💥 *RUD'ANI...*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)*SLIMZY*
Wattpad@slimzy33*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*Mai bukatar a tallata masa hajarsa 07042277401*
*37*
💅🏻MMN MB HENNA💅🏻
💅🏻MMN MB HENNA💅🏻
Ina mata Yan qalisa
Uwar gida da Amarya harma da Yan mata shin
Kina bukata kayar lalle maroon masu kyau da inganci Wanda kowa yagani sai y yabba
Maza garzayo kisamu naki akan farashi mai sauki ga biyan buka
Muna bada sari ko sayen daya kofa abude take
Ga duk mai bukata
Muna aikawa kowane Gari cikin amincin Allah
*muna kwababben lalle maroon*
*muna Wanda zaki saya kije ki kwaba d kanki*
*munada Ruwan kwabin lalle maroon munada kayan hada ruwan kwabin lalle yyi maroon*
DOMIN KARIN BAYANI KI TUNTUBEMU TA WANAN NO: 🤳🏻*07068975608*
*MMN MB HENNA*💅🏻momy na sashen mai martaba mahaifiyar Anwar suna tattaunawa sukaji sallama a k'ofa,mai martaba yayi musu iso,
momyn Anwar na shigowa ta zube a k'asa cikin kuka ta soma magana "Ranka ya dade nasan kai adaline rayuwar Anwar tana cikin hatsari da garari likita ya tabbatar mana inhar baa bashi abinda yakeso ba to tabbas zamu iya rasashi yanzun haka da taimakon oxygen yake numfashi kasa baki faruk shine babba yayi hakuri ya barwa Anwar fatima"
shiru momyn faruk tayi take maganganun fatima suka fad'o mata a kunnuwanta tabbas yadda Anwar keson Fatima ya sadaukar da rayuwarsa akan fatima ya kamata ace Shi ta zaba ta aura musamman yadda yake cikin hatsari amma kuma kalaman fatima akan Anwar sun tabbatar da akwai wani abu game dashi wanda tasani yasa take wad'anan furucin,
gyaram murya mai martaba yayi "tabbas naso ace faruk zaiyi hakan amma yanzun haka walimar aurensu fulani ta shirya akeyi shiyasa kikaji gidan a hargitse,zanyi kokari wajen ganim faruk ya Amince idan be amince ba banida yadda zanyi wajen tursasashi akan hakan sanan yarinyar bata raayinsa,tabbas da Anwar zaiso Aysha y'ata da yau zaa d'aura masa aure da ita"shiru momyn Anwar tayi tana sauraren mai martaba bata taba tunanin zataji wanan kalaman daga garesa ba bayan ta sanar masa da halin da d'an nata yake ciki tabbas tunda tasamu wanan matar a tare dashi tasan bazata samu goyon baya ba,
share hawayenta tayi "Allah ya taimakeka zamu tafi bari inje kawai'cikin fushi ta mike dik yadda zatayi d'anta ya rayu zatayi wajen ganin ta kwato masa fatima kota halin yaya bazata zuba ido wajen ganinsa a kwance a nakashe ba bayan dik irin gudun mawar dayabawa fatima irin yadda ya saida rayuwarsa,
daddy dakyar ya yunkura yabi ta yasan fushi tayi babu inda ake haka tayaya zaa daura auren yaro da yar da yakeso ace ya saketa ya saketa?tayaya?
faruk ne yayi sallama cikin fadar yadau kwalliya sosai yayi masifar kyau mai martaba yayi murmushi ganin ya tsugunna nesa dashi "matso nan umar faruk zo mana?meke tafe dakai yasa baka tafi wajen taron ba?"
mama fulani ce tayi sallama ta shigo tayi ado da lemongreen din lafaya da golden hannuwanta da yatsunta sunsha zobunan zinari walkiya takeyi cikin zolaya mai martaba yace "uwar Amarya uwar Ango uwar taron gida ya na ganki a nan?"
murmushin kissa tayi ta kalli faruk "ranka ya dade ga uban taro a nan ana can wuri ya cika baki kowa shi yakeson gani ga jakadiyya can ta d'auko zahra da iyayenta suna wajen shi nazo tafiya dashi"
wani miyau faruk ya hadiya mai d'aci sam baiso fulani ta shigo ba amma tabbas baxai fita ba batare da ya fad'awa mai martaba abinda yake tafe dashi ba,
mai martaba ya jinjina kai had'e da murmushi yana jin dadin yadda fulani ke kulawa da faruk tun yana karami take tsananin sonsa dikda Allah bai bata haihuwa ba,"to kai kaji mamanka na jiranka gashi kamar naga akwai magana a bakinka"
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...