💥 *RUD'ANI...*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)*SLIMZY*
Wattpad@slimzy33*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*Mai bukatar a tallata masa hajarsa 07042277401*
*41*
dakyar Rumaisa ta saita natsuwarta cikin karayar zuciya take kallon fatima wadda itama ita take kallo,
"ki fadamun gaskiyar lamarin nan kafin ki kwana a ciki dan kema kinsan nasan gaskiya ko kin manta?"nan fatima ta tuno mata ranan da rumaisa da Anwar sukai musayar miyau a gabanta a tunaninsu batada hankali,
"tou in baki fadamun ba nima shaidace akan wanan lamarin dan haka zan samu mai martaba na sanar masa da yardarki Anwar yayi lalata dake akan gadonki ba Sunnah"
girgiza kai rumaisa tayi "Tabbas Anwar yayi lalata dani da yardata amma da gudun mawar mama fulani wadda itace tasani haka a lokacinda banasamub lokacin faruk fatima mukai yarjejeniyq akan zanyi ciki zai zama na faruk zan kuma taimaka mata mu kashe faruk,ni kuma nagagara hakan saboda ina sonsa yanzun ma tacemun inhar na shirya fita daga wanan masifar to nazo tanada shawarar da zata bani idan naki Kuma kada nakira sunanta karna kuskura nabtona mata asiri dan nice zan kwana a ciki"
jikin fatima ya soma rawa gabanta ya yanke ya fadi ta dafe kirjinta da zuciyarta keyi kamar ta fasa kirjinta ta fito lallai mama fulani makira ce idan haka ne cikin sauki zan tona mata asiri kenan?dakyar fatima ta saita natsuwarta ta fuskanci rumaisa wadda hawaye yaki daina zuba daga idanuwanta,
"zan taimakeki amma wanan ya zama tsakanina dake sanan karkibkuskura ki sanar mata da hakan"rumaisa ta jinjina kai ta hadiyi wani miyau mai d'aci cike da damuwa tace,
"bazaki bari faruk ya sakeniba ko?fatima ki taimakeni nasan kece hasken idaniyarsa kece a cikin zuciyarsa ki tallafamun faruk ya soni koda bai kai son da yakeyi miki ba ina sonsa ina tsananin kaunarsa fatima"wani abu fatima taji ya caki zucuyarta kishi nan da nan ya taso mata da badan tana neman yadda zaayi tavtarwatsa lamarin fulani ba da babu abinda zai sa ta zauna tarw da rumaisa harta fada mata tana son mijinta mijinda take tsananin kauna da kishinasa,
"shikenan yanzun inada abinda zan baki kije dashi wajen fulani da zarar kinje dashi zanji komi sanan nasan yadda zan bullowa lamarin kuma zan lallabi faruk ya zauna dake"take rumaisa ta rungume fatima cikin farin ciji fatima murmushin k'eta tayi dikda wani sashe na zucuyarta na tausayin rumaisa musamman yadda ta fita hayyacinta ga jego ga karamar yarinya kada ma tazo jininta ya hau,
ta janye jikinta ta mike "idan kin tashi tafiya kisanar mun abinda zanyi a shirye yake ke kadaice kawai nake jira"rumaisa ta jinjina kai tayiwa fatima murmushi wanda kana gani kasan na karfin Haline a sanyaye tace,
"Nagode"fatima ta wuce yana sak'e sak'e cikin zuciyarta a kwayar idon rumaisa ta hango gaskiyar lamarin bata goyon baya dari bisa dari amma dole zatai nata takun domin kada su hada kai su rufta da ita, murmushi fatima tayi tunowa da ta mannawa rumaisa recorder lokacin data rungumeta koda taci Amanarta ta tabbatar Daga abinda zatasa a kunnenta wanda rabia ta kawo mata zata juyo komi dangane da tattaunawarsu,
fatima ko ganin gabanta batayi kamar daga sama taga mutum a gabanta tayi saurin d'agowa gabanta ya yanke ya fad'i ganin Anwar a gabanta da irin kallon da yakeyi mata ko kifta ido bayayi ya lumshe idonsa ya bude tayi masifar kyau dan kwanakin da bai gantaba ta sauya kyawunta ya kara fitowa gashi sarautar kanta tayi mata kyau,irin ramar da Anwar yayi saida fatima taji ya bata tausayi ya same sosai yayi fari kal sai kashin hanci,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...