5

271 28 3
                                    

💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻‍♀️

  *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)*

                   *SLIMZY*✍🏻
       _wattpadd@slimzy33_

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

*SAKON TAAZIYYA GAREKI MAI DAMBU ALLAH YA JIKAN MAHAIFINKI YA GAFARTA MASA MARUBUCIYAR ZANEN KADDARATA*

                       *5*

Faruk na kwance a Kasa sumamme Saddam ya bayyana a cikin suffarsa ta tsohon aljani Yana kallonsa Yana girgiza Kai "banason in cutar dakai yaro ba Kai nakeda niyyar cutarwa ba Fatima nakeso in koyawa hankali in nakasa rayuwarta daga karshe in rabata da Rai Amma kana kokarin shigowa gonata.....Ka fita aniyata!!!Ka fita a wanan lamarin Kada kace zakayimun shisshigi idan kayimun shisshigi zaka dandana azabar yuhana"ya karasa maganar Yana daga murya wuta na fitowa daga cikin bakinsa idanuwansa jini na zubowa.....haske ne ya kauraye wajen Daya dumfari faruk dake kwance sai yaga wuta sai ya dawo....ya d'aga Kai ya fasa wata k'ara ya bace....

Karar da Saddam yayi ce yasa faruk zabura daga yar sumar da yayi ya Shiga waige waige cike da tsoro,ya laluba aljihun rigarsa ya zaro wayarsa karfe goma na dare?shin bacci yayi ko Suma yayi a kofar gidan?...cikin sauri tayi dialing number Yana waige waige......drivernsa ya Kira Yana Saman layinsu Inda ya Saba parking mota ya jirasa har bacci ya soma daukarsa yayi furgigit "ranka ya dade"yace cikin wata iriyar murya Mai kamada bacci,

"Saeed kana ina?"

"Ranka ya dade ina Inda nasaba tsayawa "is ok ganinan"yace ya datse wayar Yana kalle kalle kofar gidan su Fatima ya dade Yana kallon kofar gidan cike da tashin hankali ya furta "yanzun aljani zaki aura Fatima?"ya girgiza Kai "bazan taba barinki kisha wahala ba dikda bakisona"....dakyar yake taka kafafuwansa da sukayi masa nauyi yabar wajen,

Abbahn Fatima tagumi yayi a parlor kamannin Saddam ke yawo a idanuwansa tabbas wanan yaron akwai wani bakon lamari a tattare dashi kamanninsa da zatinsa da yanayinsa tamkar ba bil'adama ba?a haka Fatima keson aurensa?yake tambayar kansa,

Ummah ce tsaye tana karewa mijin nata kallo ta zauna gefensa"yadai Malam naganka cikin wanan yanayin?meke faruwa ne?Dan Allah Ka yafewa Fatima"

"Ba maganar yafewa Fatima bace,abinda ta zaba Shi zatayi AI banikeda rayuwarta ba nine na haifeta dai Amma banina hura Mata Raiba nawa inbata tarbiyya nayi kokari Amma Fatima ta gagara....ta zabawq kanta rayuwar karya da son duniya don haka ba abinda zance,saidai inajin tsoron wanan yaron da ta dage Akan saita auresa...gaba dayansa bayamun kamanni da mutane tamkar aljani"

Zaro ido ummah tayi tsoro ya kamata cikin tashin hankali tace "aljani kuma?"ta dafe kirji "kwarai aljani"

Abbah ya Mike "idan ma BA mutum ta kwasoba sai su karata can"ya Barta wajen zaune,

Ummah tsoro ya cikata taga parlorn na juya Mata ta Mike cikin sauri har tana cin tuntube tabi bayan abbah...

*******
Faruk durkushe gaban mahaifinsa karfe sha Daya na dare,

"Faruk Baka isa Ka janyo mana masifa ba muna zaune,mahaifiyarka ta sameni da wani lamari Akan wata yarinya wadda Ka bata labari da kanka don haka ban amince ba"

Da sauri faruk ya kalli Mai martaba"Daddy...Baka.."

Mai martaba ya daka masa tsawa "ban amince ba idan Ka sake kusantar Inda yarinyar take ma naji labari sai nayi mummunan Saba maka,Dan haka kasani nida hakimi mun tattauna dazu nayi shawarar jibi zaa daura aurenka da rumaisa yar sarkin Rano"

Gumi ne ya wanke fuskar faruk har Yana diga,tabdijan yarinyar da Bai tabajin digon Sonta a zuciyarsa ba?"

********
  Washe gari....

RUD'ANIWhere stories live. Discover now