11

185 16 0
                                    

💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻‍♀️

  *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)*

                   *SLIMZY*✍🏻
       _wattpadd@slimzy33_

*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*

*ASSALAMU ALAIKUM INAYIWA DAUKACIN MUSULMAI FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH YA MAIMAITA MANA GODIYA DA DUBUN GAISUWA GA MASOYANA A DIK INDA SUKE INAYI MUKU SON SO FISABILILLAHI*👏🏼😍❤️

                            *11*

Ganin duhu yasa Malam abbah shafa gefen daddumarsa ko zaisamu touch light saidai shiru....bakinsa na ambaton sunayen Allah Bai fasa ba ya Shiga zuba ayatulkursiyyu babu kakkautawa cikin ikon Allah hasken dakin ya dawo ya waiga gefensa sahu ya gani na shedar fita Amma ba sahun mutum ba.... Ajiyar zuciya ya sauke hade da daukan carbinsa Daya Fadi ya cigaba da ja....tsaki akaja a cikin dakin Mai tsayi kafin yaji karar buga kofa garammmm....


Fatima jikinta sai rawa yakeyi faruk Yana rike da ita Yana bin mugayen aljanun dake zageye dasu ko kyaun gani basu dashi,cikin furgicinda tashin hankalin ukubar da yuhana zai gana musu yake ke tunani sai ganinsa sukayi a gabansa yayi haniniya kamar mayunwacin zaki kafin ya fuzgi Fatima a hannunsa ya riketa da hannunsa duk gashi Yana kallon idonta..."waye yace ki Rabi jikinsa kina matar aure?matar auren ma tawa?kina tunanin cewa koda baa auramun ke ba Zan barki ki Rabi wani namiji ne?"hawaye ke zuba a idon Fatima wadda bata ganinsa sai sautin muryarsa takeji....yakai Mata fuzga zai kwantar da ita a Kasa ya kwanta da ita faruk ya saki wata irin Kara cike da takaici ya kauda kansa gefe....sosai jikinsa ke rawa Anya zai Bari yuhana ya Kara kusantar ta?shin kusantarta da aljani keyi Mai hakan zai haifar a gaba?

Jin yuhana na kici kicin danneta da wani irin nauyinsa Mai kaman dutse yasa ta Shiga magiyar rokonsa bata ganinsa Amma hancinta na jiye Mata wani irin wari da bata taba jinsa ba......

Malam abbah tsananin adduar da yake aikawa yuhana ne ya ishe masa adaidai lokacin da zai kusanci Fatima wani haske ya baibaye wajen ta ayar Allah take Yana Kai hannunsa jikinta wani Abu Mai kama da shocking yajasa ya Kara kokarin Kai hannunsa sai wuta ta tashi zabura yayi cikin fushi ya d'aga hannunsa Sama....Malam abbah ya gani zaune Yana karatun alkurani Mai girma...zafi yakeji ta ko INA a jikinsa hakan yasashi bacewa Yana ihu tamkar Wanda Ake konawa....

Wata iska ce Mai sanyi ta ratsa wajen yayin da wurin yayi shiru kafff shedanin aljanun sun bace...Fatima tana yashe kwance a Kasa tana jiran abinda zaisa ta hadiyi zuciya ta mutu.....kallon Sama idanunta keyi....lokacinda faruk ya Mike cikin sanyin jiki ya karasa Inda take ya hura Mata iska a ido ta lumshe idanuwanta......

Wasu hawaye masu zafi ke kwarara a idon Fatima..."fatimah....tashi zaune inaji a jikina mun kusa kubuta daga sharrin wanan azzalumn aljanin"

Cikin wata irin murya Mai ban tsoro sukaji daga bayansu Wanda ba karamin furgita faruk yayi ba tamkar zai saki fitsari a Wando "bazaku taba fita daga tarkona ba koda kun tsira a nan wasan Bai kare ba Dan tabbas bazan taba daina bibiyar rayuwar Fatima ba"...yace Yana kyalkyala dariya,

Wani miyau Mai daci faruk ya hadiye zaiyi magana cikin seconds yuhana ya rikide ya koma kamannin faruk sakkk da wasu shadda farare a jikinsa Yana kallon faruk Yana murmushi ya Ciro wani Abu a aljihunsa "kaga wanan?to dashi Zan halakar da Mai martaba mahaifinka kuma a nadani sarautar garinku kaga aljani da sarautar bil'adama.....wanan kadan daga cikin tuggun Dana hada maka Kenan...bakasan RUD'ANIN dake tattare da rayuwarku ba koda kunyi nasarar barin nan to RUD'ANIN dake gabanku sai kunyi danasanin barin nan....zanje in anwance da matarka....ya bace....faruk ya Dora hannu akai ya fasa ihu da Saida dajin ya amsa.....zabura Fatima tayi tana waige waige bata gani "faruk Maike faruwa ne? faruk faruk kafadamun faruk"

RUD'ANIWhere stories live. Discover now