💥 *RUD'ANI...*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)*SLIMZY*
Wattpad@slimzy33*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*Mai bukatar a tallata masa hajarsa 07042277401*
*38*
Hmmm, tafiyar daban take, hakan salon ma daban ya ke, Labarin Nadiya! Nadiya...... Labari ne da aka gina bisa halin mu na yau da kullun, ba kuma gama garin labari ba! NADIYA, matar aure, yayin da ƙaddara ta afka mata to soma soyayya da wani mutun daban, wanda ta ke jin inda babu shi, ba zata taɓa rayuwa ba, gefe guda kuma Sadeek, wanda ya mutu a kan ƙaunar ta kuma ƙani ga Alaji....!
Bai taɓa haihuwa ba! Hasali ba zai haihu ba! Kwatsam sai ga ciki daga matar shi? Shin ɗan waye? Hmmm m... Soyayya, tausayi, cin amana, duka a littafin DAMA ACE.....Kin shirya?
Ki biya kuɗin ki domin tafiyar da ke, tafiya ce da zata jijjiga zukatan makaranta, Naira 500 9994468172 Access bank fiddausi musa tare da shaidar biya ta 08036953516 ko 07042277401.Kuma kin san wani abin ɗaɗin, ba zamu dakata da posting RUƊANI da KUSKUREN SO ba, ko da ace saura basu samu ba, ina tabbatar maku da waɗanda suka biya zasu same shi.
#SLIMZY
#FEEDOHM
#DAMA ACE...Share hawaye momyn faruk tayi cikin damuwa ta tura kofar dakin da yake,Afrah na zaune gefensa na hagu Afee na zaune gefensa na dama tana rike da hannunsa idonsa a lumshe aka tura kofar da sauri ya bude kofar ya kafe momy da ido fuskar fatima keyi masa gizo a fuskar momynsa ya mike da sauri dikda irin ciwon da yakeji haka ya dafe kirjinsa gefe daya bangaren zucuyarsa dakyar yace "momy....momy fatima ta tsaneni tak'i amincewa dani ko?"
tausayin Anwar ya kama mahaifiyarsa ta kalli daddy da idanuwanta da suka kumbura ta sunkuyar da kanta daddy ya ruko hannunta "calm down momyn yara kada ki tada hankalinki zai samu sauki"
ta kallesa da jajayen idanuwanta ta girgiza kai saiga wadu sababbin hawaye,"ta yaya bazan tada hankalina ba juya kaga yaron nan yadda ya zama wallahi yarinyar nan ta cuceni daga taimako?Allah ya wadaran wanan taimako da mukai mata ashe tsatsa zata dasa mana a zuciyoyin mu duba kagani kamar tsafi yaron nan ya fita hayyacinsa saboda wata soyayya can"
Afee a raunane tace "momy yanzun kina nufin Anty fatima bata amince da yaya Anwar ba?bata duba halin da yake ciki ba ta agaza masa a lokacin dayake bukatar agaji kamar yadda ya agaza mata da rayuwarsa baki daya?"
cikin fushi Afrah ta share hawayenta tace "fatima butulu ce kune baku saniba nadade da sanin ba son yaya Anwar takeyi ba dama karya takeyi munafukace butulu ce"kalmomin Afrah akan fatima anwar ji yayi kamar ana watsa masa rushi a jikinsa ya D'anyi tari muryarsa a dashe ya kallesu ya lumshe ido inama zai iya fada musu shine sanadin daya rasa fatima?inama zai iya warware musu sirrinsa dake lullube da bargo wanda zuciyarsa ke harabawa da tsananin tsoro da furgicin ranan tonuwar asirinsa?
daddy ya zauna gefen gadon cikin sigar lallashi ya kira sunansa
"Anwar"ya dago manyan idonsa batare da ya amsa ba ya zubawa daddy ido tamkar yana fahimtar sa daddy cikin sanyi ya soma masa nasiha akan samu da rashi tare da kaddara dik na Allah ne tabbas daddy yayi gaskiya kuma Allah ya nuna masa iyakarsa wasu sababbin hawaye suka soma zubo masa jikinsa yayi sanyi ya kasa kwakkwaran motsi ya lumshe idonsa yanajin bugun zucuyarsa kalaman fatima na dawowa a kwakwalwarsa....
******
cikin rudewa rumaisa ta zube a gaban mamah fulani "shikenan yarinyar nan tasan sirrinmu tamu ta kare na tabbatar ta tanadi makaman yakin da zata yakemu dashi asirin mu na gab da tonuwa mama fulani kiyi wani abu"ta fashe da kuka mama fulani kad'a kafa kawai takeyi ta d'ora kafarta daya kan daya ta jike da gumi,ta cije lebe tace,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...