💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻♀️
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)**SLIMZY*✍🏻
_wattpadd@slimzy33_*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*15*
Fararen idonta Tass Akan kofa Amma samm bata gani hannuwanta take lalube yayinda ya karasa ya tsugunna a gabanta ya ruko hannunta,wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke ta damke hannunsa masu dumi da taushi ta lunshe ido "farukk INA katafi Ka barni tun dazun?banjika ba dik hankalina ya tashi samm banason zaman gidan nan saboda gaba Daya tunda muka shigo gidan nan nakejin faduwar gaba tamkar wani Abu zai sameni"tace a sanyaye,...hawaye faruk yakeyi Yana Kara murza yatsunta cike da salo na soyayya Wanda ya haifar Mata da kasala tayi shiru takasa magana sai numfashi da take saukewa,..."Fatima ....kiyi hakuri da abinda Zan fada miki dikda a ganina ba wata matsala bace saidai bansan ke Yadda zaki dauki maganar ba Amma ina fatan ki fahimceni.....Fatima....inaso Zan barki a gidan nan Zan tafi a zuwan nagudu wani waje banaso ahalin gidan nan sugano nidin Wayene saboda momy kanwar babana ce...sanan kinga inhar natafi dake masarauta zamu fuskanci kalubale tare dake banaso ki fuskanci wata matsala kinji nafiso dik abinda zaifaru ya Zamana nine akayiwa"
"Haba faruk...meyasa bazan fuskanci dik wani yaki da tarzoma akanka ba,dik wata tarzomar da Zata biyo Baya ta biyo bayan rayuwar da kayi Dani a duniyar aljanu"ta fashe da kuka....shima kukan yakeyi dakyar ya lallasheta ta amince saidai zuciyar Fatima ta karaya Anya faruk zai dawo gareta dikda yayi Mata alkawarin cikin dare zai rinka zuwa ganinta.....sanan ya Mika Mata wata takadda Daya rubuta numbersa ta karba ya Karanto Mata ta haddace tsamm akanta da nufin zaiyi welcome back na layinsa....kuka sosai sukeyi lokacin da ya jiyo takun kafa cikin sauri ya fice.....
Yuhana ne tsaye a jikin kofar dakin da Fatima ke zaune wadda bata ganin Komi sai hawaye da takeyi....wata guguwa ce taji ta taso gadan gadan yasa taji wani fitsari na neman kubce Mata tabbas bazata mance da wanan iskar da dik lokacin datajita tasan sadam yuhana ne.....hawaye ya wanke Mata fuska....tsaye yake a gabanta cikin kamanninsa na tsohon aljani Wanda yazo Mata a kofar makaranta wanan Karon wani irin bakin hawaye yakeyi.....gamm ta runtse idonta bataso taji Komi so takeyi yakasance mafarki takeyi....hannu taji a kafadarta yasa ta sandare a zaune....cikin wanan muryar tasa yace "Fatima....harkin isa ki gujewa mijinki?ko kin manta da igiyar aurena uku akanki Wanda bil'adama da aljanu jinsina suka shaida auren mu?....kina tunanin kinci bulus?dik Wanda yaci kudina beci bulus ba haka zalika dik Wanda ya wulakantani saina kaskantar dashi....nazo gareki ne in karbi hakkin aurena INA bukatar kwanciya dake"...ya sheke da dariya jikinta ya kama rawa harshenta ya Shiga karkarrrwa tana waige waige tanaja Baya harta hade da bango.....
Kiiiii ya janyota ya Shiga kici kicin Dora Mata nauyin jikinsa ta kwalla karar gaske...take ya kalli bakinta wani Abu ya fito daga idonsa ya Shiga bakinta harshenta ya daure....
Anuwar na kishingide a kujera Kiran rumaisa ya sake shigowa wanan Karon dauka yayi besan wayeba yace "umhmm ina saurare Wayene"
"Gimbiya rumaisa ce"tace cike da isa da gadara....baice komiba hakan yasa dukkansu sukai shiru suna sauraren juna Jin bashida niyyar magana rumaisa ta Dora da fadin "Ka lasamun zumarka Ka tafi kabarni ance kaje gida yaushe zaka dawo domin ina cike da bukatar ka"tace cike da isa....yadda take magana kamar tana bashi order yasa yayi tsaki ya datse wayar,
Daidai nan afee ta fito cikin sauri...Zata wuce yace "ke ina zaki haka kamar wadda ta zare"
"Ihu naji ya anuwar kuma kamar sashen yaya Zahra ne bakaji ba?"....sai lokacin yayi jimmm kadan tabbas yaji an kwalla Kara Amma ya dauka a wajene,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...