💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻♀️
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)**SLIMZY*✍🏻
_wattpadd@slimzy33_*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
Aunty Zahra tawa wanan page din naki ne @ *MOM* *AHLAN*....dikda inadan fushi Amma just for u dear I love you...❤️
*13*
Wata irin guguwa ce ke yawo dasu cikin sararin samaniya ga wata irin fuzga da iskar keyi hakan ya Kara bawa faruk Dakar Karanto dik adduar Data taho bakinsa.....cakkkkk yaji sun dira a Kasa jikin wani tankamemem gida hasken dake wajen yabashi Damar kalle kalle tabbas nan cikin gari ne....katse masa tunani tayi rikida tayi ta koma inuwa a gabansa "faruk da Fatima na cika Muku alkawari kamar yadda na dauka na taimakonku Ka kasance Mai taimako ga bil'adama hakan yasa naji inason taimaka muku Amma kuyi shiri sosai Dan fuskantar kalubale daga yuhana nabarku lafiya"....faruk ya bude Baki zaiyi Mata godiya Kenan ta bace....take hasken dake wajen ya rikide ya Zama duhu,
Jingina yayi da jikin gidan,gaba Daya jikinsa a sanyaye yake sai lokacin ya fahimci halin da Fatima take ciki,dago hannunta yayi ya saki yaga ya Fadi wata zabura yayi jikinsa na rawa "Fatima... Fatima....Fatima Dan Allah Kada ki mutu ki farfado gamu a cikin duniyar mutane mafarkin da kika Dade kinayi a rayuwarki....Fatima ki tashi"jikinta yayi dumi hawaye ne ya wanke fuskar faruk cike da takaici da kunar Rai ya dago ta,kansa ya dago Yana waige waige can ya hango wani famfo na bohole a kofar gidan ya kwasa cikin sauri turus yayi babu abinda zai dibo ruwan dashi nan ya Shiga waige waige....kawai ya yanke shawarar Tara hannunsa ya kunna ya ruga da sauri ya watsa Mata a fuska....ya kura Mata ido Yana ganinta ta hasken farin wata take motsa idonta tana sauke ajiyar zuciya....a hankali ta furta"farukkkk abbah na...inaso Inga abbah na yaushe zamu koma duniyar mutane?"
Iska Mai dadi ke Hurata yayinda faruk ya tsareta da ido cike da tausayawa tabbas Fatima ta Rasa ganinta gabaki Daya....da tana gani bazata tambayesa yaushe zasu koma duniyar mutane ba.....lumshe ido tayi iskar na ratsata tanajin wani dadi saidai wani irin faduwar gaba da takeji....Kiran sallah ne yasa tayi saurin bude manyan idanuwanta kamar tana gani....tace cikin rawar murya "fa....fa...rukkk kamar Kiran sallah nakeji...a ina muke?kodai aljanun ne suka musulunta suke Kiran sallah?"
Murmushin karfin Hali yayi "Fatima Allah ya kubutar Damu....yanzun haka muna cikin duniyar mu mundawo cikin duniyarmu Fatima saidai akwai duhu saboda Darene bansan a ina muke ba"yace cike da damuwa,
Dafe kirjinta tayi"alhamdulillah....Dan Allah Ka kaini GA abbah na in roki gafararsa"tace tana laluben Inda faruk yake,
A hankali mutane suka Fara fitowa saboda Kiran sallah ne na asuba wasu na tafiya masallaci a haka Inda suke jikin wanan gida har gari ya Fara wayewa hasken annuri da iska Mai dadi ta farkar da faruk daga Dan mafarkin da yakeyi ya Shiga dube dube jamaa nata yawo kasantuwar safiya ce....kallon katafaren gidan yayi ya Kara kallo cike da mamaki da al'amara...shiru yayi Yana nazari tabbas wanan gidan yasanshi Amma a INA?...wata zuciyar ta bashi amsa da a garin zazzau....ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Fatima Yadda ta kuje ta rame kasusuwan wuyanta dik a waje ya kalli gashin kanta da yayi dukun dukun kamar ta shekara bata wanke ba fuskar nan tayi duhu sai hancinta zur kyawunta na nan Yadda take ya tsallaka,
"Assalamu alaikum"yayiwa wani mutumi sallama....mutumin kallon faruk yakeyi Yana kallon kayan jikinsa....kamar mahaukaci haka yake kallonsa saidai GA kyau nan a tattare dashi tamkar balarabe a fuzge Yana kama da wani Dan sarki da yasani...ganin haka yasa faruk magana"bawan Allah niba mahaukaci bane Dan Allah ina tambayar nan din wani gari ne?"
"Zaria"ya basa amsa a takaice yayi masa godiya ya juya ya tsallaka mutumin ya bisa da kallo.....ya tabbata tunaninsa.....karasawa yayi Yana kallon gidan Yana jinjina kai...wanan gidan uncle dinsa ne tabbas gidan su Anuwar....Kenan aljanar gida ta kawosu?tunda nan din kamar gida ne Amma tayaya zai Fara introducing kansa a matsayinsa na faruk yarima?gabansa ya yanke ya Fadi ya kalli Fatima.....Anya bazai nemi taimako su ajiye masa Fatima ba bare da sunsan koshi din waye ba?daga Baya sai yazo ya dauki Fatima idan Komi ya daidaita?....Anuwar....zuciyarsa ta Kira masa tabbas yasan waye anuwar kuma Shi kadaine da namiji wajen mahaifinsa Wanda yake matukar ji dashi Yana gudun Kada anuwar ya bata rayuwar Fatima.....
********
Bacci sukeyi hankalinsu kwance daga Anuwar har gimbiya rumaisa.....wadda suka sha shaaninsu har wajen asuba suna manne da juna...a hankali rumaisa ta bude idonta ta saukesu Akan anuwar tana lumshe ido tana tuno Yadda ya sarrafata a Daren jiya Wanda ya gusar Mata da dik wata kishin ruwa da take ciki....da sauri ta Mike taja bargo ta rufe kirjinta tana dukan gefen pillow dinsa cikin Rada tace"Anuwar...Ka tashi safiya tayi Ka mance anan Ka kwana?at any moment faruk zai iya shigowa Ka tashi please Kada wadanan bayin magulmata su shigo"...bude idonsa yayi Yana gani dishi dishi....cikin sauri ya Mike ya zauna Yana kokarin tuno mafarkin da yayi a Daren jiya game da matarsa da zai aura....tabbas ya dace dik halin da yake ciki ya Shiga Zaria.....don anema masa yarinyar,Kallonsa rumaisa takeyi cike da shauki wani irin shaawarsa ke Kara fuzgarta ji takeyi kamar su cigaba...ya zuro kafafuwansa zai sauka daga gadon ta rukosa ya juyo Yana wurga Mata wani kallo da Tasha jinin jikinta....."Anuwar.... please kadawo"....
Kada Kai kawai yayi "naji"yace Yana saukowa daga gadon tabisa da kallo Anya Zata iya hakuri kuwa har Daren yau? gaskiya ah ah dole tasamo hanyar da zasu Kara kasancewa tare domin anuwar din jarumi ne shidin nadaban ne....idan haka ne meye matsalarta da faruk tunda dai ta rigada ta auresa?.....
********
Kuka sosai rabiah takeyi tana kallon gawar mahaifinsu Wanda tun asuba aka kawosa aka sanarwa makota da Yan uwansa rasuwarsa.....umman hawaye ne kawai ke gudu a fuskarta shikenan Wanda ya jajirce wajen Nemo Fatima ya kwanta dama gashi Fatima batada rabon neman gafarar mahaifinta ya mutu bata gansa ta roki gafararsa ba.....
Kanin mahaifinsu ne suka shigo da wasu Maza uku zasu dau gawar ya kalli rabiah yace "wai nikam kun Kira mutanen Libya ansanar Mata da mutuwar mahaifinta?"Duka Yan parlorn suka Kaso kunne dama kowa nason yaji labarin Inda Fatima take,
Rabiah batace komiba sai kuka da takeyi ummah ce tayi karfin Hali "zatazo...tasani"tace kowa ya Shiga kallon kowa....
Sunaji suna gani akayi gaba da gawar abbah....Wanda hakan yasa rabiah ta sume bata San Inda kanta yake ba,mutane ne suka ta akayi daki da ita.....
********
"Faruk...Ka gano Inda muke kuwa?"Fatima ta watso masa tambayar da ya farka daga tunanin mafitar da yakeyi gashi mutane sun fara taruwa ana kallonsu...."Fatima nan Inda muke gidan uncle Dina ne nayi shawarar ajiyeki anan batare da sunsan koni waye ba Zan tafi gidan aminina shikadai ne Zan tunkara a wanan lokacin ya saurareni Dan bansan badakalar da yuhana yayi a masarauta ba saboda ya rikida ya koma ni can basusan Bani bane Fatima kafin su yarda Dani zamu Shiga matsananciyar matsala""Innahlillahi wa innahilaihi rajiun"Fatima take Fadi hawaye na zurarowa a idanuwanta Kasa magana kawai tayi,
Cikin kuka tace "gashi Bana gani....Dan Allah faruk duk runtsi Kada karabu Dani kaji?"Yadda tayi maganar a raunane yasa zuciyarsa Karaya yaji kwalla ta kawo masa domin tabbas akwai badakala a gabansu....mikewa yayi ya kakkabe jikinsa ya tunkari gate din gidan zuciyarsa na harbawa....
******
A hankali rabiah ta bude idanuwanta ta bi dakin da kallo....hoton Fatima ta kalla wasu hawaye suka Shiga bulbulowa tausayin halin da Fatima ke ciki ya kamata....sauke idonta tayi gefen gadonsu idonsu ya hadu Dana Saddam....(yuhana)Yana zaune gefen gado a suffar Saddam da yazo musu,Yunkurawa tayi tana kokarin mikewa taga hawayen jini nabin fuskarsa cikin wata irin murya yace "nine nakashe mahaifinku....fansa ta farko Kenan Dana Fara dauka,sanan Zan dau fansa Akan kowa....ina Fatima take?"....yace Yana kallonta tsoro da furgici ta Shiga ta yaya zai tambayi Fatima bayan shine ya batar da Fatima?
Hannunsa ya d'aga Sama ya haska take yaga Fatima a tafin hannunsa.....saidai a kofar gidan da take wasu irin turaku ne yake gani Wanda aljanu bazasu iya shiga ba......kururuwa yayi hade da fadin "saina wahalar da rayuwarku tunda kuka kubuta a hannuna yanzun muka Fara Wasa daku"....batt ya bace,
Rabiah ta duro daga gado ta fito cikin furgici da tsoro jamaar parlorn suka tare ta.....
Anuwar na rike da hoton Fatima gabansa kayan breakfast ne Wanda aka Tara masa tunanin Inda zai ganta yakeyi....Anya zuciyarsa tayi masa adalci kuwa da kamuwa da soyayyar yarinya a hoto?... tayaya zai sameta....yake tambayar kansa tsaki yayi ya kifa hoton a gefensa Yana furzar da iska Mai zafin gaske......
A bangaren mama Fulani kuwa cike take da farin ciki domin an tabbatar matada anuwar ya kwana a sashen gimbiya don haka dik Yadda yakeso ya tafi gida bazata barsa ba....wayarta ta janyo tana laluben numbersa takirasa.....
Yanzun zaafara Wasa.....
SLIMZY❤️
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...