💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻♀️
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)**FREE BOOK*
*SLIMZY*✍🏻
_wattpadd@slimzy33_*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*17*
Dukkansu kallonta sukeyi ko wanne zuciyarsa na dukan uku uku musamman afee wadda take a tsorace....Fatima tasoma magana hawaye ya gangaro Mata "ba kowa bane yuhana face bakin aljani Wanda ya fito a suffar mutane ya aureni a suna Saddam....Wanda yanzun haka akwai igiyoyim aurensa akaina Wanda sau Daya takkk ya sadu Dani a duniyarsu ta aljanu Wanda mukaje mukai rayuwa a can....Wanda a yanzun haka shine sanadiyyar ciwon idanuna maana wanan makanta da nake dauke da ita shine sila"....ta fashe da kuka Mai ban tausayi jikin afnan kyarma ya shigayi wadda kalaman Fatima data Basu a dunkule suka daure Mata Kai,
Anuwar kuwa ko gezau beyiba sai tsananin tausayinta dayake ratsa sassan jikinsa hade da kaunarta data Zama bargo ta lullubesa....ya kalli afee ya kifta Mata ido alamar tayi magana,...bakinta na rawa tace "yaya Zahra meye sanadin da kika auri aljani?shin da saninki kika aurenshi Koko bada saninki ba sanan taya hakan ya faru?"
Share hawayenta tayi "ta dalilin wulakanta almajiri da nayi a kofar makarantarmu ba tare da sanin cewar aljani bane....hakan ne dalilin fadawata cikin RUD'ANI"...nan ta kwashe Komi ta fada musu kaf tun daga farko har karshe har zuwanta gidan.....
Gumi ne kawai ke karyowa anuwar cikin tashin hankali baisan lokacin dayace a fili ba "Insha Allah nine Zan Zama sanadiyyar warakar ciwonki dikda yace babu Wanda zai magance Miki wanan matsalar koda Zan Rasa Raina Zan Nemo miki magani"..yace Yana kallon afee wadda kuka takeyi sosai tana kallon Fatima ta ruko hannunta "yaya faty.....Dan Allah ki zauna a nan Damu kinji?"
Girgiza Kai tayi "da zarar Dan uwana ya dawo Zan tafi zantafi in roki gafarar mahaifina da yar uwata rabiatu domin sun kaunace ni suna kokarin nunamun hanyar Dana dauka bame bullewa bace Amma na rufe ido na inaso inyi tozali da mahaifina koda bazan gansa ba"..tace tana kuka,
Anuwar yayi gyaran murya "afnan inaso wanan maganar ta Zama sirri karki kuskura momy taji matsalarta domin inhar taji matsalarta to tabbas Zata koreta"
Afee ta gyada masa Kai ana kiraye kirayen sallahr magriba ta Mike "Zan tafi inyi sallah bazan dawo ba sai anyi isha'i Zan dawo ki Kula da ita"Yana Gama fadin haka ya fice,
Wata ajiyar zuciya Fatima ta sauke..samm tanaji a jikinta zaman gidan nan akwai wani RUD'ANI a cikinsa Dan haka tilas ta fice tabar gidan...take zuciyarta ta tuno Mata idan kintafi faruk dinki ya dawo fa?ta lumshe idanuwa....
********
Kuka sosai faruk yakeyi a sashensa bayan ya dawo daga gidansu Fatima Yana kwance a Kan gadonsa tayaya zai Shiga gidan nan don ganin Fatima ya sanar Mata da mahaifinta ya rasu?tambayar da yakeyi wa kansa Kenan ya Zama dole dik yakin da zai fuskanta ya jajirce tunda har ya iya shigowa gidan nasu....da wanan tunanin yayi shiru a kwance ba bacci yakeyi ba,Kanwarsa ce ta turo kofa hade da sallama...da sauri ya bude ido Yana kallonta itama Shi take kallo tace "ya faruk ko kowa Bai yarda dakaiba Nina yarda dakai domin nadade da Jin wani yanayi a jikina dik lokacin da wanan Mai suffar taka yazo garemu sai naji wanan abun wallahi na gasgata Ka"tace tana kuka,
Wani farin ciki ne ya lullube faruk domin samun ta a tare dashi babban makami ne kanwarsa Allah yayi Mata wani Tarin baiwa Wanda ba kowa yasan hakan ba ta hanyarta zaisamu yaje GA Fatima gobe,
Hannu ya Mika Mata ta tako tazo ta rike hannunsa gam,wasu hawaye ne suka cicciko a idanuwansu Duka su biyun a raunane faruk yace "Dan Allah ki taimakeni momy ta daina fushi Dani inason momyna.....Dan Allah ki agazamun Mai martaba ya warware aurena da rumaisa'
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...