💥 *RUD'ANI...*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)*SLIMZY*
Wattpad@slimzy33*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*Mai bukatar a tallata masa hajarsa 07042277401*
*36*
Daga *slimzy* marubucuyar wanan littafin rud'ani
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Labarin Nadiya! Nadiya...... Labari ne da aka gina bisa halin mu na yau da kullun, ba kuma gama garin labari ba! NADIYA, matar aure, yayin da ƙaddara ta afka mata to soma soyayya da wani mutun daban, wanda ta ke jin inda babu shi, ba zata taɓa rayuwa ba, gefe guda kuma Sadeek, wanda ya mutu a kan ƙaunar ta kuma ƙani ga Alaji....!
Bai taɓa haihuwa ba! Hasali ba zai haihu ba! Kwatsam sai ga ciki daga matar shi? Shin ɗan waye? Hmmm m... Soyayya, tausayi, cin amana, duka a littafin DAMA ACE.....Kin shirya?
Ki biya kuɗin ki domin tafiyar da ke, tafiya ce da zata jijjiga zukatan makaranta, Naira 500 9994468172 Access bank fiddausi musa tare da shaidar biya ta 08036953516 ko 07042277401.
Kuma kin san wani abin ɗaɗin, ba zamu dakata da posting RUƊANI da KUSKUREN SO ba, ko da ace saura basu samu ba, ina tabbatar maku da waɗanda suka biya zasu same shi.c
cikin kuka ummah ta nufi fatima wadda ke rungume a hannun faruk da gaba daya ya dimauce "kayi wani Abu Dan Allah kada aljanin nan ya tafi da fatima bazan iya rayuwa babu ita ba please galadima ka taimakeni"ya karasa maganar muryarsa na rawa,..
rabiah cikin kuka take rike da hannun fatima wadda kw gurnani kamar doki wata majina da miyau na fitowa daga bakinta kamar wanda yasha poison galadima nata tofa mata addua ya had'a manyan yan yatsanta na kafa ya daure da farin kyalle,
"menene kakeyi haka galadima daure yatsunta biyu kamar wadda ta mutu?wani irin abu kakeyi idan bazaka iyaba mutafi wani waje"cikin kosawa yayi maganar momy wadda hankalinta a tashe yake ta daka masa tsawa tana rike da kafadar ummahn fatima wadda ke rizgar kuka,
"faruk wace irin magana ce wanan da rashin hakuri?yanzun kai bakaga kokarin rabasu yakeyi ba""momy kalli yadda farin dafara ke fitowa a bakinta anya ba poisoning fatima akayi ba aljani zaiyi hakan ne?"
galadima ya girgiza kai yana murmushi "Ranka ya dade bakasan sharrin jinnu ba,to wanan hade kafar da nayi na daure kamar gawa da kace dauresa nayi yadda ba gudu babu ja da baya "Ajiyar zuciya faruk yayi idanuwansa jajir gumi ne kawai yakw karyowa a goshinsa,
galan din ruwan maganin da Anwar ya karbo ya dauko faruk ya runtse idonsa yanzun kenan abinda Anwar ya saida rayuwarsa ya karbo shine zai warkar da fatima?wani kishi yaji ya turnuke sa ya runtse idonsa nan da nan kunnuwansa ke juyo masa sautin kukan Fatima a tare da Anwar yasan tana sonsa tana tsananin kaunarsa shiyasa take kuka,
galadima ya soma yayyafawa fatima wanan ruwan nan da nan ta soma burgima tana ihu yuhana cikin wata irin murya mai cike da azaba yake fadin "karka kasheni kuyimun adalci itace ta Shiga gonata shiyasa nakeson koya mata hankali ga masu hali irin nata nayi maka Alkawarin zan rabu da ita bazan sake dawowa ba karka kasheni inada y'ay'a da jikoki"cikin azaba yake maganar,
faruk ya kalli fatima yadda yaga hawayen jini na zubowa daga idonta ya zabura,"jini ke zubowa daga idonta galadima ka tsaya ba yuhana bane fatima ce karta makance idonta ya tsiyaye"yana kokarin janye galadima momy ta fuzgosa ta sharara masa mari a karo na farko tana jifansa da wani irin kallo,
"kafi mahaifiyarta sonta ne juyo kagani yadda ta runtse ido batason gani saboda tsananin soyayyar dake tsakanin d'a da mahaifi kai awa kaida kaganta da hakoranta talatin da biyu ka natsu so ba hauka bane ka bari a rabata da wanan jarabawat data tsinci kanta "jikin faruk yayi sanyi ya kalli ummahn fatima yadda ta runtse ido tana hawaye gumi na karyo mata ya juya ga rabiah wadda ta had'a kanta da gwiwa tana rizgar kuka,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...