💥 *RUD'ANI...*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)*SLIMZY*
Wattpad@slimzy33*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*Mai bukatar a tallata masa hajarsa 07042277401*
*34*
Alwala Anwar ya gabatar haka kawai yaji gabansa ya tsananta faduwa baisan dalili ba zuciyarsa da gangan jikinsa suna bashi wani abu na faruwa tamkar fatima na cikin wani hali.....saka kafarsa yayi cikin masallaci dai dai nan ya kalli faruk dake kwance rike da kansa hawaye nabin gefen fuskarsa ya kalli mai martaba da jamaar cikin masallacin wadanda suke adduar karshe ta d'aurin aure....
"Masha Allah d'an sarki jikan sarki yarima Allah ubangiji yasa kayi adalci a tsakanin matanka.....mai martaba ka cika adalin sarki mai kaunar al'ummarsa"cewar galadima wanda bakinsa yaki rufuwa mai martaba da kansa yasa hannu a goshin faruk yaji zafi rad'au "faduwar ta mecece?umar faruk inace na mallaka maka muradin ranka fatima?katashi ka godewa Allah ka godemun sanan zan gindaya maka sharrud'a masu karfi akan fatima da rumaisa"
tsaye Anwar yayi jikinsa na karkarwa maganganun mai martaba da surutan fadawa da jamaar masarauta itace take yawo a k'wak'walwar kansa ya kalli galadima wanda suka had'a ido jikin galadima yayi sanyi kallo daya yayiwa Anwar ya dauke kansa ya gagara kara kallonsa
baya Anwar yayi hade da yanke jiki ya fadi numfashinsa yaji yana kokarin kwace masa,
"subhanallahi innahlillahi wa innahilaihi rajiun"mutanen masallacin sukayo kan Anwar wanda tuni idanuwansa sunyi sama suna kokarin rufewa mai martaba har ya kai kofar fita ya juyo faruk zama yayi dirshan ya dafe kansa tunani barkatai akansa yau watarana ce da bazai taba mancewa a rayuwarsa ba dama zai mallaki fatima a matsayin mata?juyawa yayi ya kalli Anwar wanda yake kwance sharban a sume mai martaba ya bada umarnin akaisa masarauta karamin parlorn fada sanan ya bada umarnin a kira doctor,
rumaisa tare da mama fulani ne zaune a babban parlorn mai martaba wanda ta nan sukaga an shigo da Anwar zaayi karamin parlor kallon juna sukai sanan suka kalli dogarai da kuma galadima da ya musu jagora,
"menene ya samesa?meke faruwa?"take tambayarsu cike da mamakin ganin Anwar wanan halin gaban rumaisa ne ya fadi ya dubi mama fulani kasa kasa tacw "kardai asirin mu ne ya tonu,gabana na tsananin faduwa mama fulani"numfashi mama fulani ta sauke,
"ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru wanda zaiji wanan sirrin matukar kin aikatamun abinda nakeso".....jinjina kai rumaisa tayi ganin mai martaba ya shigo cikin tashin hankali yasa duk suka kwantar da kai tare da shirin aiwatar da kudirin daya kawosu,
doctor ne ya shigo da sauri hannunsa rike da first aid box ya nufi inda aka Shiga da Anwar,
"Ranka ya dade?meke faruwa ne naganku dik cikin wani yanayi ko wani mummunan abu ya faru ne?naga faruk tamkar ba cikin hankalinsa ba"ta kalli faruk daya shigo idanuwansa jajir,
"tou faruk nasan farin ciki babu abinda bayasawa inaga murnar nasarar auren zahra da aka daura masa yasashi cikin wanan halin,shi kuma Anwar ni banmasan daga inda yake ba kawai ganinsa mukai ya shigo masallaci shine ya yanke jiki ya fad'i"..
wasu hawayene suka fara gudu a fuskar rumaisa wadda dama da wanan plan din daidai abinda yayi shocking dinta jin an daura auren faruk da fatima shikenan faruk yasamu abinda yakeso ta zama bola yana gab da tona mata asiri,..mama fulani ta ruko rumaisa cike da kissa "kidaina kukan nan da kikeyi gaban mai martaba kike kamar yadda uba yake ga faruk haka kema nasan tabbas akwai ciwo abinda akai miki kuma ban taba tunanin faruk zai aikata hakan ba"gaban faruk ya yanke ya fadi da yake tsaye,mai ya aikata?yake tambayar kansa nan da nan yaji kansa ya sara ya juya zai bar parlorn mama fulani ta dakatar dashi,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...