💥 *RUD'ANI...*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)*SLIMZY*
Wattpad@slimzy33*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*Mai bukatar a tallata masa hajarsa 07042277401*
*42*
shiru mai martaba yayi yana karewa Anwar kallo tausayin Anwar ya kamasa ganin yadda ya jike da gumi ga hawaye dake gudu a fuskarsa kamar an bude famfo "Anwar ka kwantar da hankalinka nasan bazaka taba aikata abinda rumaisa tace ka aikata ba nasan bakai bane itama zata fad'i gaskiya da zarar taji matsa karka jefa kanka cikin wanan masifar kaji?"
girgiza kai Anwar yayi cikin kuka yake kallon mahaifiyarsa wadda kallo daya zakayi mata kagane a fusace take ya juya ya kalli daddynsa wanda yana kallon tashin hankali a kwayar idonsa yana matukar tausayin daddynsa mai kaunarsa mai son farin cikinsa gashi ya jefasa cikin rudani da tashin hankali sakamakon son zuciya da kururuwar shedan ya aikata zina da matar dan uwansa daga karshe ga abinda ya haifar,
"Mai martaba ina neman agajin sarki ina neman afuwarka akan"ya rushe da kuka momynsa ta Shiga girgizasa jikinta na rawa "Anwar kasan mai kakeso ka fada kuwa?Anwar karka amsa abinda ba kai bane ka aikata zan iya hadiyar zuciya na mutu idan ka tabbatar da cewa kaine kayi zina da matar aure matar d'an uwanka mai kakeso ka fada"a rude take maganar tana girgiza anwar wanda jijiyoyin kansa sunyi rud'u rud'u,
daddy ya karaso ya rukota "Haba momyn yara menene haka?ki kwantar da hankalinki kinsan d'anki bazai taba aikata abinda ake zarginsa dashiba kinji?calmdown muji mai zai fada nasan zai karyata wanan zargin da akeyi masa"
Anwar ya kalli daddynsa tausayinsa ya kamasa ya rarrafa ya ruko kafar daddy cikin kuka yace "Daddy ka gafarceni ka yafemun idan nayi karya ma asirina zai tonu amma tabbas nine nayi zina da Rumaisa sau daya tak na....."bai karasa ba yaji saukar mari a kuncinsa ya dafe ya sakejin wani saukat marin a kumatunsa,
momynsa zaman yan bori tari cukin gunjin kuka take kallon Anwar tana nunasa da yatsa bakinta na makyarkyata "Anwar ka cuceni ka cuci rayuwata ka bata mana suna ka cuci rayuwar kanka da kanka Anwar ka tabbatarwa da duniya kaidin kwartom matar dan uwanka ce"
kuka sosai momy keyi tana girgiza kai tabbas biri yayi kama da mutum ta yarda da wanan zancen,take ta tuno da ranan da sukazo barka yadda suka samu Anwar a sashen Rumaisa tamkar cikin tashin hankali suke,da ranan da ya bankado labulen dakin rumaisa da irin kallon da yakeyi mata ya tabbatar matada gaskiyar lamari Anwar shine yayiwa rumaisa ciki matar yarima faruk....gumi ne ya karyo mata ta daga kai ta jefesa da wani mugun kallo mai cike da takaici,
daddy gefe guda ya koma ya jingina da jikin bango yanajin yadda zuciyarsa ke bugawa tamkar zata fasa kirjinsa ta fito ya dafe kirjinsa gefe daya ya kalli momy a fusace "ki fito mutafi.....kai kuma ka nemi wani uban bani ba,idan hat zaki daukesa a matsayin d'anki to kifadamun na sauwake miki"yana gama maganar ya fice,
jikin momy yayi sanyi ko ganin Anwar batasonyi haka tana kuka ta fito mai martaba nayi Mata magana ko kallonsa batayi ba tabi umarnin daddynsa a kofar fita sukai karo da momyn faruk ta rukota cikin tsoro da furgici tace
"lafiya?meya faru?ina zaki cikin wanan halin?"
share hawayenta kawai tayi ta girgiza mata kai ta fice ciki. tashin hankali ta shigo fadar Anwar na durkushe ya fita hayyacinsa momy ta rukosa ta rungumosa
"lafiya ranka ya dade maike faruwa?"
girgiza mata kai mai martaba yayi cikin tsananin damuwa yayi gyaran murya yacev"ya tabbata Anwaru shine yayiwa rumaisa ciki"
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...