30

68 11 2
                                    

💥 *RUD'ANI...*🤦🏻‍♀️

     *FREE BOOK*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)

          *SLIMZY*
  Wattpad@slimzy33

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

                  *30*

*IDAN KAJI GUƊA DA LABARI...!!!*

_INA MASOYAN ASMY B ALIYU? ALBISHIRIN KU? KUCE GORO....! OHO... HO.. HO... KO KUNSAN A SABUWAR SHEKARAR NAN TA SHIRYA KAWO MUKU DADDAƊAN LABARI MAI SUNA Muhabbatil Qalb? TAFIYAR TA FARA NISA, WASAN KUMA YANA TA DAƊI._

_*SHIN KINSAN YADDA AKE SHIGA CIKIN RAYUWAR ƊIYA MACE A LALATA MATA MUTUNCI, A TARWATSA DUK WANI KYAWU NA TA? KUNSAN YADDA ZAMANI YA CANZA? KI SHIGO CIKIN TAFIYAR DAN KISHA ROMAN ILIMI DA KUMA HANYOYIN DA ZAKI SAN ANA BI DAN SHIGARKI CIKIN WANNAN HATSARIN.*_

ASMY B ALIYU KUNSAN BATA WASA A CIKIN TAFIYAR TA. KARKI BARI AYI TAFIYAR BABU KE. SAMUN ILIMIN KADAI ABIN ALFAHARINKI NE MAI SIYA.

*MUHABBATIL QALB*🔥
*MUHABBATIL QALB*🔥
*MUHABBATIL QALB*🔥

AKAN  NAIRA 300 Kacal ne.

0004157137
Asma'u Buhari Aliyu
Jaiz bank

Ko katin waya ta 07043079282
Shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp

wani kallo dukkansu sukebin Anwar dashi cike da mamaki lokaci daya farin cikin da yake fuskarsa ya gushi gumi ne kawai yake karoyo masa cikin seconds idanuwansa suka cicciko da hawayen da besan dasu ba ya kalli fatima da take hawaye yasani tabbas fatima tasan abinda ya aikata zata tsanesa tsana mai tsanani daddy kuwa mamakin anwar yakeyi ya rukosa jikinsa ganin yana kokarin yanke jiki ya fadi,

"Anwar lafiya?meye yasameka fadamun meke damunka kana farin cikin samun cikar burinka nan da nan farin cikin ya gushe a fuskarka?"dukkansu suka zurawa Anwar ido wanda tuni hawaye ya fara zarya daga kwayar idonsa,

"daddy lokaci ne yayi da zan girbi abinda na shuka wanda ba Alheri ba halin da kuka dade kunayinun addua akansa naki canjawa saita dalilin wanan baiwar Allah to akwai wata shuka wadda nayi wadda lokaci yayi tayi fure"

ummahn fatima cikin rashin fahimta take kallon rabiah sanan ta juya tace "Anwar lafiyarka kuwa?kodai akwai wani abu da kake boyemun?"

kiran wayar mai martaba ne ya shigo wayar daddyn Anwar yana dubawa yaga mai kiran ya fad'ad'a faraarsa "mai martaba ke kirana"

fatima dake gefe kuwa gabanta ke tsananin faduwa tana kallon anuwar cikin mamaki yadda gaba daya ya sauya idonsa cikin bata ko kiftawa bayayi kamar wanda yakeyi mata kallon karshe tayi kokarin kauda idonsa daga cikin nata wani abu takeji kamar shocking yana Jan ganinta zuwa garesa muryar daddy taji Yana fad'in,

"Masha Allah yabzun faruk aure zaiyi kenan?ga sabuwar jaririya ga sabuwar amarya? Insha Allah zanzo fada dani zaatafi nemaea faruk aure dama kuma kaima zan sanar da kai auren danka Anwar da zaayi dikda a gaggauce zaayi saboda wani dalili"

ji fatima tayi kamar daddy ya caka mata wuka a kirji kenan faruk fushin da yayi da ita zuwa zaiyi yayi auren huce takaici?dan tasan mai martaba bazai taba hakura ta dadi ya aureta ba,

daddy ya dubi ummah yace "naso yau zuwa yamma ayi abun nan amma sam ban yarda da lamarin anwar ba dole zan koma gida dashi kodan halin da yake ciki ina zargin kodai yasamu buguwa a kwakwalwarsa ne?"sai lokacin Anwar ya kalli daddy harshensa yayi masa nauyi yanajin wayar da daddy keyi da mai martaba amma yasan mai martaba bazai amince da Auren faruk da fatima ba dole zaisan yadda yayi yasamu fatima ta ko wani hali a daren nan yasan da zarar ya aureta tsanar da zatayi masa bazatai tasiri ba da wanan tunanin ya numfasa ya dubi daddynsa,

RUD'ANIWhere stories live. Discover now