23

148 21 8
                                    

💥 *RUD'ANI....*🤦🏻‍♀️

        *FREE BOOK*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers*)

                  *SLIMZY*✍🏻
          Wattpad@slimzy33

*SADAUKARWA:* *FATY DANMALIKI*

*ASSALAMU ALAIKUM*
*Fatan Alheri ga daukacin masoyana makaranta littafaina da ma wadanda basa karantawa hakika kaunar da kuka nunamin mutanen Whatsapp Facebook da wattpad banida bakin da Zan gode muku nagode sosai wadanda suka kirani sukaimun barkar haihuwa da wadanda suka turomin sakwanni nagode Allah ya saka da alheri ya bar kauna da zumunci fatan Alheri gareku AYSHATY HOME OF FRAMES da AISHA USMAN da sauran wadanda suka halarci bikin radin suna nagode sosai Allah yasaka da alheri*... *BARKANMU DA DAWOWA ZAMU DORA DAGA INDA MUKA TSAYA DAUKEWAR NETWORK YASA TUN TUNI BAN CIGABA BA NAGODE* *SLIMZY*( *MOM MUBEENAH*)

                          *23*
Jiki a sanyaye ta bude motar ta Shiga fuskarta sharkaf da hawaye Anya tayiwa anuwar adalci?yanzun tafiya zatayi tabarshi a cikin halin rashin lafiya bayan tanada tabbas Akan cewar wanan ciwon da yakeyi yuhana ne domin dik Wanda yayi silar warkewarta daga makanta dama haka Zata samesa,yanzun idan ta tafi ya zaiyi tana matukar Jin tausayinsa saidai kuma bazata iya bijirewa umarnin faruk na barin ta gidan ba domin faruk shine ruhin ta idan har ta bijire masa a Karo na biyu to ta tabbata butulu,tayi nisa cikin duniyar tunani ta tsinkayi muryarsa"idan kin zabi zamanki a wanan gidan kina fuskantar kaskanci to tabbas Zan maidaki kuma Zan hakura da soyayyar da nake Miki Zan barki da anuwar Dan shima jinina ne"

Share hawayenta tayi ta Shiga girgiza Kai cike da tashin hankali ta kakalo murmushi ta rausayar da kanta ta kashe masa Ido cike da karfin Hali"haba tayaya Zan zabi Zama a wanan gidan bayan Kaine Ka ajiyeni a gidan ni ajiyarka ce yau kuma kazo daukar ajiyarka sai in gagara binka?Akan me bayan yau inajin farin ciki Wanda rabon da injisa na mance hakan yau zanyi Ido hudu da mahaifiyata da yar uwata saidai bansan Yadda zasu karbeniba domin nice silar mutuwar mahaifina Wanda na tabbatar da bakin cikina ya mutu a Ransa"hawaye ya Kara wanke Mata fuska muryarta na rawa ta karashe maganar,
Tausayinta ya lullube faruk shima kwalla ce ta ciko a idonsa take ya maida kansa gefe ya cigaba da tuki batare da yace Komi ba....


Anuwar kuwa bayan ya Gama karanta shot note din Fatima wani Abu ne ya tokare masa zuciya saidai farin cikinsa Daya adreshin ta data rubuta masa a Kasan wasikarta gumi ne ya karyo masa shikenan Fatima ta tafi yafiso ya kasance waje Daya da ita yanaso Daya shigo gidansu yayi tozali da fararen idonta masu digon zaiba....momy ce ta shigo hade da sallama da waya a hannunta tana masifa "yanzun Kenan faruku ya dauki waccan kayar bushiyar ya tafi da ita?ya Zama dole in Kira masarauta in sanarwa da Mai martaba da mahaifiyarsa abinda ke tafiya bazai yuwu wanan aljanar yarinyar ta juya mana Kan Yara ba Shi kuma meye nasa daga zuwa ya tarar da wanan rikicin?"

Meeniosky tayi murmushi "momy da nasa mana domin inada tabbacin shine yayi batda kama ya kawota ajiya batare da saninku ba kamar Yadda yakeyi Mata batda kama lokacin da yazo Mata a talaka ta wulakanta sa lokacin tana teemah dollar"....zaro Ido momy tayi cike da tashin hankali "aiko bazata sabu ba wankan kuturu da sabulu yanzun Zan Kira iyayensa"

Ajiyar zuciya meeniosky tayi a zuciyarta take magana burina ya cika bazai yuwu kizo kitafi da zuciyar anuwar ba sanan kije kiji dadin rayuwa a masarauta ba da Dan sarki yareemah ba dik wata hanya da zaki farin ciki dollar saina tosheta"

Dakyar anuwar ya yunkura ya mike da sauri meeniosky ta karasa Zata taimaka masa ya d'aga Mata hannu hade da wani kallo Mai cike da tsana a tsorace taja Baya ya dubi momy Ido cikin Ido tanata waya da masarauta harta gama ta juyo garesa "momy"ya Kira sunanta a raunane

Dakyar ta hadiyi miyau ta amsa masa tana kallonsa cike da tsoro gaba Daya yanayinsa ya sauya take tausayinsa ya kamata "momy abinda kikayi yanzun ya dace Kenan?shin kina tunanin cewar Zan iya rayuwa batare da Fatima bane?to momy inaso kisani Fatima da tabar gidan nan itace haske a duniyata tamkar Rana take wadda ke haskamun duniyata idan har babu ita duniyata zatayi duhu Wanda ke kanki sai kinyi danasanin barinta gidan nan inaso kisani Fatima ruhina ce Fatima alheri ce ga rayuwar danki dake kanki"

"Anuwar kasan me kake fada kuwa?tsintacciyar magen kake Kira alheri ga rayuwarki?"

"Tabbas domin itace silar shiriyata Fatima itace silar barin dik wani mummunan Hali nawa da kikasani kuma inaso in sanar Miki Fatima yar gatace kuma yace GA kowa kuma abarso ce ga kowani namiji inaso kisani rashin Fatima barazana ce ga rayuwata matukar bansameta ba to zaki Rasa danki Daya tilo"Yana cikin maganar ya sarke numfashinsa ya Shiga Sama da kasa cikin kanknin lokaci idanuwansa na Shirin kafewa cikin tsoro da tashin hankali momy ta soma magana "anuwar Ka tashi na yarje maka soyayya da Fatima da in rasaka gara Ka aurota Ka kawota dik kiyayyar da nakeyi mata kuwa"

Jin haka yasa meeniosky taja da Baya gabanta na tsananin faduwa tana kallon momy dake tallabe da anuwar a rude....daddy ne ya Karasa shigowa wanda yake sauraren Komi ya harde hannuwansa a kirjinsa "da kinbarsa ya mutu AI tunda har yanzun halinki na kyamar talaka Yana nan a jinin jikinki kisani idan narasa dana I will hold you responsible"ya juya ya fice..... meeniosky zubewa tayi a kasan carpet kafafuwanta sun Kasa daukarta....

*******
A kofar gidansu yayi parking motar tana bin ko INA da kallo babu abinda ya canja sai Yan gyare gyare da akayiwa wasu gidaje ta kalli jikin bishiyar gidansu ta juyo ta kalli faruk Wanda ya kashe Mata ido Yana murmushi yace "kina tuna wajen tsayuwata ko?"lumshe Ido tayi wasu hawaye masu zafi na bin fuskarta kafin Tayi magana Kira ya shigo wayarsa dake ajiye a gaban motar sunan Mai Kiran yasa dukkansu gabansu ya Fadi ya dubeta"Mai martaba ke kirana"wani Abu ne taji ya soketa cike da tsoro da fargaba tace "dauka kaji"...dauka yayi cikin rashin saa hannunsa ya Danna hands free

"Assalamu alaikum ranka ya dade Baba barka da rana"

  "Umar faruk dik Inda kake ina bukatarka a gida yanzun kuma a Inda kaken tare da yarinyar daka dauko Ka ajiyeta a wajen da kuke koda a dokar daji kuke kuwa umarni ne wanan na Baka kuma banaso komi kace Mata kazo ina son ganinka yanzun ina tare da mahaifiyarka da Fulani da matarka rumaisa"wayar ce ta katse shedar Mai martaba ya katse wayar,

Ya kalli Fatima wadda idonta ke kansa zaiyi magana ta daga masa hannu "karkace Komi faruk kabi umarnin mahaifinka kawai alhamdulillah tunda burinka ya cika Ka kawoni gidan mu magana da mamana ne bakasamu dama ba to Zan Shiga gida kaje kaji Kiran da akeyi maka Allah yasa Ka dawo gareni"tace tana bude mota hade da daukar yar jakar kayanta ta fice tana hawaye....kwantar da kansa yayi a jikin kujera Yana sauke numfashi tabbas babansa yaji labari Kenan daga gidan su anuwar aka sanar masa?idan haka ne yanada tashi dabarar domin lokaci yayi da zaa daina hadasa da mahaifinsa a fusace yayiwa motar key ya bar kofar gidan.

Tsaye take a kofar parlor tana sauraren hiran ummanta da kanwarta rabiah tana kuma iya hangosa..."haka kawai nakeji tamkar nakusa hada Ido da yarki Fatima tun wayewar garin yau nakejin nishadi hade da faduwar gaba"

"Ummah nikaina ina yawan yin mafarki da yaya faty kuma inasa ran Zata dawo garemu nan bada dadewa ba mucigaba da addua da sallahr Daren da mukeyi addua bata faduwa Kasa banza"

Murmushin farin ciki Fatima tayi hade da yaye labulen parlorn dukkansu suka kalleta tsaye kallon juna ummah da rabiah sukayi ummah tace "kinga maganar da mukeyi ta Fatima tasa yanzun haka gizo takeyimun a gabana"

  "Nima ummah yaya faty nake gani a gabana tanamun gizo"

Lumshe Ido Fatima tayi ta karasa aguje tafada jikin ummah tana fadin "ba gizo bane ummah nice nice yarki Fatima"

Hannu ummah tasa Yana rawa takai fuskar Fatima tana shafawa gani takeyi tamkar gizo Fatima keyi Mata ta tabo fuskarta taji Itance nan take ta rungume Fatima ta fashe da kuka rabiah ta matsa ta fada jikinsu suka rungume juna suna kukan farin ciki.....



*Mom mubeenah*✍🏻

RUD'ANIWhere stories live. Discover now