💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻♀️
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)**SLIMZY*✍🏻
_wattpadd@slimzy33_*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*Wanan shafin nakine kacokan AMINA ABDULLAHI RADDA(MRS SAIF)MEENIOSKY tawa ina miki sonso*
*4*
Daga wajen faruk Saddam wajen teemah dollar ya koma ta fito daga toilet ta dauro alwala Kenan ya kafeta da ido....idanuwansa na zubar da jini ya d'aga hannunsa Sama haske kamar walkiya ya cika dakin take dakin ya Fara juya Mata tasa hannu a kunnuwanta Zata fasa ihu rabiah ta shigo dakin kamar kiftawar ido hasken nan ya dauke....Fatima ta Shiga waige waige kamar me neman wani Abu jikinta na tsananin Bari rabiah ta dubeta cike da kulawa "ya Fatima wajenki nazo"
Fatima maimakon tayi sallah take ta mance da zancen sallah tace "Ina sauraronki tana kokarin hawa gado ta janyo wayarta"
Ajiyar zuciya rabiah tayi"yaya Fatima yanzun meye laifin auren yaya faruk?daga abbah yayi miki magana sai ki hau fadan maganganu haka?haba yaya faty dikda bansan saddam ba bankuma naso insanshi Amma faruk shine saan aurenki duba da mudin talakawa ne ba masu kudi ba"
Wani kululun bakin ciki ya tokare wuyan Fatima kamar ta shake rabiah "ke ni saarkice da zakizo kina fadamun Yadda zanyi rayuwa?Kenan kinfiso Natashi a gidan talauci in dawwama cikin talauci to be yuwuwa wallahi bazan auri faruk ba Saddam shine zabina shine farin cikina"
Saddam dake tsaye akansu ya kafesu da ido Yana saurarensu ya kyalkyale da wata irin dariya wadda wuta ke fita a bakinsa wani haske fari salll na fita daga cikin idonsa yace "saina aureki Fatima.....sai kinsan kin tureni a titi sai kinsan wulakanta halittar Allah beda kyau saina kassara rayuwarki daga karshe in kasheki"....yace Yana kallonta cike da fushi da tsana,
Hayaniyar Fatima ta shigo da ummansu tana tambaya "ya kuke mana fada cikin dare kudubi Yadda muryarku ke tashi meye haka lafiyanku?"
Cikin sanyin murya rabiah tace "ummah wai daga na bata shawarar auren ya faruk shine"...
Cike da masifa ta amshe "ehh shine kije ke ki auresa mana ki kare rayuwarki a wahala?bazan auresa ba kome zaai saidai ayi Saddam Zan aura idan Akan matsamun zamu gudu mutafi can a daura mana aure"....mamaki yasa ummah sakin Baki tana kallon tsagwaron fitsara da Fatima keyi Akan aure GA mahaifinta yace Dole faruk Zata aura.....ummah batace komiba ta rufo kofar tabarsu nan...
*******
Da sassafe faruk ya iso kofar gidansu Dan yasan tanada lectures din safe mamakinsa bakar motar saurayinta ya gani take gabansa ya Fadi amsa kuwwar muryar aljanin jiya ya dawo kunnensa.....Gefe ya nema ya tsafa yanabin motar million arbain da kallo tabbas wanan yaron akwai abun mamaki....fitowa Saddam yayi daga motar suna hada ido da faruk tsigar jikin faruk ta tashi kansa ya Shiga sarawa....Yana hango wani hasken fari a kwayar idon Saddam Wanda ke fitowa take ya soma janyo adduoi yanayi a zuciyarsa daga nesa kadan Saddam ya harde hannuwansa gudun faruk Kada ya konasa ya bude Baki yayi masa muryar tsohon jiya "Dan saurayi ba mafarki kakeyi ba.....nine Wanda nazo maka a cikin baccinka jiya nayi maka gargadi akan wanan yarinyar Fatima....idan kanason rayuwarka kanason kanka da arziki to INA Mai shawartarka daka fita harkarta"
Rufe ido faruk yayi Yadda kalaman Saddam ke bugun kwakwalwarsa kamar zasu buga masa Kai gashi Yana masa magana fuskarsa na juyewa ta tsoho tana komawa ta kyakkyawan saurayi....allahumma ajjirni fi musibati.....fitowar Fatima da karar rufe kofar gidansu yasa faruk saurin bude ido Yana sanye da rigar sanyi ja dik ta fita hayyacinta...wata harara ta watsa masa ta kauda Kai kamar bata gansa ba,...."Fatima....Kada ki Shiga motar nan motar alj....."bakinsa ya tsaya ganin abbanta ya fito da sauri daga gida,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...