima da kallo cike da fargaba kafin ya tambayeta Saddam ya iso"nine na kwanta da ita Ko haramun ne?aurene fa an rigada an daura dubban jamaa sun shaida auren Fatima da Saddam aljani...."ya fashe da dariya,

Kuka ta saki ta durkushe a wajen faruk ya dubeta haushi da takaicinta suka lullubesa tabbas yanason taimakonta kuma zaiyi kokarin taimakonta Amma bayajin digon Sonta a zuciyarsa....

Itako tausayi faruk ya bata wani irin sonsa taji Yana ratsa zuciyarta tanaso yayi Mata magana ko zataji dadi Amma tunda suka iso wanan dajin a Daren jiya ko kallon Inda take bayayi Mai hakan ke nufi?.....

"Faruk.....jini ne a jikina yake Bina jinin jikina zai kare Ka taimakeni"ta rushe da kuka,

Ya watsa Mata wani irin kallo Wanda Saida gabanta ya Fadi sanan ya cije lebensa yayi zaman Yan bori kansa na Sara masa yanaso yasan halin da mahaifiyarsa take ciki yasan dik Inda take yanzun tana cikin tsananin tashin hankali....kwalla ta cicciko a idonsa.....Saddam ya d'aga hannunsa Sama ya hura iska wuta ta tashi take plate din abinci ya bayyana a hannunsa ya ajiye ya saki wata dariya....ya kalli faruk "kanada taurin Kai yaro bakayimun komiba kawai Ka shigo gonata ne yasa kaima nake kurba maka ruwan azaba ta...nabarku kun kwana a nan ne gobe zamu bar nan zamu tafi Libya ainihin Inda nakeso muyi rayuwar amarci nida amarya ta matukar natafi Libya daku shikenan Zan mantar da kowa Ku"

Zabura faruk yayi ya Shiga girgiza Kai "inaaa haka bazata kasance ba ta yaya zaibari aljani yayi galaba akansa?AI idan yafi karfinsa baifi karfin Allah ba...faruk ya samu kwarin gwiwa....

Mika hannu Saddam yayi ya cafko Fatima hannunsa kamar zalbe daga Inda yake ta kwalla Kara ya matseta a jikinsa take ta saki fitsarin wuya ya kafeta da idanuwansa wadanda basuda kyaun gani.....haske ne ya fito daga idonsa ya Shiga idanuwanta take taga wani haske ya kashe Mata ido cikin mintuna uku ta runtse ido koda ta bude idanuwanta dindimmmm bata ganin Komi a gabanta...duhu ta gani...ta saki kuka "wayyooo Allah Bana gani Bana gani...na makance faruk idanuwana basa gani"....jikin faruk ya kema rawa ganin Saddam yayi masa wani kallo yasan kansa zaiyo take ya soma ambaton Allah a cikin zuciyarsa cikin tsananin tashin hankali da fargaba gabansa ya tsananta faduwa.......





*SLIMZY*✍🏻

RUD'ANIWhere stories live. Discover now