💥 *RUD'ANI....*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers*)*SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33*SADAUKARWA:* *FATY DANMALIKI*
*KAMAR YADDA NAYI ALKAWARI ZAN CIGABA DA POSTING 3RD DECEMBER INSHA ALLAH GASHI NAFARA BAYAN DAUKEWAR HANYAR SADARWA DA MUKAYI NA WASU WATANNI YANZUN ZAMU D'ORA*
*25*
Anuwar kuwa tsare Fatima yayi da wani Mayen kallo Wanda hakan yasa tsigar jikinta taji Yana tashi saurin ambaton Allah tayi kafin ta nisa ta dubeshi cike da dimaucewa "yaya anuwar Mai ya fito dakai a wanan lokacin bayan bakada isasshiyar lafiya?sanan Ka tako kazo Inda nake batare da izinin mahaifanka ba,na tabbatar momy ta datse alaka tsakanina dakai dikda dama babu wani Abu Wanda ya wuce karamci da mutunci a tsakaninmu meyasa bazakayiwa mahaifiyarka biyayya ba kayi abinda takeso?kadaiga abinda ya sameni sakamakon bijirewa iyayena da nayi na fada mummunan halaka Wanda Allah ne kadai ya kubutar Dani"kanta w sunkuye take maganar,shikuwa kallon labbanta yakeyi Yadda take motsasu tana magana ba karamin Burgesa tayi ba yanajin wata sabuwar kaunarta na keta bargo da jijiyoyin da jini ke yawo a jikinsa,harta gama magana baisaniba yayi nisa wajen kallonta da shaukin soyayyarta,
Jin shiru yasa Fatima dago kanta idanuwanta da nasa suka hadu tayi saurin kauda Kai tadan bubbuga jikin kujerarsa firgigit yayi sai lokacin yayi ajiyar zuciya kafin daga bisani yace "Fatima momy ta yarjemun inzo in nemi aurenki hakan yasa nazo da bukatata inaso ki amsamun tambayata shin kina Sona?zaki aureni?".....ya tsareta da mayun idanuwansa farare Tass da kyakkyawar doguwar fuskarsa wadda tadan rame kadan,
Wani jiri ne taji Yana dibarta lallai wani irin faduwar gaba taji lokaci Daya ta yaya zai Mata wanan tambayar bayan yasan cewan faruk shine Wanda yakesonta sukeson juna sukeda burin aure?.... innahlillahi wa innahilaihi rajiun shine abinda zuciyarta ke maimaitawa wace amsa ta dace tabawa anuwar?shin idan tace bata sonsa a halin rashin lafiyar dayake ciki ta dalilin warkar da ita da yayi wani Hali zai Shiga?amsa dayace Zata bashi itace tana sonsa soyayya ta Yan uwantaka bata aure ba,
"Ina sauraronki Zahra.....ki sanar Dani amsar tambayata domin sati Daya kacal yayi yawa zamuyi aure"
.zaro Ido tayi cike da fargaba haka kawai takeji a jikinta faruk zai iya zuwa koda wani lokaci ya dace ta sallamesa ta bashi amsa kobata Kai zuciyarta ba,"Ina sonka....a..."bata karasa ba wayar dake hannunta ta Shiga ruri cikin sauri ta duba faruk ne gabanta ya Fadi ta kalli anuwar sanan ta dubi wayar Tata shiko ya cika da tsananin farin ciki dikda ya fahimci ba ina sonka kadai takeso tace ba Kiran wayar ne ya katse Mata hanzari cikin in ina tace tana kokarin bude motar "am...amm.in ummah na kirana sai anjima sai wani lokaci"ta fito abinta jikinta na rawa Sam batason bacin ran faruk Dan tabbas idan yazo yaga anuwar yasan cewar itace tayi masa kwatance har yazo me zai dauka?bayan ita kuma tausayinsa yasa ta bashi a rubuce....
Shafa sumar kansa yayi yabi bayanta da kallo Yana murmushin cike yake da tsananin farin ciki yau din nan zai sanarwa da abbah maganar soyayyarsa da Fatima tana sonsa ya buga mota yabar kofar gidan.....
Fatima kuwa tana saka kafa cikin parlorn gidan taji wani jiri na neman daukarta tunawa da tayi da amsar data bawa anuwar ta zaro Ido cike da tsoro daga rabiah har umma kallonta suke fuskokinsu dauke da tambayoyi.....
Kujera ta nema ta zauna jagwab ta dafe kanta sai lokacin ta tuna da faruk ya kirata wayarsa harta katse ya dace tasake kiransa....
********
A kofar masarauta anuwar ya Parker motarsa ya dace ya biya ya Kai gaisuwa wajen Mai martaba da ahalin gidan sarki daidai kofar Shiga sukai Karo da faruk kallon juna sukayi faruk fuskarsa a daure Yana ganinsa yaji wani kishi ya taso masa ya tokare masa kirji Shi kuwa anuwar farin cikin dayake ciki yasa yadanyi murmushi ya Mika masa hannu alamar su gaisa,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...