45

119 10 1
                                    

💥 *RUD'ANI...*🤦🏻‍♀️

     *FREE BOOK*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)

          *SLIMZY*
  Wattpad@slimzy33

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

*Mai bukatar a tallata masa hajarsa 07042277401*

                       *45*

*Sakon ban hakuri zuwa ga masoyana dake jiran littafin rud'ani su gafarceni kunsan karfen nasara bayi da tabbas amma komi yayi settling Insha Allah aski yazo gaban goshi😁*

Hankad'a rumaisa faruk yayi had'e da wanka mata wani gigitaccen mari wanda nan da nan taga wasu taurari idonta ya soma ganin duhu "ke ni zaki rungume saboda tsabar iskanci da rashin kunya?ke yanzun rumaisa idan ance miki ki rungumeni saiki rungumeni?to karya kikeyi idan kin rungumenine dan ki had'ani fada da matata karyarki tasha karya"..

"haba.....faruk nima fa mat...."bata karasa fadin ita matarsa bace ya kara zabga mata wani gigitaccen mari fatima ta tako a hankali tazo kusa dashi yana hango Kishi a kwayar idonta amma hakan be hanata yin murmushi na kissa ba tace "rungume mijina a gabana bashi zaisa na yarsa cewa kinada muhalli a zucuyar Faruk ba rumaisa,kuma bashi zaisa kisamu damar shiga zuciyarsa ba kingane ko da irin kallon da kikemun na tabbatar da cewar da gangan kikayi dan zucuyata tayimun zafi amma kisani banji komiba kuma harabada bazaki samu abinda kikeso ba dikda kema matarsa ce kinada hakki akansa"

fatima ta karashe maganar tana satar kallon faruk aiko take ta hango bacin rai karara a kwayar idonsa yayi mata wani kallo wanda ita kadai tasan maanarsa koba komi taji zafin ganinsa da rumaisa rungume da juna ta fada masa maganar data kona masa rai yaji me taji,

"karki sake fadin matatace dan rumaisa ba matata bace wanan furucin da kikayi ne yasa zan yanke wanan hukuncun dan idan tanaji a cikin zucuyarta ita matatace ta daina rumaisa na sakeki saki uku"daidai nan Aysha ta taho sashen tana fadin "Anty fatima naje sashenki bakinan......"cak ta tsaya jin hukuncin da faruk ya yanke,

wani jiri ne taji yana daukarta rumaisa take ta yanke jiki ta fadi hade da sakin wata gigitacciyar kara wadda ta amsa duka cikin gidan, Yana gama magana ya fuzgo fatima da hannunsa ya nufi sashenta da ita,

Aysha kuwa a guje ta nufi sashen momy ko ganin gabanta batayi sukai kicibis da momy da wasu bayi guda biyu "ke Aysha ihun menene mukeji a ciki. gidan nan?inacan tare da su momyn Anwar naji ihu na fito"

jikin Aysha na rawa tace "am umhmm Dama yaya faruk ne ya saki Anty rumaisa saki uku naje sashen kenan zam shiga najishi "

"innahlillahi shi menene ya kaisa sashen rumaisa?meyasa yaje?sanan waye ya bashi damar aikata hukuncin daya aikata akan rumaisa bayan mahaifinsa yace yabar hukunci a hannunsa?ta dafe kanta tace, ina yayi?"

"naga yayi sashen Anty fatima"

"kiramun shi"momy tace cike da rud'ani ta nufi bangarenta cike da sababi tana mita... 


faruk cikin fushi ya dubi fatima "meyasa zaki fadi abinda kika fadamun? kinga yanzun kinsa idona ya rufe na yanke hukuncu batare da jiran mai martaba ba yanzun me zancewa Abbah?"

tabe baki fatima tayi ta juya baya batace komiba ya juyo da ita gabansa "inayi miki magana kimun magana mana kina jina ina magana?"

wani kallo tayi masa ya fuzgota zai rungumeta taja da baya ta turasa yana kallonta cike da mamaki tace "Allah ya tsareni Allah ya kiyaye ai idan kaga ka rungumeni to wankan tsarki kayi, maana ka cire rigar jikinka kayi sabon wanka kasa wata dan baka isa ka rungumi wata da Riga kazo kace zaka rungumeni da ita ba ah tou nika bani waje ma inada abubuwan yi na shirye shirye"tayi gefe zata wuce ya rukota ta janye,

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 16, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RUD'ANIWhere stories live. Discover now