6

227 24 0
                                    

💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻‍♀️

  *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)*

                   *SLIMZY*✍🏻
       _wattpadd@slimzy33_

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

*Jinjina ta musamman gareki MOM AHLAN Akan littafinki na AZIMA Da AZIZA more grace to your shining elbow....nemi AZIMA da AZIZA idan Baki karantaba ki soma kiji madarar basira*

                     *6*

Fatima murza idonta takeyi tana kallonsa da kayan jikinsa ta juya ta dubi dandazon taron daurin auren ta rufe idanuwanta a fili take furta "Allah ka farkar Dani daga wanan mummunan mafarkin....idan har mafarki nakeyi bazan sake kwanciya bacci ba harabada"...ta bude idanuwanta da wasu hawaye masu zafi suke sauka....hada ido tayi da Saddam idonsa na hawayen jini...take ta kwalla Kara hankalin jamaar dake wajen ya dawo kanta kallon kallo akeyi yayinda waliyin Saddam da waliyin Fatima tuni sun shafa adduar daura aure....

Faruk ya iso wajen cikin tashin hankali suna had'a ido da Maroki ya zube a Kasa a gaban faruk..."kaga Dan sarki jikan sarki yarima Mai jiran gado yariman sarki Mai adalci Wanda daurin aurensa be hanasa zuwa daura auren talakawan gari ba"...numfashi yaja ya sauke,

Ya maida dubansa GA Saddam Wanda yayi girgiza ya rikida a idon Fatima da faruk ya koma tsohon almajirinsa ya d'aga kansa Sama ya feso wani Abu Mai ruwan ganye ya fesawa faruk Wanda take harshensa ya daure ya kuma kasa motsawa daga wajen,

Jamaar daura auren nan sai mamakin ganin yarima faruk sukeyi shiko mahaifin Fatima kansa ne ya daure ya dubi wani mutumi dake tsaye yace "dagaske wanan dan saurayin Dan sarki ne?"

"Kwarai mahaifinsa shine sarki abdulmalik dan abdulazeez tsohon sarkin zazzau"...gumi ne ya jika fuskar abbah,

Saddam kuwa gaisawa ya shigayi da mutane cikin suffarsa ta kyakkyawan saurayi sai walkiya yakeyi tamkar balarabe....abbah ya rike hannun Fatima ya nufi cikin gida da ita Inda mutanen waje aka fara gabatar da walima.....

Faruk wayarsa taki daina ringing Sam bazai iyasa hannunsa a aljihunsa ba domin jikinsa a daskare yake,dakyar cikin zuciyarsa yake karanto ayatulkursiyyu...nan ya farajin jikinsa Yana warwarewa....yasa hannu ya Ciro wayarsa Mai martaba ne....wani faduwar gaba ya darsu a kirjinsa jikinsa ya soma tsuma....

Bai daukaba ya Mike hanyar barin layin Amma abun mamaki da yayi tafiya Daya biyu sai yaga Saddam a gabansa da bakaken Kaya cikin wata irin mummunar halitta idanuwansa jajir manya manya sun sauko kamar zasu fado...hanya saita hadewa faruk ya Rasa INA zakaije,....

Kiran wayar Mai martaba ke Kara hargitsa mishi kwakwalwa zuciyarsa kamar Zata fashe saboda fargaba da tashin hankali...

Kallon gabansa yayi yaga Saddam tsaye Yana masa murmushi cikin wata irin murya Mai ban tsoro yace "nafada maka yaro Kada Ka Shiga gonata Amma Ka gagara hakura saika taimakawa Fatima ko haka nake hangen kudurin a cikin idanuwanka da zuciyarka...hakan yasa nayi fushi dakai Zan hadaku Duka in halakar daku Baki Daya"ya d'aga idonsa Sama wani haske da tatsatsin wuta ke fita a idon Saddam...

Waiwayen gidansu teemah yayi mamakinsa bega gidanba fili ya gani kallon gabbas da yamma kudu da arewa yayi bega komiba ya runtse idonsa cikin tashin hankali yake Kiran sunan Allah koda ya bude idonsa duhu ya mamaye ko INA....

********
  Cikin kololuwar tashin hankali momyn faruk ke tsaye a tsakiyar fadar Mai martaba tana trying wayarsa Amma bata Shiga gumi ya jikata sharkaf ta dubi sarki "ranka ya dade wayar Umar faruk bata Shiga....da tana Shiga baa dauka Amma yanzun Sam bata zuwa"

"Innahlillahi wa innahilaihi rajiun...Ina jikana ya Shiga?ina aka kaimun yarima Mai jiran gado da Daya tilo namiji a cikin wanan masarautar"dattijuwar ta karasa maganar da fashewa da kuka,

RUD'ANIWhere stories live. Discover now