💥 *RUD'ANI...*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)**SLIMZY*✍🏻
_wattpadd@slimzy33_*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*22*
Kallon kallo meeniosky da Fatima sukeyi Wanda ko wanne gabansa na tsananin faduwa ta bangaren meeniosky kishi ne ya haddasa Mata mugun faduwar gaba tabi kayan jikin Fatima da kallo wani irin hassada da kishi ya taso Mata wani irin kyau da annuri ke fita a fuskar Fatima da kamshin turare Mai sanyin dadi,Fatima kuwa ta tsunci kanta cikin faduwar gaba ne batayi tunanin Zata hadu da wani Dan gidan a bangaren anuwar ba,
Cije lebe meeniosky tayi take dabara ta Fado Mata cike da kissa ta saka kururuwa ta dire tray din dake hannunta ta fashe da matsanancin kuka Mai Kara Wanda daga sashen momy sunajin haka dukkansu suka Mike a zabure afrah tace "laaaa kamar muryar anty meenah momy ita ke wanan kuwwar kodai ya anuwar ya bugeta ne"afee kuwa gabanta ne ya faddi kaddai Fatima ce wanan aljanin ya dawo gareta rigerigen fita sukayi a kofar fita sukai Karo da faruk Wanda shima ya Shiga tambayarsu ko lafiya?
Ihu sukacigaba daji babu Wanda ya bi ta kansa Duka sukaiyi sashen gaban faruk na tsananin faduwa Yabi bayansu yazo wuce sashen Fatima ya kalli kofar dakin yayi jimmm kafin ya bi bayansu....
Jin tahowarsu yasa meeniosky hankada Fatima ta fada Kan gadon da anuwar ke kwance Wanda jikinsa ya jike da gumi dagashi sai singlet tasa kuka tana nunata"dama karya kikeyi karyar makanta kikeyi kika shigo cikin wanan iyalin don ki lalata musu rayuwar yaro... karuwancin naki har yakai ki biyosa har daki kizo don biyan bukatarki Yana cikin tsananin rashin lafiya?"
Tsaye faruk yayi a jikin kofar Yana kokarin cewa "meke...faru...."harshensa ya datse ganin Fatima a sashen anuwar cikin rabtsatsiyar doguwar Riga abun mamaki a gadon da yake kwanciya idonsa da nata suka hadu da juna Wanda taji wani shock ya Shiga jijiyoyin jikinta narkakkun idanuwanta ta zuba masa na seconds kafin ta dauke Kai saboda tsananin kyawunsa da kwarjini da Allah yayi masa tabbas wanan faruk ne domin taganesa tasansa a shigar talakawa da yakeyi Mata yazo wajenta batasansa a Dan sarki yarima Umar faruk ba a kurarren lokaci tasansa lokacin data Rasa ganinta.... meeniosky cikin kuka ta kalli faruk take ta Ganesa tabbas shine Wanda yakeson Fatima a zuwan talaka Wanda akace ta wulakanta batare da sanin Dan sarki bane.....Kishi ne ya turnuke faruk idanuwansa sukai jajir ya Kasa dauke idonsa akanta karar saukar Mari da momy tayi Mata ji kake tassss yasashi saurin dagowa ta rike kuncinta hawaye wani nabin wani "dole ma yau zakibar gidan nan munafuka dama basaja da wasan kwaikwayo kikeyi mana kenan da kika sanar Damu cewar ke yar gudun hijira ce dakeda Dan iskan Daya kawoki ya ajiye Ashe da idanuwanki karuwanci kawai kikeyi shiyasa kika dauke hankalin Dana Ashe da abinda kikedashi a daki kike bashi Allah ya isa tsakanina dake bazan Jira zuwan alhaji ba barinki gidan nan ya Zama dole"...hawaye ya wanke fuskar Fatima ta juya GA dubanta GA anuwar Wanda yanason yin magana ya Kasa saboda tsananin ciwon da yakeji tausayinsa ya lullube Fatima samm bataji zafin tozarcin da momy tayi masa ba sai tausayinsa Daya lullubeta a sanadin samun lafiyarta ya fada cikin wanan yanayin,
Dakyar ta bude Baki tace"momy Niba karuwa bace hasalima bantaba karuwanci ba wani namiji Bai taba rikemun koda Dan yatsa ba,ganina cikin dakin yaronki kuwa shine nazone inyi masa godiyar dawainiyar da yayi Dani Wanda a sanadin hakan nasamu ganina ya dawo Amma Niba makauniyar karya bace"...
Fincikota momy tayi tana kokarin rufeta da Duka cikin muryarsa wadda take fita dakyar yace "momy....karki taba Fatima domin Fatima ruhina ce idan kika tabata tamkar ruhin danki kika taba idan kuma kince ah ah to kiyi Mata wani Abu ni kuma take zaki rasani domin wanan ciwon da nakeyi Zan hadiyi zuciya in mutu ne"galala momy tayi tana kallon anuwar Wanda ke magana dakyar take hankalin momy ya tashi Jin yadda yake sauke numfashi Yana rike da kansa dake barazanar rabewa biyu,
Tausayin anuwar ya lullube Fatima hankalinta yayi mugun tashi ta gefe guda kuwa tana kallon faruk Yadda ya rungume hannuwansa a kirjinsa cike da mamakin Fatima kardai abinda yake hasashene ya tabbata?kallon faruk tayi irin kallon dayayi Mata Mai cike da tambayoyi yasa jikinta yayi sanyi ta Mike Zata fice har takai kofa anuwar yace "Fatima idan kika tafi tabbas Zan Rasa Raina kuma idan na Rasa Raina na rayata a wuyanki domin kece silar hakan...idan ban Rasa Raina ba dik Inda kika Shiga Zan nemoki kuma saina aureki don haka karkiyi gigin tafiya batare da sanin Wanda ya kawoki gidan nan ba wato daddy"Yana maganar hakoransa suna datsewa fuskarsa ta sauya gabaki Daya zuwa wani yanayi Mai ban tausayi juyowa tayi ta kallesa ta share hawayenta tasa Kai ta fice...ganin hankalinsu momy nakan anuwar yasa faruk samun Damar bin bayan Fatima wadda ta nufi sashenta da gudu tana kuka,Tsaye yayi a bakin kofa Yana kallon yadda Fatima ke kuka wato dik wanan kukan tanayinsa ne Akan anuwar?me anuwar din yayi Mata?dawo Mata da ganinta da yayi ne yasa ta dimauce akansa?bayan Shi ya Rasa farin cikinsa da iyalinsa tsawon lokaci a duniyar aljanu a dalilinta?yanzun wanan halarci da sadaukarwar da yayi Mata yasa yasamu gurbi Kenan a zuciyarta?tabbas dole yasan nayi....idan har batabisa ba to ya tabbata tanason anuwar kuma zai rabu da ita koda hakan zai zamo silar mutuwar sa...
Cikin tsawa ya Kira sunanta ran Yan Maza sun Baci Umar faruk"Fatima..... tashi"yace Yana huci,zuciyarta na dukan uku uku ta zabura ta zauna samun kanta tayi da tsananin tsoronsa GA kwarjini da yayi Mata kallo Daya tayi masa kibiyar soyayyarsa ta caki zuciyarta take ta tuna da shine faruk dinta da take burin mallaka a Karo na biyu shine Wanda ya Mata babbar sadaukarwar da koda taron Maza sunkai idi ba zaasamu kamarsa ba....kishi ne ya bayyana a idonsa Yana jifanta da wani kallo itama kallonsa takeyi da narkakkun idanuwanta wadanda suka cika taff da hawaye "kuka kikeyi?"ya tambayeta hade da hada girar Sama Data Kasa....girgiza kanta tayi ta Shiga share hawayenta wasu na Kara zubowa "ba kuka nakeyi ba"
"Tou me kikeyi?kuka kikeyi Akan anuwar ko?kinasonsa ne?"ya jefa Mata tambaya cike da isa da izza ya tsareta da idanuwansa dake Kara furgitata bata taba sanin haka faruk yake da kwarjini ba sai yau..shiru tayi takasa amsawa ya Kara tambayarta cikin daga murya cike da tsoro ta girgiza Kai "ba sonsa nakeyi ba inajin tausayinsa domin a yanzun ya zabi yayi rashin lafiya ni insamu lafiya,wanan rashin lafiyar da yakeyi tasamesa ne a sanadin samamun lafiyar Ido da yayi dikda Mai maganin ya gargadesa Akan inhar nasamu lafiya Shi zai kamu da matsanancin rashin lafiya"
Tsaki faruk yayi zuciyarsa na tafasa yace "look Fatima bazakiyimun rainin wayau da hankali ba kinaji ko Dan haka ki tattara inaki inaki kizo in maidaki gaban iyayenki inyaso na tabbatar a can zansamu Damar aurenki Amma ban yarda dake da zamanki a gidan nan ba"
Gabanta ya yanke ya Fadi faruk be yarda da itaba dik irin dumbin soyayyar da takeyi masa ya mance cewar shine ya kawota nan din yanxun kishi ya rufe Mata ido yazo tafiya da ita?shin Mai tafiyarta zai haifarwa anuwar Wanda yayi Mata sadaukarwa waye zai Kula dashi?tausayinsa ya kamata take kalamansa na dazun suka dawo Mata ta runtse Ido hawaye na gangaro Mata tabbas bazata iya bijirewa faruk ba Amma shin wani Hali anuwar zai Shiga idan ta tafi?Saida tasamu lafiya Zata gujesa Shi a halin rashin lafiya?idan kuma taki bin faruk tayi masa babban butulci...ta fashe da kuka zatayi magana ya d'aga Mata hannu "nasan zakice daddy zaidawo kinbar gidan wanan ba matsala bace na Baki minti talatin ki shiryo ki fito INA kofar gida idan Baki fito ba kuma Zan tafi kuma kisani idan natafi bazan Kara waiwayarki ba"be Jira amsarta ba ya fice...ta fashe da kuka Mai ciwo ta jingina da jikin gado wasu hawaye masu zafi ne suke fita a idonta ta runtse idonta tausayin anuwar ya lullubeta ta yaya zatayiwa anuwar butulci?
Wasu takardu ta kalla a dakin ta zabura ta dauko da biro cikin sauri ta soma rubuta shot note a jiki tanayi hawaye na jika takardar haka tayi rubutu tsaf sanan ta ninke ta dafe kirjinta dake soka Mata bazata iya barin faruk ya tafiba idan ya tafi ya zatayi da soyayyarsa wadda ta Zama jinin dake yawo a jikinta?haka ta dauki kayan da anuwar ya Siya Mata ta fito dakyar ko ganin gabanta batayi cikin sauri ta nufi sashen anuwar ta zuge glass din window ta cilla masa farar takarda idonsa a rufe yayi saurin budewa takadda ya gani a kirjinsa ya kalli window cikin sauri yaga gilmawarta yayi murmushi Fatima ce...a hankali ya Shiga bude takardar,
Da afee taci Karo suka rungume juna suna kuka "anty Zahra yanzun tafiya zakiyi?"kuka sosai Fatima takeyi ta sharewa afee hawaye ta rungumeta a jikinta tana shassheka cikin sauri ta tuna da faruk na jiranta ta janye jikinta ta fice cikin sauri ta jikin mirror ya hangeta Yana ganinta ya sauke ajiyar zuciya yayi murmushi cikin zuciyarsa ya furta Ashe tana Sona?ya tada motar Yana jiran karasowarta.....
*Sako GA masoyana nasamu matsala da hannuna ne na goce yasa kukajini shiru....sanan masu mun barka na haihu ban rigada na haihuba kuyita mun addua da saura...INA kaunarku fisabilillahi*
*SLIMZY*❤️
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...