💥 *RUD'ANI...*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)*SLIMZY*
Wattpad@slimzy33*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*Mai bukatar a tallata masa hajarsa 07042277401*
Ga mai bukatar littafaina akwai complete documents
*Zainul Abideen 300*
*Izza Ta 300*
*Duhu sarkakiya 300*
*Ramin mugunta 300*
*Kukan zuci 300*
*K'ugiya 500**shin kunason in cigaba da littafin rud'ani babu tsallaken rana?ku hanzarta kuyimun cinikin wadanan littafan ga maison biyar din 1k kacal a tuntubeni ta nan a hanzarta kafin intafi yaji.... 07042277401*
*33*
k'arar bude kofar momyn Anwar tasa Afnan mikewa ta zauna tana kokarin kunna side lamp Afrah ta d'aga kanta cikin bacci tayi mik'a had'e da hamma tace "ke kuma lafiya kika mike kika zauna hade da kokarin kunna mana haske a daki"kafin ta karasa magana haske ya karade dakin runtse ido tayi haske na kashe mata ido cike da masifa take kokarin mikewa suka jiyo shasshekar kukan momy kusan a tare suka duro daga kan gadon suna kici kicin bude kofat fita meeniosky ta mike zumbur ta zauna cike da tsoro ko lafiya momy ke kuka tsakar daren nan?nan ta mike cikin sand'a ta tsaya daga jikin kofa bazata iya fitaba sakamakon daddy da takejin muryarsa,"haba momyn yara meyasa zaki kuka bayan Allah be saki kuka ba kiyi nasa addua dik inda ya tafi na tabbatar Anwar will never leave us"cikin kuka momy ta soma magana,
"kana ganin yadda gaba daya yaron nan yake nema ya fita hayyacinsa saboda wanan yarinyar haba so aiba hauka bane da zai dauki mota ya fita cikin daren nan wayasan inda ya nufa?ko masarauta ya tafi?"
"Anya Anwar zai nufi masarauta a daren nan?bari na gwada kiransa a waya koda zai dauka muji inda ya tafi"daddy ya kalli gefen da yan biyu ke zaune sun zabga tagumi nusamman afnan wadda tuni tun fitowarsu ta fara zubar da hawaye ya juya ya kalli momy data rafka tagumi tana shasshekar kuka cikin tsananin damuwa,..
gudu sosai Anwar ke shekawa akan titi ya sanya karatun alkurani cikin motarsa suratul bak'ara yana saurare gabaki daya hankalinsa baya jikinsa tuki kawai yakeyi minti minti yana dukan sitiyarin motar cike da damuwa yakan runtse idanuwansa fatima yake gani dazun data runtse idonta tana zubar hawaye gumi kawai yakeyi kiran daddy ne ya shiga wayarsa da sauri ya kalli wayar,
ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa idanuwansa sunyi zuru zuru wayar ta cugaba da ringing bai dauka ba tana katsewa daddy ya soma kira a karo na biyu,
a dausashe yace "daddy why meyasa kake kirana kabarni kawai saina cikawa Fatima burinta saina rabata da wanan Aljanin"wayar ta kusa tsinkewa sanan ya danna recieve,
daddy ya kalli momy ta zabura jin muryar Anwar "Hello daddy"hada baki sukai a tare wajen fadin "Anwar kana ina?ina kafita da mota zakaje a cikin daren nan?"girgiza kai Anwar yayi ya shafa kansa yace "natafi kauye wajen baba wuro karbowa fatima magani"
a tare sukace "what?me kake fada Anwar?ko zakasaka kanka a hatsari sai kasa da daddare?"murmushin takaici yayi yana kada kai "na shirya fuskantar koma menene akan fatima har sai na sama mata lafiya na mallaketa"yana karasa mgnr bai jira cewarsu ba ya kashe wayar,
gudu kawai yakeyi cikin daji bakajin kukan komi sai tsintsatsaye da macijazai da kwadi da kukansu ya karad'e cikin dajin wata katuwar halitta ce kamar giwa yaga ta taso tayo kan motarsa wadda be gantaba da farko tun karosa kawai tayi hannunsa ya fata rawa ya soma tangal tangal a titi motarsa tayi kamar zata fadi kamar daukewar ruwa ya nemeta ya rasa gumi sai karyo masa yakeyi addua kawai yakeyi cikin tashin hankali yakejin kuwwa a kunnensa....
********
kallonsa fatima tayi taja da baya kadan ya wuceta ya shigo tana binsa da kallo gabanta ya tsananta faduwa.....mamakin faruk takeyi tayaya zai baro d'akin matarsa yazo gareta a wanan daren?gashi tana tsoron masa magana a tunaninta faruk ne kar yagane haukar karya takeyi,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...